PART 11 page 55-60

86 7 0
                                    

[8/21/2020, 8:13 PM] FARI'S DOTA💎💃🏼: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
             💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

  *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH  ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___56💎

   Saida suka gama shaqiyancin su day izgilanci tukuna suka baro wajen,

A hankali Inna Bilkisu ta tako zuwa bakin rumfar d'akinsu suna qoqarin shiga d'aki jikinta a sanyaye tace.

"Ruqayya, Ali kuji tsoron ALLAH, duniyar nan da kuke gani batada tabbas, shin ashe halin da Yaya hawwa take ciki bai isa yazame muna aya da kuma darasi ba?, Karku manta tare da muke zaune da ita acikin gidannan, itama mutumce kamarmu amma ALLAH yajarabci rayuwarta tahanyar komawa a cikin wannan yanayin da take ciki wanda muma bamufi qarfin ALLAH ya jarabcemu fiyema da yanda muke ganinta, I zuwa yanzu ya kamata ace mudukanmu munyi karatun ta natsu, mu zamo tsintsiya mad'aurinmu d'aya duk abunda yasamu d'ayanmu mu d'auka mu yasama kuma  mu wa'aztu domin wannan halin da take ciki wlh iznane agaremu."

"To jikanyar limamai, Ina ruwanki meya shafeki da al'amarinmu?, Dama akace maki ke muke tsoro da zakizo kice muji tsoron ALLAH?, Ke nifa bilki bana son sa ido kiyi sha'aninki kibarmu muma muyi namu, yo Ina ruwanmu da halin da take ciki ai haukane ba'agareta farau ba kuma ta cancancesa, wlh Banda ALLAH ya isa tsakaninmu da ita bisa abunda taja akayi mana Babu abunda zamuyi mata, aikin banza in wa'azi kike son yi to jeki kiyi mata ita dake d'auke da haqqoqan mutane akanta take damunmu da kuwace kuwace tana hanamu bacci."  Inna ruqayya tafad'a tana harararta, tsaki baffa Ali yaja had'e da juyowa yana kallonta cike da takaici yace.

"Ke Bilki, mufa yanzu babu ruwanmu da al-amarin kowa agidan nan don haka kifita harkarmu, baruwanki da duk abunda zamuyi koda kuwa kafirci ne, kabarinki daban namu daban kinajina ko!" Jinjina kai Inna Bilkisu tashigayi kafin tace

"Wal'iya zubillah, Ali meyakawo wannan zancen, ai _inni laku minnannaasihin (ni kawai agareku mai nasiha ce)_ ubangiji ALLAH kashiryemu kuma yabaku haquri."

Tana gama fad'an haka tajuyawarta tabar wajen tana maijin takaicin halin da suke ciki.

Muneera kam tutse baki tayi tana susar kai tace. "Inna wai meyasa kuke yima Inna Bilkisu haka?, ALLAH tanada kirki kawai don baku gane bane, amma lokacin da kuke rufe  wajen 'yan sanda ALLAH duk ita take kula damu tana bamu abinci." A hasale Inna ruqayya tayo kanta tana fad'in

"Ke dallah rufemun baki, akace maki donku takeyi, duk wata maqarqashiyar rufemun da akayi ai da had'in bakinta ita da baffanninku, ai kinga kuwa dole su baku abinci ko don gudun duniya tazagesu."

"Kai Inna, ALLAH ba haka bane, ai mukad'ai ke zaune dasu ina duniyar take balle ta zagesu, kawai kice keda baffana bakwa son gaskiya kuma wlh sai anyi maku irin na inna hawwa idan baku dena ba, ni Babu ruwana, abunda ma nece mata (banqararriyar kaza) wlh da gaske ni haka naga takoma."

Kanta baffa Ali yayi da wani icce dake gefensa tafice da gudu daga gidan tana susar kai...

••• ••• •••
Baba da umma kuwa suna zamansu hankali kwance Babu wanda ke takurasu, gwargwado suna cin mai kyau kuma suna shan maikyau,  hakama alhaji naqoqarin ganin ya kyautata masu saboda su samu kwanciyar hankali da natsuwa kuma Alhamdulillah ba laifi sun d'an fara ragewa kansu damuwa, wasu lokutanne kawai take bijiro masu idan suka tuna da 'yarsu sai 'yar matsalar hajia nafeesa dake musgunawa umma tahanyar yawan baqaqen maganganu da tsawar da take yimata duk kuwa da taka tsantsan da takeyi da ita, ga Rashin kunyar da yaranta keyi wanda shike sakesa hajia nafeesa fitina idan aka qiyi masu yanda suke so.

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Where stories live. Discover now