*WA NAKE SO?* 💝💝💝
123-124WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.comDA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.
Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*
Da yamma suna zaune a daki suna hira Hajiya ta shigo. Kallon ta sukai. Fateema tace
"Sannu Mama!""Yauwah Fateema wannan me surutub ta cika miki kunne ko?"
Murmushi Fateema tayi. Nusaiba tace
"Kai Hajiya!"Hajiya tace
"Ku taso ku rakani gidan Hajiya Rukayya!""Toh!"
Fateema ta fada tana mikewa. Fita Hajiya tayi. Nusaiba ta isa gaban mirrow tana shafa hoda sannan ta dauki turare ta fesa.Fateema kuwa mayafi ta dauka kawai ta tsaya kallon ta. Sai da ta gama ta juyo tace
"Anty ke ba zaki gyara fuskar ki ba?""Kai kyale ni haka!"
"Ai ke dan kina da kyau ne!""Kema kina da shi ai."
Nusaiba tace
"To ki dan shafa hodar mana."Amsa Fateema tayi ta shafa. Nusaiba tayi murmushi tace
"Kinga yadda kika kara kyau!"Kai Fateema ta girgiza kawai tace
"Muje!"
Turaren ta ta dauka ta fesa mata. Tai murmushi tace
"Muje mun bar Hajiya a waje fa."Nan suka fita. A falo suka same ta zaune wannan yasa suka karasa gun ta ta kalle su da fara'a tace
"Kun fito."Fateema tayi kasa da kai tace
"Eh!"Mikewa tayi tai gaba suka bita a baya. Mukullin motar ta ciro ta bude. Sannan ta budewa Hajiya gidan baya ta shiga, Nusaiba ta shige gidan mai zaman banza. Fateema kuma ta zaga ta shiga wajen driver. Mai gadi ya bude musu. Fita sukai sannan tace
"Wacce unguwa ce?""Sharada phase 1 ki shiga ta layin yahya gusau."
"Toh!"Taja motar suka dau hanya suna tafe suna dan taba hira da Nusaiba har suka shigo titin Yahya Gusau din. Titin dake hannun daman su suka shiga nan ta nuna mata layin ta shiga. Wani katon gida ta nuna mata. Horn tayi mai gadi ya fito yana cewa
"Gun wa kika zo?"Hajiya tace
"Lawan!"Yana ganin Hajiya yace
"Ranki a dade ashe tare kuke barka da zuwa ina yini?""Lafiya ya aikin?"
"Alhamdulillah!"Ya juya da sauri ya bude gate din. Shiga tayi tai parking a katon parking space din su da zai ci a kalla motoci sama da ashirin. sannan ta kashe motar. Ta fita da sauri kan hajiya ta bude ta bude mata. Fita tayi ta rufe zatabi bayan su wayar ta tai kara tana dubawa taga Momy ce. Murmushi tayi tabi bayan su ta dauka tare dayin sallama.
Momy ta amsa tana fadin
"Wato kin samu Hajiya kin manta dani ko?"Murmushi Fateema tayi tace
"Ina yini ya gida?"
"Alhamdulillah yasu Hajiyar?""Suna lafiya bari na bata."
Ta karasa kusa da Hajiya ta mika mata waya tana fadin
"Momy ce."Amsa tayi ta kai kunne tayi sallama. Amsawa Momy tayi sukai gaisa sannan sukai sallama. Wayar Fateema ta kaa tace
"Momy mun fito ne!""To a dawo lafiya!"
Ta kashe wayar. Sai da sukai tafiya mai tsayi sannan suka karasa main parlon ba kowa a ciki dan haka suka kara shiga falo na biyu anan suka zauna.

STAI LEGGENDO
WA NAKE SO?
FantasyLabari akan sarkakiyar soyayya har ka rasa wanda kake so saboda tsabar yadda kowa ke nuna maka kulawa da soyayyar sa. Labarin guda biyu ne kowanne da kalar ssa but sun hadu ne a inda suka rasa gane wanda suke so? Aliyu, Muhammad da Aisha Fauwaz, Fu'...