*WA NAKE SO?* 💝💝💝
196WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.comDA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.
Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*
Anan ya jasu sallah. Sukai sallah ya dauke ta suka tafi wajen dinner. Da suka je ma a mota suka tsaya tace
"Yaya!"Ya juyo tace
"Muje ko?"
Ya bude ya fita yace
"Ina zuwa."Ya fita ya zagaya ya bude Mata ta fito. ya Kama hannun ta suka nufi gate din.
Lokacin har amare da ango sunje suka karasa ciki su Mamah suka hanga suka karasa suka Kara gaisar dasu sannan suka wuce wajen da Yaa Abubakar yake zaune shi da matar sa da Ya'ya sa. Sannan suka karasa wajen Yaa Usman daga nan suka wuce bangaren da aka tanada musu.
Zama sukai, Nan MC yace
"Muna yiwa Yarima Aliyu barka da zuwa tare da Mai dakin sa Gimbiyya Aisha. Kanwa ango da Amarya."Umar da Farouk ne suka zo suka gaisa sannan suka wuce wajen zaman su haka sauran ma Yaa Ibrahim da Umar da Mustapha duk suka zo suka gaishe su.
Haka aka cigaba da tafiyar da taron. Aisha ta mike ta kamo hannun sa tace
"Yaya muje ai Mana picture."Ta Kama hannun sa sukai ciki wajen Marayma da Muhammad. Maryama ta kamo hannun Aisha tace
"Kinyi kyau."Kema haka. Ta matsa tace
"Yaya kayi kyau."
"Nagode!"Nan suka gaisa da Aliyu sannan akai musu picture wajen Mujahida da Shu'aibu sukaje Suma akai musu pictures din sannan suka tashi suka koma wajen su.
MC ne ya Kira Yaa Aliyu da Aisha Akan su fito su Yi wa angwaye da Amarya liki. Nan suka fita suka farai musu ruwan kudi suna tsaye Yaa Abubakar da Matansu suka fito Suma sukai hau liki haka suka koma ma zaunin su.
Karfe Tara da Rabi ya matsa Mata sai sun tafi haka ta mike suka koma gida.
Washe gari akai yini Ranar asabar akai daurin aure da yamma akai walima. Sam Aliyu ya Hana ta Kai amare. Dan Dukkan su can garin su Aisha aka Kai su.
Gidaje ne iri daya ya gina musu guda biyar. Anan ya bawa Yaa Umar da Ibrahim da Mustapha ma key. Aka Kai Maryam da Mujahida can.
Gida ne manya wanda yake dauke da part biyu gini yai kyau na zamani Mai kyau. Abbah ya zuba musu Kaya masu kyau da tsada.
An Kai amare gidan su kowa an barsu da angwayen su duk a Daren suka more amarcin su. Kowa yaji dadin yadda ya samu amaren sa da mutuncin su.
Washe garin Kai amare da safe tana kwance a daki Aliyu ya shigo ya kalle ta yace
"Ya dai Baby Love?""Na gaji Yaya.'
Kallon ta ya tsaya yace
"Da yake an gama biki ko?"Kai ta gyada tana murmushi. Yace
"Muje mu dawo nai Miki tausa ko?"Kai ta gyada tace
"Ina zamu?""Dady ne yazo zaku gaisa."
"Waye Dady?""Mijin Mama."
"Allah sarki.'
Ta dire kafar ta tace
"Muje."Ya dauko Mata mayafi ta yafa sannan suka Fita. Falon Abbah suka isa kai tsaye. A bakin kofa sukai sallama aka amsa suka shigo. Tinda suka shiga Dady ya zuba mata ido tayi kasa da kai ta karasa ta zauna.

STAI LEGGENDO
WA NAKE SO?
FantasyLabari akan sarkakiyar soyayya har ka rasa wanda kake so saboda tsabar yadda kowa ke nuna maka kulawa da soyayyar sa. Labarin guda biyu ne kowanne da kalar ssa but sun hadu ne a inda suka rasa gane wanda suke so? Aliyu, Muhammad da Aisha Fauwaz, Fu'...