5-6

143 8 0
                                    

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳

*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Wow gsky fan's😍bani da bakin gode muku amma inayinki over 😍kuci gaba da sambadomin comments
Ni kuma bazan gaji wajan sambado muku typing ba Allah yabar kauna much luv to urs fans💔

Dedicated to feedyn bash marubuciyar ARNAN DAJI
Heart u sister💓

بسم ا لله لر حمن لر حيم

🅿_5⃣➡6⃣

Yayi gudu mai nisa da ita  kafin ya sauketa akasa yana haki alamun yagaji
Kallonsa tayi ta sun kuyar da kai kasa tace sannu yaya khalifa
Murmushi yayi yace waima yaushe kika fara kirana da yaya ne ?

Itama murmushin tayi tace tun ranar da muka fara gudu ajeji
Yaya khalifa kayi hkr ka yafemin abinda namaka hakika na yarda Dan Adam ba abin wulakantawa bane domin baka San Wanda zai taimake ka ba
Ka yafemin wlh harda sharrin kawaye da suke zugani wai inada kyau abbana yanada kudi
Kuka tafara mai taba zcy ta cigaba da mgn
Tun alkcn da baba dauda yasa wuka ya kashe iyayena tun alkcn na sallamawa duniya sannan rayuwa awannan ajeji ita kadaima darasi ce agareni wlh har kunyarka nakeji Yaya khalifa kai garkuwa ne agareni ka yafeni Dan Allah ta kuma sakin wata kuka mai ban tausayi gamida durqusawa agabansa tacigaba da basa hkr

Khalifa har kasan zuciyarsa yakejin kukanta

Durqusawa yayi shima agabanta yace naji nifa na yafe miki tuntuni Dan Allah kibar wannan kukan  karya ja miki ciwo kinga dai ajeji muke balle nayi tunanin kaiki asibity
Kukan tadan tsagaita tana kallonsa tace Yaya khalifa wai wannan jejin yasunansa?
Kallonta shima yayi ya miqe tsaye kafin  yace taya zan sani kedai tashi mutafi kawai kafin azzaluman nan suzo nan su samemu tashi tayi suka fara tafiya

Dauda yana zaune ya hakimce akan kujeran da Abba ke zama akatafaren parlourn sa
Ya daura daya kan daya
Babban rigan Abba ne ajikinsa fara sol

Cike da masifa ya kalli samudawan dake zagaye dashi yace mutum biyu !mutum biyu!mutum biyu
Ace duk yawanku duk katancinku amma kun kasa kamasu mutum biyu kacal 

Dukkan Ku baku da amfani yanda na turaku haka kuke dawowa wasu ma kam babu su babu labarinsu

To idan bazaku iyaba na namemo wasu Wanda suka fiku iya mugunta Dan wlh idan takarduna suka bata gabaki dayanku saina kasheku

Ku wuce Ku fita Ku ban waje qartin banza marasa amfani daya daga cikinsu ne yayi mgn yace boss wlh namijin ne wayo garesa gashi jejin akwai namomi masu cinye mutane

Harara dauda yafara aika masa fuskansa amurtuke  kafin ya miqe tsaye jikake Tass!Tass!Tass! Maruka   uku ya sauke masa yace zancan banza zancan wofi to ni INA ruwana idan yaga dama ya cinyesu harda Ku dinma ni burina kawai akawomin takardun nan
Ku fita yanzun nan kafin raina yakara baci
Fita sukayi gabaki dayansu

Dauda ya koma ya zauna
Khalifaaaaa safreenaaa
Saina kasheku
Dana san zaki girma ki kawomin cikas a plan dina dana kasheki tun kina yarinya kai kuma khalifa na raina ka ashe kai zaka zamemin qashin kifi to wlh bazan barku ba duk gudunku ajeji saina sa ankamo min Ku

Suna cikin tafiya safreena ta hango wani bangare mai haske tace laahh Yaya khalifa kalli can wajan daga idonsa yayi ya kalla yace muje mugani

Suna zuwa sukaga ashe wata babbar fili ne awajan ga ruwa kwance abin sha,awa tsalle safreena tayi gamida jin dadi da gudu taje tafara shan ruwan tasha sosae SBD tanajin qishi juyawa tayi ta kalli khalifa tace kai bazaka sha bane?

