Wa nake so? 195

365 22 1
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
195

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*

Haka in ya dawo zai sa a kawo Masa yaron sosai yake Jin yaron tamkar dan cikin sa. Dan kullum ya fita sai ya shigo Masa da Kaya kala kala masu tsada da kyau. Fateema ba karamin Dadi take ji ba haka Nan ba Wanda take so ta gani in bashi ba.

Yau ta kafa ta tsare sai taga Fu'ad Wanda tana daki Nusaiba na wajen ta tare da Annur dake hannun ta Baba ta shigo tana fadin
"A kawo shi Baban sa ya Ganshi."

"Baba ya dawo ne?"
"Eh!"

Ta amshi Annur ta fita dashi. Nusaiba ta kalle ta tace
"Waye babban sa?"

"Fu'ad!"
"Oh ya dawo. Daman Ina son ganin sa bari naje."

Ta mike ta fita Fateema ta bita da kallo zuciyar ta na bugawa. Bayan minti talatin ta kasa zama dan haka ta mike tayi dakin Fu'ad.

A falo ta same shi zaune a kasa gefen Nusaiba Yana magana kasa kasa. Abinda ta iya ji kawai yace
"Banyi dan na Bata Miki rao na kema kin sani."

Annur ta Shiga ta dauka ta juyo ta fice kawai. Da kallo suka bita. Yace
"Muje ba rakaki dare yayi ko?"
Ya mike tabi Bayan sa. Yace
"Kin fiya daru Autar Mami."

Baki ta turo yai Dariya Yana fadin
"Sai na cire bakin!"

Fateema dake tafiya tana Jin sa tai sauri ta shige ciki. Nusaiba race
"Bari nai wa Anty Fateema Sallama."

"Kyale ta muje kawai!"
Suka fice.
Fateema na Shiga daki ta rumgume Annur ta saki wani kuka. Ta rasa kukan menene ji take kamar zuciyar ta zata fashe dan damuwa. Ranar gaba daya batai Bacci ba kan safiyya kuwa idon ta ya kumbura saboda kuka da rashin Bacci.

Da safe Bayan tayi wanka ta saka bakin siket da Riga highneck long sleeve baka da fara gaban ta zip ne ta saka hula akan ta.

Dakin Baba ta Shiga ta dauko Annur suka fito falo dan ta karya. Zama tayi ta ajiye tea da dankalin da ta debo akan stool. Ta daga Annur tana fadin
"Baka Jin yunwa Baby nah?"

Ta daura shi Akan ciyar ta, ta zuge zip din dake gaban rigar ta, ta fito da maman ta tasaka Masa a Baki yaron ya amsa yana lumshe Ido. Ta shafa kan sa tana Masa addu'a.

Fu'ad ne ya fito daga dakin sa Dan Shima jiya Sam bai Bacci ba Kuma ba zai ce ga dalili ba Amman ya kasa Bacci Yana fitowa falon yai tozali da Fateema na bawa Annur nono. Cak ya tsaya Yana kallon su yadda tayi kyau ga kirjin ta fari tas dashi.

Dagowa tayi suna hada Ido yai sauri ya dauke Kai yayo cikin falon. Itama ta cirewa Annur a Baki tana zuge rigar ta. 

Kitchen ya Shiga ta daura Annur Akan kafadar tana shafa Bayan sa.  Hajiya ce ta fito ta ce
"Baki karya ba."

"Wallahi na tsaya bashi ya Sha ne."
"Kawo shi sai ki karya ko?"

Ta mika Mata shi sannan ta dauki tea din ta kurba. Hajiya ta kalle ta tace
"Me ya samu idon ki?"

Zatai magana Fu'ad  ya fito daga kitchen rike da cup. Tayi kasa da Kai. Cup din ya ajiye Akan stool din gefen kujerar yayo gun Hajiya yace
"My boy!"

WA NAKE SO?Where stories live. Discover now