PART 6

155 9 2
                                    

[7/12, 10:22 PM] FARI'S DOTA💎💃🏼: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
             💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

  *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH  ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Hi fan's am so sorry akan yanda kuka matsu mukoma asalin labari, Karku manta ita SANNU SANNU bata hana zuwa..no matter how matuqar ALLAH yabani aron lumfashi da kuma rayuwa zan sadaku da farkon labarin da muka faro, karku manta *baku san ko waye Abu sumayya ba?, bakusan asalinsa ba? taya ya had'u da matarsa batool shima baku sani ba? meya jawo batooul tabar iyayenta har na tsawon shekaru bakwai? Shin Abu sumayya ya cancanci mutuwa adaidai lokacin da yakamata yasan ko waye mahaifinsa?, meyasa mahaifin batoul ya sheganta shi, Shin batool itama ta cancanci ta fuskanci jarabawar da take ciki adaidai lokacin da take d'okin sake had'uwa da iyayenta?* 😅Inada yaqini akan shima baku sani ba kuma bakuda duka amsoshin wud'annan tambayoyin, wannan waiwayen tushen labari da mukayi shi kad'ai zai amsa maku duka wud'annan tambayoyi kuma da sannu ya sadaku da farkon labarinku, saboda haka kujuri zuwa rafi na tabbatar ranar da tulun zai fashe na nan zuwa🤣Ina matuqar godiya bisa yanda kuke qaramun k'warin guiwa ta hanyar comment d'inku, nakanyi farinciki kuma na nishad'antu da hakan akoda yaushe, FILLAH INA SONKU OVER💋😍_

Page___31💎

  Har Nuraddeen zai wuce yadawo yayi tsaye yana jin maganganun dake fitowa daga bakin muneera, tun daga farko har qarshe babu abunda baiji ba yafito ransa a'bace yana watsawa Inna ruqayya da tayi tsuru tsuru da idanuwa tana 'yan kame kame wani irin mugun kallo da yasa cikinta murd'awa, nunata da yatsa yayi yace.

"Wai ni za'a kai wajen wani malami ko boka don in so wannan abar?" Yaqare maganar yana nuna muneera sama da qasa da hannu, murmushin gefen baki ya saki cike da takaici kafin yaci gaba da cewa. "To wallahi Inna ruqayya koda matan duk duniya zasu qare bazan tab'a auren muneera ba Kuma badon bana sonta ba sai don kawai kinzamo mahaifiyarta, duk da  'yar uwata ce ita bazan iya aurenta ba har duniya ta nad'e don haka idanma mafarki kukeyi to wlh kufarka kunema mata mijin daya dace da ita, wannan Nuraddeen da kike gani in sha ALLAH mallakin Rashida ne ita kad'ai, zuciya da kuma ruhi gaba d'aya natane bana tunani ko a mafarki kwakwalwata zata aminta da shigowar wata azuciyata ko wacece ita ciki kuwa har da muneera d'in da kuke qaqabar 'yar uwata ce domin bare tagama mani komai aduniya.." wata irin qara muneera tayi had'e da ciyo kwalarsa tana kuka, "wallahi ya nura baka isa ba, don ka kawai aka halitto ni bazai yuyu na auri wani inba kaiba.." Bata qarasa maganar sanadiyar wani zazzafan mari daya d'auketa yana kallon wuyar rigarsa data riqo, qafa yakai zai hankad'ata tayi saurin duqewa wajen tare da riqe masa qafafuwa tana kuka,  "don ALLAH ya nura karka damu da inna, kafita batunta da halayenta ni kai nake so, zan zauna da kai ko mata nawa zaka aura amma karka yimani hukunci akan halin Inna ita da baffa sune basa son matarka haka ranar naji suna fad'a wai Inna hawwa takaita wajen malan bakada imani za'a dinga turo mata aljanu suna tsoratata, yanzu haka ciwon da takeyi sune sukasa yaturo mata shi.." baya baya Nuraddeen yayi kamar zai fad'i saboda tsorata da kalaman dake fitowa daga bakin muneera, duk da dai ciwon da Rashidarsa keyi ba irin wanda take nufi bane amma maganarta akwai qamshin gaskiya aciki idan yayi la'akari da tsoron da Rashida kecewa ana bata da Kuma yawan firgitarta acikin barci, kasa cewa uffan yayi har saida Inna Bilkisu dake tsaye cikin rumfarta tana sauraronsu ta matso wajen ganin yanayin daya shiga ta dafashi tana fad'in. "Karka kuskura ka amince da wannan soki burutsun na muneera kasan halinta da shirme, idan kuma har gaskiya take fad'a to kada ka tsorata domin da wannan tsoron naka za'ayi amfani wajen cutar da kai da kuma matarka kayarda ba mai yimaka sai ALLAH kuma Babu wanda ya isa ya cutar da kai sai abunda alqalamin qaddara ya rubuto akanka, maza kawuce kaje wajen iyalinka ba abunda zai sameku in sha ALLAH tunda kun riqe ALLAH, sharri shi Kuma d'an aikene duk inda kaje  zai dawo ya sanar maka."

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Kde žijí příběhy. Začni objevovat