page 62-70

71 4 3
                                    

🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
             💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

  *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH  ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___63💎

  Tunda suka hau titi babu wanda yacewa wani uffan har suka isa gida, kowanensu ya lula duniyar tunani akan yanda rayuwa zataci gaba da tafiya dasu bisa linzamin qaddarar da suke akai, musamman Dr nura da yake ganin gaba d'aya cinmutuncin da matar mahaifinsa tayi akansa yaqare, don haka akwai buqatar ya d'auki matakin yiwa abun tufqa tunkafin yayi tsayi.

Gaba d'aya sai sukajidaren ranar yazo masu abai baice, hatta 'yar firar da suka sabayi a kowane dare kasawa sukayi kowane ya shige part d'insa ya kwanta, haka ma da safe kusan yanda suka kwana haka kowane yatashi fuskarsa babu wata walwala har suka zauna wajen  karyawa ba wanda yace wani abu bayan gaisuwa, miqewa Rashida tayi bayan tagama nata Karin zata wuce  d'akinta taji muryar Dr yace.

"Koma kizauna maman boy ina son zamuyi magana dake."

Bamusu takoma ta zauna yayi gyaran murya had'e da cewa.

"Ina mai baki haquri bisa abunda yafaru jiya, da nasan hakan zata kasance wallahi da ban d'aukeki nakaiki gidan muba, gashi hakan da nayi na neman sauya walwala da kuma farincikin gidannan gaba d'aya, naroqeki kimanta da abunda yafaru domin haka zaisa rayuwarki taci gaba da inganta kamar yanda tafaro, tabbas Bata kyauta ba data cutar dake ta hanyar munanan kalamanta batare da tasan koke waye ba! kuma ko kad'an batayi maki adalci ba a matsayinta na uwa da tasan irin zafin da akej idan aka aibatawa mutum d'a, Amma duk da haka Ina nema mata afuwa a matsayinta na matar mahaifina, ina tabbatar maki da hakan bazata sake faruwa ba in sha ALLAH kinji."

"Uncle kenan! bazance banji komai araina ba akan abunda yafaru jiya kasancewar yazamo silar jefaku cikin halin da tunda nake zaune daku ban tab'a ganinku acikin koda makamancinsa ba, ba ina damuwa bane akan abunda tayi mani ba, kawai damuwata tabayyana ne adalilin yanayin da nake kallon fuskokinku aciki, kalamanta abune da babu tushe, asali ko kuma inganci aciki da har zan damar da kaina. amma shi b'acin ranku da kuma damuwarku tamkar wutace dake cin zuciyata idan Ina ganinku acikinsa wanda natabbata bazata dena ciba har sai lokacin da naga farinciki yabayyana   fuskokinku, kuyi haquri domin nima nazamo sila wajen sa ajefeku da kalaman da suka cutar da zukatanku."

Kallon Fatima Dr yayi had'e da cewa.

"Kijifa abunda take fad'a!, taya za'ayi tazamo silar cutuwar zukatanmu bayan laifin ita akayiwa."

"Hakan nafaruwa kuwa Dr, musamman ga  zukatan da basu fiye son kansu ba kuma suke kallon damuwar wasu amatsayin tasu, don haka damu da ita mu manta da komai mu fuskanci gabanmmu."

"Shikenan ALLAH yaqarawa zukatanmu haquri kuma yabasu girman d'auke duk wata jarabawa da kuma gwagwarmayar rayuwa."

"Amin ya rabbi."

Suka fad'a tare suna murmushi, nan suka dasa rankon sabuwar firar da basuyi ba jiya,

Bayan wata uku little yaqara wayau Rashida ta yanke shawarar yayesa saboda ganin irin girma daya taso masa kuma babu abunda bai iya ciba. Ana saura sati d'aya tayayeshi suna zaune ita da fatima tace.

"Aunty nifa wani sati cire yaronki zanyi amama, ALLAH nagaji da tsutsannan da yakeyimun."

"Kai maman boy, shekararsa d'aya da wata d'aya fa kenan?"

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Where stories live. Discover now