17-18

126 4 0
                                    

🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳

*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Gsky nayi missing dinku my fans momyn ahlan tadawo
domin cigaba da nishadantu daku kudai ku dage da gobarar🔥cmmnts so much qauna 💔fans

Luv u sis amatullah 😘 thix ix ur page inajin ddin cmmts dinki

Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم

🅿-1⃣7⃣➡1⃣8⃣

Kwanan khalifa biyu kwance ajeji kamar gawa
Wani jarumin maharbi
Mai suna zakin dawa ne ya tsinci khalifa sbd yakasance yakan shiga jeji yayi har wata uku kafin ya koma wata karamar kauyensu dake cikin gafen jeji mai suna kauyen babban bishiya

Ko da zakin dawa yaga khalifa saida ya tsorata domin shi tunda yake shiga jeji bai taba ganin wata halitta kamar wannan ba domin yanzu ace zai koma kauyensu na babban bishiya saiya kai kusan rabin wata kafin ya isa duk da yanada doki

Durkusawa yayi gamida yin addua kafin yataba khalifa ya tabbatar tabbas mutum ne hannunsa ya kai saitin hancin khalifa baiji komai ba yasake kai hannunsa saitin qirjin khalifa nanma shuru yaji gabansa yafadi kunnansa yakara aqirjin khalifa yakai kusan 30scnd kafin yaji kamar zcyrsa tana harbawa da sauri yadagosa dama yaga jikinsa da kamar  an harbesa dan yaga shatin alburushi agefen kafadarsa da kuma gafen wajan dantsansa tunani ya hauyi shi kuma wnn daga ina kuma ko meya samesa

Wuka ya ciro gamida kunna wuta sannan ya hau cire masa bullet din yasa masa magani ya daukesa ya daurasa adokinsa
Da yazo da niyyar kaiwa wata uku a jeji amma sakamakon yanda yaga wannan bawan allahn nan yana bukatar taimako hakanne yasa yafasa ya dauki hanyar babbar bishiya

Gudu zakin dawa yakeyi baji ba gani kwanansu sha uku kafin  suka isa kauyen saidai yadan tsaya yasa masa magani ya du'ra masa ruwa

Kauyen cike yake da albarkatun shukuki na ya"yan itatuwa
Ga albarkatun gona  kauyen dai gashinan kore shar dashi masha allah abin sha,awa

Amma daka ga mutanan kasan basa fita cikin gari amma mutane ne masu karamci da gani

KO da zakin dawa yadawo duk wanda yagansa saiyayi mamakin ganinsa domin wa'adin dayakeyi ajeji bai cika ba yadawo amma sakamakon ganin mutum atare dashi yasasu gane cewa lallai to akwai matsala

Gidansa ya wuce kai tsaye ya kirawo masu magani aka duqufa yiwa khalifa magani

Wasa wasa saida khalifa ya share sati 2 amma duk da haka bai farfado ba amma ba laifi jikin nasa yayi kyau dan sosae zakin dawa ke basa kulawa haka kawai yaji khalifa ya kwanta masa arai

******
SAFREENA

kwananta daya kwance ajeji sakamakon marin da dauda yamata ta gangara ta bugu da wata dutse tana farkawa kasa gane kanta tayi dan gabaki daya ji tayi kanta yasara mata  batasan wacece itaba hanya tagani tasa kai tafara gudu ajeji baji ba gani
KO tsayawa hutawa batayi sannan idan dare yamata bata tsoro ko tunanin abinda zai sameta dan kuwa hankalinta yagama fita

A wannan gudun da safreena takeyi ne saida ta dibi kwanaki sha hudu masu lafiya tukunna akwana na shabiyar ta tsinci kanta akan titi da yamma tafito titin kenn tana shirin burmawa wata jejin
Saiga wata mota nan take tayi sama da ita nan take numfashinta ya tsaya cak

Cikin tashin hnkl yafito amotan  wani saurayi ne  kallonta yayi cike da tsoro bakinta fari sol abushe harya tattare da fatan bakinta rigan jikinta duk ya yage yayi kace2  kafafunta kuwa bazasu misaltu ba yanda suka koma
Nan da nan yaji tausayinta yakamashi yaduba yaga jejin da tafito tsoro yakamasa taya mutum bil adam yafito awannan gungumiyar jejin da rai agogon hannunsa ya duba yaga karfe biyar na yamma da sauri ya sureta ganin bata motsi yasata amota yana adduar allah yasa dai ba mutuwa tayi ba da mugun gudu yaja motan suka bar wajan

******

DAUDA

adan wannan lkcn duniya tamasa dadi ba karamin facaka yakeyi da kudi ba
Asati biyu kadai yaje kasan turawa sunkai goma neman mata kuwa sai abinda yakaru domin yanzu dauda baya neman mata a nigeria saidai baturiya yar kasar waje yayi abokai tantirai ga qattin da yajerasu agidan duk da yanzu baya kai kwana 2 a nigeria zai barta


More comments more typing

Share

By mmn ahlan✍🏻

GUDU A JEJIWhere stories live. Discover now