Wa nake so? 157

338 27 5
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
157

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*


Ta juya zasu tafi sai taji yace
"Fateemaa!"

Bata juyowa ba ta cigaba da tafiya ba tai aune ba sai ganin sa tayi a gaban ta. Ido ta zaro tana kallon sa.

"Wai Fateema menene haka ne Fauwaz ne fa where are you behaving like this wannan ba Fateema da na sani ba."
"Tinda ba wacce ka sani bace ai sai ka fita a hanyar ta ko?"

Tayi gaba zata wuce yai maza ya kai hannun sa ya tare ta tare da rike ta. Annur ya kalla yace
"Get inside."
Da gudu yai ciki. Ta bi yaron da kallo sannan tace
"Dan Allah sake ni."

"Wai Fateema me nai miki ne?"
"Me kai min kamar yaya?"

"Kin canja ko magana fa tinda nazo gidan nan bata hada mu ba."
"And so?"

"Wallahi ba haka kike ba da!"
"Da da ai da yanzu ba daya bane ko?"

"Me kike nufi."
"Komai ya canja."

Kai ya girgiza yace
"A'ah ba komai ba dai."

"A wajen ka kenan ni a waje na komai ya canja."
"Kina nufin har son da kike min?"

Wani kallo ta watsa masa ta janye hannun ta da karfi ta juya zata tafi. Cikin zafin nama ya janyo ta ya hada da bango ya saka hannayen sa ya tare ta.
"Menene haka?"

Kallon ta kawai yake yana jin son ta na daduwa a cikin zuciyar sa. Fuskar sa ya matsar gaban tata suna jiyo nunfashin junan su ido ta runtse ya kalli idon ta sannan ya kalli lips din ta dake shekin lips stick batai aune ba sai jin lips din sa tayi a kan nata da sauri ta bude ido ta ture shi amman sai ya rumgume ta.

*
Gloria ganin sha daya tayi bai shigo ba yasa ta fito tana zuwa kofar part din Momy ta ganshi rumgume da Fateema. duk basu lura da ita ba dan Fateema fadi take
"Menene haka Yaa Fauwaz kasan fa babu kyau dan Allah ka sake ni."

"Ba zan sake ki ba Fateema sai kin fadan me nai mimi kike share ni tinda nazo gidan na ko kallon arziki baki min ba dan wa nazo garin dake nazo ba."
Tsaki ta saki tace
"Ina ruwa na ni nace ina bukatar ka ne."

"Tsaki kike min! Ni kikai wa tsaki."
Baki ta murguda tace
"Malam ka sakeni."

"Sai na hukunta bakin da yai min tsaki in yaso gobe ma ki kara."
Yana gama fadar haka ya fara kissing din da ta zafi zafi. Ido ta zaro dan yadda yake mata da mugunta yake mata zafi kawai take ji kokarin ture shi take amman ta kasa

Gloria da tayi mutuwar tsaye ta saki wani ihu tayo kansu. Duk da yadda yake mata kiss din na mugunta ne amman sai da ya fara shiga wani hali ihun da Gloria ta saka ne ya dawo dashi daga tafiyar da ya fara da sauri ya saki Fateema ita kuma ta duka a wajen tana kuka.

Kan Fauwaz tayi yana fadin
"Menene haka Fauwaz? Cin amanata zakayi dan haka ka matsa sai mun dawo kasar ka me kake yi haka? Ko a turai baka bin matan banza sai anan!"

"Shut up malama wannan ba matar banza bace kuma ki shirya kwanan nan zata shigo cikin gidana as my second wife."
Ido ta zaro tana fadin
"wallahi baka isa ba baka isa kai min kishiya ba kaji na fada maka dan ka cucen shine zaka auri wannan matar to ni ban yadda ba shiyasa take min wani gani gani ko?"

WA NAKE SO?Where stories live. Discover now