Wa nake so? 141

354 34 12
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
141

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*


*
10:00pm tana kwance akan gadon ta bayan tai addu'a har ya fara bacci taji wayar ta na kara hannu ta saka ta dauka ta kai kunnen ta
"Kanwata ya kike ya dare?"

"Alhamdulillah!"
"Gud just call to say gud nyt!"

"Thank you!"
"You are welcome gud nyt!"

"Have a sweet dreams!"
Ta kashe wayar.

*
*
*
Washe gari
9:00 am zata fita tayi round kenan ya kira ta. Dauka tayi tace
"Morning Uncle ya aiki?"
"Alhamdulillah and yours?"

"Same!"
"Gud Allah taimaka!"

"Amin thanks!"
"Never mind daman na kira naji ya kika tashi ne?"

"Alhadulillah nagode sosai."
"Aha bye!"

*
5:00pm sauri take tana hada jakar ta dan zata shiga tayi siyayya ta tafi gida tana isa bakin kofa aka budo kofar kallon ta ya tsaya yi tana sanye da hijab har kasa Ash kala.
"Wow beauty!"

Ya fada yana shigowa. Kallon sa tayi ta dan saki murmushi tace
"Ina yini?"
"Lafiya lou Dr kinyi kyau wallahi kallan ya amshe ki!"

"Ko nagode!"
"Ina zakije ne?"

"Wallahi ina son na shiga sahad ne nayi siyayya!"
"Amman ba neman rakiya."

Murmushi tayi yace
"Muje to!"
Fita tai ya biyo bayan ta. Motar ta ta nufa ta shiga shima ya shiga tashi tana fita ya bi bayanta har suka karasa sahad tana parking shima yayi ya fito tare suka shiga ciki amman kowa yayi gun da zai siyayyar sa.

Gun perfurms ta fara zuwa ta jidi wanda take so sannan ta karasa wajen man da take shafawa ta dauka ta dauki na kitson ta. Gun sanitary pad ta karasa ta dauki ledar kenan taji yace
"Har yanzu baki gama ba?"

Da sauri ta maida ta juyo tace
"Eh!"
Ta bar wajen murmushi yayi ya dauki sanitary pad ya saka a basket din sa ya nufi counter din. Total akai masa ya biya ya tsaya jiran ta.

Daga nan gun wajen sweet and bisket ta tsaya ta zaba ta saka a basket ta karaso tana zuwa ya matso kusa da ita yana fadin
"Ya dazu kika bace min."

Murmushi kawai tayi kudin aka dada kan Fateema ta bayar ya mika ATM card din sa zatai magana yace
"Please sorry!"

Shiru tayi aka diba suka fito gun motar ya ta shiga ta saka kayan ya karasa ya saka na hannun sa sannan yace
"Ina zuwa!"

Gun sai da ice cream ya isa ya siyo leda biyu sannan ya dawo. Leda daya ya dauka a wacce ya ajiye ya bar mata daya sannan ya ajiye mata ledar ice cream daya a cikin motar yace
"To anan zamuyi sallama ko"

Kai ta gyada yace
"Ok bye ki gaida Momy!"
"Nagode!"

Ta fada juyawa yayi ya shiga motar sa tana tsaye ya fito yace
"Lafiya?"
Kai kawai ta girgiza ta shiga tata motar ta tayar suka fice a tare.

A falo ta zube kayan bayan ta shigo sun gaisa da Momy ledar da ya saka mata ta dauko ta bude pad din da ta ajiye ce a ciki kai ta girgiza ta bude ledar taga wasu Hijab ne a ciki masu masifar kyau guda uku. Budewa tayi Momy ta fito tana fadin
"Kai amman Hijab din nan yai kyau nawa kuma?"

WA NAKE SO?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora