SANNU SANNU......

338 13 0
                                    

[6/15, 11:34 PM] +234 703 729 2170: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
             💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

  *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH  ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___6💎

  Rubutun dake jikin compliment card d'in shurahbil yaqurawa idanuwa kafin yafara k'ok'arin karantosa cike da mamaki,

" _DR. N.I.ALIYU (PSYCHATRIC DR.)_" ya sake maimaitawa aransa, sannan yabi sauran address d'in dake rubuce da kuma numbobin waya har guda biyu da kallo, jujjuya card d'in yafarayi yana son tunano inda ya tab'a jin wannan sunan, Nan take yatuna cewa ai babban likitan da yasha ji ana zance agarine akan k'warewarsa wajen iya kula da mararsa lafiya musamman masu fama da matsalar k'wak'walwa ya matuqar sanin aikinsa tare da tausayawa mararsa lafiya sosai wanda wannan dalilinne yasa nan take yasamu d'aukaka cikin qanqanen lokaci, shekararsa hud'u kenan da yasa akayo masa transfer daga minna zuwa kano, kuma cikin ikon ALLAH yanzu babu inda labarinsa bai kaiba acikin garin saboda tausayi, kamanta gaskiya da kuma taimako acikin aikinsa, ajiyar zuciya yayi tare da cewa "tabbas babu ko shakka wannan mutumen shine likitan da naji ana zance agari, idan kuwa hakane yazama dole na samesa har gida saboda matsalar auntynah tunda ance shi mutumne mai sauqin kai wataqil zai iya bamu wani taimako kodon saboda soyayyar da yake yiwa yaranta" haka yaqarashi zancensa shikad'ai yana safa da marwa acikin d'akinsa kafin ya kad'a katin a aljihu yabar d'akin, yana fitowa yaci karo da zainab tafito ita da twinse zasuji wajen bukin wata qawarta, da gudu suka nufi wajensa kowacensu na Kiran "oyoyo uncle" tare da bud'e hannuwa, shima bud'e nasa yayi suka shige Yana dariya yace,

"Iyyeee 'yan matan aunty Ina zuwa akaci wannan gayu haka?."

"Party zamuje" hussaina tafad'a tana kallon zainab data qaraso wajen, duka hassana ta kaimata had'e da cewa "ke kuma bikine zamuje ba party ba ko aunty zee" tafad'a itama tana kallonta.

Dariya zainab tayi sannan tace "Gaskiya kam hassana fad'amata mu biki zamuje ba party ba, haba hussaina wane party ana zaune lafiya, ai sai kija uncle hussain ya kakkarya mu idan yaji haka!." Kallon shurahbil da shima dariyar yakeyi tayi sannan tace "don ALLAH ya shurahbil Ina zakajene?."

"Ya akayi ne?" Ya amsa mata atak'aice tare da  mik'ewa tsaye daga duqen da yake zai wuce don yasan halinta, yanzunnan me zatace ya ajiyeta, bai qarasa fitaba ta biyoshi da sauri tana fad'in. "Emm.emm dama cewa nayi ko zaka rage mana hanya pls"

"Ok, dama nasan shine zancen" yafad'a tare da ficewarsa, da sauri ta dawo baya tariqa hannuwansu sukabi bayansa suna yimata 'yan tsalle tsalle.

Bayan sun shiga mota shurahbil ya tayar suka bar gidan ya juyo Yana kallon zee da tasha kwalliya qamshin turare na tashi ajikinta tako ina yace,

"Zainab kinji fitinannen qamshin da kikeyi kuwa?"

"Eh ya shurahbil turaren yayima dad'i ko?." Saida yamere baki tare da yin kwana ya hau titi daidai sannan yace

"Wane dad'i, turare na hawan kai haka?, Meyasa Wai ku bakwa fahimtar cewa annabi yafaku, fisabilillahi wannan qamshin turaren da kikeyi yayi yawa, zai iya jawo hankalin maza akanki, ga wannan baqar kwalliyar da kika b'ata fuskanki da ita, gaba d'aya ta maidaki wata irin halitta daban sai kace dodo ko kuma aljana. dubi d'inkin dake jikinki zainab inada tabbaci akan ko lumfashi maikyau baya barinki gashi kin d'auko mayafi sai kace abun tatar k'ullu kin d'ora akai, gaba d'aya kincika duk wasu sharudd'an da zasu iya jefe rayuwarki cikin halaka" turo baki tayi ranta ab'ace saboda jin yanda take faman kushe mata kwalliya da kafin tace,

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Where stories live. Discover now