Murmushi yayi kuma baiyi motsi daga wajan da yake tsaye ba wani Dan karamin fashashshen kwarya tagani ba'ri daya ta dauka ta wanke duk yana tsaye yana kallonta ruwa ta dibo ta kawo masa ya karba yana murmushi yasha kafin yace ngd Anty safreena hade rai tayi ta turo baki ta zauna kusa da bakin rafin

Shima zama yayi yace menene ? tace to ba kai bane kawani kirani da suna Anty safreena dry yayi karo na farko da safreena tafara ganin dryn khalifa domin shi bai cika dry ba idan wani abunne yafiyin murmushi
Abinda yabasa dry kuma yanzu yanda tayi mgn cike da shagwaba tana turo baki kawai yaga tayi masa kyau shiyasa ya dara

Kallonsa kawai safreena keyi yace mata yadai wannan kallon fa ? Murmushi tayi tace dryn ne naga yayi maka kyau
Sassauta dryn yayi yace kema mgnr da kikayi yanzu tayi miki kyau murmushi ta kuma yi kafin shuru ya biyo baya

Duk kansu tunani suka shiga yi khalifa tunani yakeyi wannan gudun da sukeyi ajeji yaushe zai kare gashi kullum kara shigewa sukeyi
Taya zasu fita ajeji sannan bayan sunfita taya zai fara fuskantar sharia da dauda akan kisan kai din daya dingayi SBD wani burinsa na banza

Ita kuma tunani takeyi ko ya akayi da gawan mahaifanta shin anyi musu suturan daya dace kuwa ko an wulakanta mata gawan iyaye Allah yasa dauda ba jefar mata da gawan iyaye yayi ba kamar Wanda suka aikata mummunar laifi bata San lkcn da kuka ya kufce mata ba

Kukanta ne yadawo da khalifa daga duniyar tunanin da yakeyi kallonta yayi kafin ya fuskanceta yafara mgn cikin sanyin murya

Haba safreena meyasa bazaki daina wannan kukan ba kullum sai kinyita ahalin yanzu babu abinda su Abba da momy sukeso banda adduah nasan abun ba sauki da ciwo tunda agaban idanunki akayi amma yakamata ki daure kiyi yaki da zuciyarki ki fuskanci gaba

Cikin kuka tace. Wlh Yaya khalifa ko nayi yunkurin daurewa bana sanin lkcn danake kuka babbar tashin hankalina bansan ya akayi da gawan Abba da momy ba duk mutumin da ya mutu burinsa bazai wuce ayi masa sutura akaisa gidansa na gsky ba amma baba dauda babu digon imani azuciyarsa idan har akace ya jefar da gawan iyayena ne to hakika zan dauwama cikin baqin ciki taci gaba da kuka

Lallashinta khalifa ya hauyi yana bata baki tareda nasiha harta Dan sassauta kukan

Yace lkcn magriba yayi kitashi muyi sallah tunda ga  ruwa tashi tayi batare data basa amsa ba  gawani masifaffen yunwan datakeji yana addabanta kallon tausayi khalifa yabita dashi ji yake kamar  yayita kuka

Bayan sun  idar da  sallan ne gari yayi  duhu tsoro ne Yakama safreena tamatso kusa da khalifa ta zauna sai ba'rin sanyi takeyi
Yace sanyi kikeji ne?
Ta gyada masa kai alamun eh rigarsa daya yacire na saman dashike biyu ne yasamata suna nan zaune har lkcn sallan isha yace safreena lkcn sallah yayi tashi tayi sukayi sallah gamida adduah Allah ya kubutar dasu awannan jejin Allah kuma yabasu sa,a akan dauda

Zama sukayi shuru banda kukan  namomin jeji babu abinda kakeji ga tsoro ga yunwa
Khalifa ya kira sunanta  ahankali safreena kinajin yunwa ko ? Shuru tayi batabasa amsa ba Sai ga hawaye tace ai kaima kanaji ta kuma cewa
Kafata kemin ciwo kafan ya kalla duk sun kumbura yace na matse miki batace mishi komai ba ya hau matse mata kafan tausayi itama yabata batasan lkcn da tasaki kuka ta kwanta ajikinsa ba tace Ina tausaya mana Yaya khalifa muna mutane amma mun koma rayuwar jeji da gudu ajeji

Ya bude baki zaiyi mgn kenan saiga hasken touchlight mai hasken gske ji sukayi ance  gasu can
Tashi yayi ya kama hannun safreena
Suka cigaba da gudu ajeji cikin duhun dare

Suna gudu ana binsu
Ana harbi amma inaa basu kamasu ba balle bullet yashiga jikin dayansu
Jan safreena kawai khalifa keyi ayayinda shima da kyar yake gudun har garin Allah ya waye

Tsayawa sukayi ya juya ya kalli safreena amma mai layi tafarayi kafin ya riqeta ta zube kasa.....

_____to  suma  tayi mutuwa tayi nima dai bansani ba

Idan muka hadu a next page maji

Taku momyn ahlan✍🏻

Comments

And

Share

  M ahlan

GUDU A JEJIWhere stories live. Discover now