PART 7

161 16 11
                                    

[7/16, 10:46 PM] FARI'S DOTA💎💃🏼: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
             💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

  *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH  ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

😭😭 _THE MOST BREAKING HEART & HEART TOUCHING PART OF THE BOOK_💔💔

Page___36💎

  Sake miqewa yayi ya nufi toilet d'in bakisa d'auke da addu'a ita kuma ta lumshe idanuwanta tana jin wani irin azababben bacci na  son d'aukarta, a wannan lokacinne madubin boka bargaji ya nuna masa cewa Rashida  bata cikin tsarki, nan take yafara surqullensa yana turo mata miyagun aljanu masu matuqar qarfi, wani iskane yataso da qarfi cikin d'akin da sauri Rashida tafarko daga nannauyan baccin daya soma d'aukarta tana cije baki, kan kace me tuni tafara ganin duniyar na juya mata, qoqarin kama addu'o'i tafarayi abakinta amma duk wacce tajawo saita kucce mata, wasu
Halittu tafara gani cikin iskan daya mamaye gabanta suna nufato inda take kowane da kalar sigarsa suna qoqarin illatata amma qarfin addu'o'in da takeyi ya shamakance tsakaninta dasu, hakan yasa suka gagara yimata komai saboda aduk lokacin da suka tunkarota wani irin gilashi mai qarfi suke ganin ya shiga tsakaninsu da ita, basu dena tsorata taba ita ma batadena karanto addu'o'in da suke bakinta ba har saida  azabar ciwon da take ji ya tsanantar mata, gaba d'aya tarud'e tashiga tashin hankali, wani irin yanayi take jin kanta aciki wanda tunda aka haifeta bata tab'a jin kanta acikiba, yanayine da kallo d'aya zakayi mata kasan cewa naqudace ta taso mata adaidai wannan lokacin, tun tana jurewa har tafara gazawa idanuwanta suka fara zubarda k'walla tana kiran "ALLAH, ALLAH." don alokacin iya shi kad'aine bakinta ke iya furtawa.
  Ganin duk aljannun da bargaji keturawa sun kasa nasara yasa yakira wani mugun shed'anin aljani wanda aduk lokacin da aiki yayi masa tsanani ko yake nema ya gagareshi shi yake turawa kuma cikin ikon ALLAH zasuyi nasara saboda ALLAH ya riga daya sakar masu talala, cikin wani qamari da girgiza ya dumfaro Rashida da alokacin bata iya furta komai saboda azabar naquda data rufeta, wani surqulle boka bargaji ya sakeyi yanda idanuwan Rashida zasu bud'e, tun tana kwance saman gadon har tajid'o dafe da cikinta alokacin aljanin ya bayyana da wata irin mummunar siffa agabanta nan take ta some wajen ba tare data koma sanin inda take ba, duk iya abunda boka bargaji zai iyayi shida shed'anun dake taimaka masa wajen ganin ankawar mata da hankali ko mugun sammun da akayi mata yayi tasiri akanta sunyi amma cikin ikon ALLAH da nuna qarfin addu'a hakan ya cutara, nasara d'aya sukayi shine d'auketa da akayi akabar garin da ita, sanadiyar hakan aljanin ya dinga buga Rashida a jikin itatuwa yana wurgi da ita bisa duwatsuna, yamatuqar fusata ganin yanda yakasa aiwatar da aikin uban gidansa akanta Wanda wannan dalilinne yasa saida y azabtar da ita sannan ya Kai ya jefar inda suke sa ran bazata tab'a rayuwa ba kafin safe.

••• ••• •••
   A 'ban garen Nuraddeen kuwa yana fitowa wanka riqe da d'an qaramin towel yana tsane ruwa akansa yace. "Habibty ki daure kitashi muje intayaki kiyo wankan nan, nasan yanda kika tsani kwana cikin irin wannan halin na janaba baccin bazai yimaki dad'i ba idan kikayi kwanciyarki a haka, gashi biyu har da rabi nadare ya somayi nasan lokacin tashinki shima yakusayi tunda ukku takusa. Pls daure ki tashi kinji?"

Yaqare maganar had'e da juyowa yakai kalonsa inda take kwance, gabansa ne yayi mugun fad'uwa da sauri ya nufi inda yabarta kwance yana jaye mayafin da suke lullub'ewa don gaskata abunda idanuwansa kefad'a masa, a firgice yaja baya ganin bata wajen kwance da sauri ya nufi falo cike da fargaba amma ga mamakinsa nan d'in ma bata nan, kasa gasgata kansa yayi ya dinga d'add'aga pilows d'in kujeru da gefe gefen kujera cikin tashin hankali gabansa na bugawa da sauri da sauri, curtains d'in tagogi falon ya shiga d'ad'd'agewa yana kiran sunanta, babban taahin hankalinsa ma qofar falon daya gani kulle Wanda yatabbatar masa daba fita tayi ba, da gudu yakoma uwar d'akan yana rerrega qarqashin gado da bayan wardrobe yana sake kiran sunanta da qarfi, bud'e qofar toilet d'insu yayi yaqara shiga yana dudubata har bayan gambu kafin ya fito jikinsa na rawa yabud'e d'akin gaba d'aya, gaba d'aya ya manta darene haka yadinga kiran sunanta yana bud'e qofar kitchen,

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Where stories live. Discover now