page 96-END

262 22 8
                                    

🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___96💎

A'a Usman wlh maganin nan nada matuqar had'ari sosai, bazan so wani abun ya sameka ba har yayanmu ya sake shiga cikin wani hali, kaine kad'ai karage masa aduniya da zai kalla yaji sanyi bayan iyalinsa, naroqeka kabarni zanje da kaina in fuskanci hukuncin laifin Dana aikata, natabbata ALLAH baya mayar da tubar bayinsa matuqar sukayi ingantacciyar tuba kuma mai kyawo, idan ko har wani abun ya sameni to nayi imani da cewa ALLAH na nufin ya jarabta nine domin yaga qarfin imanin da nace nayi da kuma tubata idan har na gaskiya ne, saboda haka kabari inje kaji d'an uwana!" yaqare maganar had'e da d'ora hannunsa saman kafad'arsa.

Kusan mintuna ashirin da wani abu sukayi suna rigima akan wanda zaije cikinsu, shidai baffa Usman ya nace shi zaije don ayanzu bai shirya rasa d'an uwan nasu ba tunda har ya tubarwa laifinsa, shi kuma baya cikin wud'anda haqo asirin zai iya cutarwa kamar yanda bokan yafad'a idan har aka haqo abun shi baffa Ali da matarsa da sukayi asirin su zai koma mawa balle wani abun ya samesa, shi kuma baffa Ali yana ganin tunda har yatuba to dole yayi qoqarin gyara laifukan daya aikata da hannunsa da kansa ko zai samu sassaucin hukuntawa daga ubangiji, ya sani ubangijinsa zai karb'i tubarsa amma haqqin wud'anda ya zalunta dolene sai yayi duk yanda yakamata wajen ganin sun yafe masa kafin ALLAH yabarshi.

Dole badon baffa Usman yaso ba ya haqura ganin yanda ya dage harda kuka, amma ya tabbatar masa dacewa Dole tare zasuje koma inane bazai barshi yaje shi kad'ai ba.

Da sauri sauri baffa ke tafiya ko gabanshi ma baya gani saboda tsananin b'acin rai har ya isa gida yana fitar da haki d'aid'ai ya samu gefe da tsakar gidan ya fad'i zube kwance yana kuka, gaba d'aya yau yarasa qarfin zuciya da jarumtar da zai iya hana kansa kuka, Babu abunda yake tunanin in banda lafuzzan d'an uwan nasa, ace kimanin kusan shekaru talatin yana fama da damuwar rabuwa da kuma fushi akan d'an nasa tilo duk ta adalilin kaidi da baqin sammun da d'an uwansa na jini uwa d'aya uba d'aya yayi masa, meye rauninsa a matsayinsa na babba agaresa daya cancanci wannan hukuncin?, Meyayi masa aduniya da bai cancanci yafiyarsa ba har sai ya rabasa da d'ansa na tsawon wannan lokaci?, Wace irin kulawace bai bashi ba aduniya daya zab'i jefasa cikin mummunan hali haka?, Haka yayita tambayar kansa yana tsiyayar da hawaye har ya gaji don kansa ya bari.

kallon baba nusaiba da tun shigowarsa taqaraso wajen d'aya zube kwance hankalinta atashe, yanda yake kukan ya tabbatar mata daba abu qarami bane ke damunsa ba, don haka saita d'auko mafifici ta shiga yimasa fiffita batare da race masa uffan ba har sai da taga yasamu natsuwar da zai iya kallonta, murmushi ta sakar masa had'e da cewa.

"Waye ya tab'a mani adilin mai gidana baban nura abban Rashida har ya karya zuciyarsa haka tasashi zubar da qwalla, kayi haquri da yanayin da rayuwa kanzo dashi na farinciki ko akasinsa, kayarda da wanzuwar qaddara mai kyau ko marar kyau agareka, ka amince babu mai yimaka sai ALLAH domin shine kad'ai ke iya sarrafa zukatan bayinsa, shiga damuwarka daidai yake da rushewar dukkanin farincikin gidannan musamman na wacce ke rayuwa bisa walwalarka da kuma farinciki, idan ni nayi maka laifi kayafeni baban nura idan kuma waje akayi maka kayafesu baban Abba amininsa?"

Duk da yana jin wani nauyi a zuciyarsa da kuma wani abu da yazo ya tokare masa amaqoshi hakan bai hana jin tasirin kalamanta azuciyarsa ba da sukasa nan take yaji wani irin sanyi ya mamaye masa ita,

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Where stories live. Discover now