PART 10 page 51-55

197 11 4
                                    

[8/12, 10:06 PM] FARI'S DOTA💎💃🏼: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
             💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

  *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH  ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___51💎

   A qoqarin su na tsallakowa zuwa d'aya b'angaren baba na tallabe da jakunkunan su umma tamiqa hannu zata karb'i d'ayar dake sagale a kafad'arsa ganin yanda yake tafiya daqyar saboda yawan da suka yimasa tana fad'in.

"Malan kenan! ALLAH kafiye qarfin hali da yawa, miqo wannan jakar ko itace in riqa maka tunda sunyi maka yawa." Maganar takeyi tare da qoqarin karb'ar jikkar ahannunsa har lokacin suna a tsakiyar titi kai kace cikin gida suke hankali kwance, wata motace tashigo ta junction  d'in aguje tana yimasu oda amma saboda hankalin su gaba d'aya baya akan titin ba suma kula da zuwan nata ba balle suji odar da akeyi masu. abunka da mutumen qauye ba ruwansu da tunanin ai nan birnine akwai  banbancin dake tsakanin titunansu dana qauye.

Ganin motar na tunkarosu ka'in da na'in inda yasa dr.nura dake kallonsu tun d'azu ta cikin glass d'in motar yayi saurin fitowa tare da rugawa ya jayikkesu da qarfi, cikin tashin hankali duk suka saki jakunkunan nasu tsakiyar titi gabansu na matsanancin fad'uwa, yana jayesu motar na wucewa aguje kamar iska wacce kad'an ya rage ta buge Nuraddeen garin taimakonsu.

Kallo d'aya zakayi masu kafahimci tsantsar tsoron daya ziyarto zukatansu alokaci d'aya, binsu yayi da kallo cike da takaici kafin yakoma yakwaso jakunkunan nasu dake tsakiyar titi.

"Haba baba!, shifa titi da kuke gani ba gidajenmu bane da zamuyi yanda muke so akai ba, wajene da ke cike da barazanar d'aukar duk wata rayuwar da tayi kuskuren gittawa akai ba daidai ba sanadiyar ababen hawan dake kai da komo akansa, yanzu da wani abun ya sameku wani hali kuke tunanin zaku jefa halinku aciki, don ALLAH baba kudinga duba tituna dakyau idan zaku tsallaka saboda akwai banbanci tsakaninsu da naku na karkara."

Ya qarasa fad'a ransa a d'an b'ace yana miqa masu jakunkunansu.

"Kayi haquri yaro, injin bakaji ciwo ba."

Umma tafad'a tana goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata.

"A'a baaba, Amma dai adinga kula saboda gujewa qananan had'urra da manyansu."

"Mungode bawan ALLAH daka taimakemu, badon haka ba da mun afkama abunda mukayi qoqarin gujewa, mungode sosai da wannan taimakon da kayi mana, ALLAH ya saka da alkhairi yayi maka albarka."

Baba yafad'a yana kallon Dr nura daya shiga duniyar tunanin muryar umma da yaji, tabbas yatab'a jin mai irin muryar nan tata amma a Ina ne? shine ya kasa tunawa.

Daidai lokacin qanensa ya qaraso wajen riqe da gorar ruwan guda biyu a hannunsa daya siyo masa, "Yaya lafiya?."

Ya tambayesa yana kallonsu umma had'e da yatsine fuska, halinshi kenan aduk lokacin da zai had'u da talaka saboda yanda yaqi jininsu, shiyasa basa wani shiri da yayan nasa da matarsa ko kad'an, don tsakaninsu da talaka d'an jimmane da d'an jummai injisa.

"Ba komai, muje."

Dr.nura yabashi amsa had'e da wucewa yana kallonsu, bayanshi yabi ummat nayita sa masa albarka suka nufi tasha ya ajiyesa sannan yajuya ya maida motar tare daba Mai gadi makullin motar yaba Fatima sannan yawuce gida.

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Where stories live. Discover now