Page 77-80

101 11 8
                                    

    *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
             💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

  *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH  ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___78💎

   Shikuwa ashe lokacin ko barci bai tashiba don gaba d'aya ya shafa'a da zancen fitar da zasuyi, kwance yake yana baccinsa hankali kwance uncle hussain d'in ya d'an bubbugi qafarsa ya tashi yace dashi.

"Kaje baba na kiranka tun d'azu ya shirya kai kad'ai yake jira."

Yana gama fad'ar hakan ya juya yafita da sauri yamiqe yafad'a toilet yayo wanka, bai tsaya wani abuba yana tsane jikinsa yaciro qananan kayansa yasa had'e da zura takalminsa yafito, a tsakar gida ya samesa yafito daga cikin d'aki matan nabiye dashi suna yimasa addu'ar ALLAH ya kiyaye ya gaggaishesu cikin girmamawa had'e da karb'ar ledar hannunsa yana gaishesa shima.

Kallonsa baba balarabe yayi tun daga sama har qasa bayan ya amsa masa gaisuwar had'e da cewa.

"Kar kace dani yanzu katashi bacci Naga kamar akwai sauransa acikin idanuwanka."

"Aikuwa dai, don gaba d'aya na sha'afa da zancen tafiyar nan, koda uncle Hussain yaje bacci nakeyi."

"To kawo ledar, maman 'yan biyu jeki kizubo masa abun karya warsa."

"A'a d'an tsohona mutafi, idan naje can sai na karyar."

"Anya zaka iya kuwa?"

"Eh mana, muje tunda ba noma ne zanyi ba."

Su maman 'yan biyu nata yimasa dariya had'e da tsokanarsa wai kar yaje yadawo masu kamar a hurasa yafad'i, murmushi kawai yayi masu had'e da juyawa yafita baba balarabe yabi bayansa suna biye dasu suma suna yimasu ALLAH ya kiyaye.

Suna isa kasuwar bayan ya taimakawa baba balarabe yabud'e shagonsa na kayan d'unki da yadukkan mata da yake saidawa suka gama jejjera komai sannan yasamu waje ya zauna yana kallon yanda d'aid'aikun mutane ke shigowa cikin kasuwar da sauran masu shagunan da suka fara bud'ewa, dariya baba balarabe yayi had'e da cewa

"Yaufa mazan boko ne akasu sai faman raba idanuwa sukeyi, ko yazata kaya dasu?"

"Sa ido kagani, zaka sha mamakin mazan bokon nan sosai, don yau zakayi cinakin da baka tab'a yiba."

"Ah..to madallah ai haka akeso, bara ni naje can nadawo." Yafad'a tare da ficewa yabar shagon, wajen wani mai saida tea da biredi yanufa yace ya bashi leda d'aya ta biredi da madarar ruwa gwangwo d'aya sai bonbita itama sachet d'aya sannan yasa ya soya masa qwai guda ukku tare da ruwan tea a cup ya karb'a yanufo shago dasu, a daidai bakin qofar shiga shagon nasa da yake akan hanya wucewa cikin kasuwar yake yaci karo da baffa d'auke da kondon kajinda yake sayarwa shida yaransa da suke biye dashi d'auke da sauran kwandunan kaji suna shigowa saboda tuni yakoma sana'arsu adalilin qarewar da dabbobin nasa da ada yake kasuwancin saye da sayarwa dasu, gashi badamar ya rabke hannuwa tunda iyali sun riga da sun taso masa don yanzu Masha ALLAH, ALLAH ya albarkacesa da 'ya'yaye har biyar aduniya, yanada 'yan mata hud'u da kuma namiji d'aya wanda shine qarami yanzu yanada shekaru biyar aduniya, hakan yasa yakoma sana'ar kiwon kaji acan gida irin buloros d'innan kuma yana zuwa dasu anan kasuwa yana saidawa kuma balaifi yana samun cinaki sosai da yake rufawa kai asiri dashi, da sauri ya qarasa wajensa fuskarsa asake yamiqa masa hannu yana fad'in.

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Where stories live. Discover now