Wa nake so? 140

315 28 14
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
140

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*

*Zeezy74 from wattpad. Am really appreciate Dis page is urs. Ina fatan yafi na jiya dadi*

*
A gidan gwamnati suka suka basu tsaya sanya ba suka bawa PA bayanan abinda suke nema nan da nan ya fita ya nemo musu address din gidan su Aisha. Ba bata lokaci Mr President,  Mai martaba da PA suka dauki hanyar gidan su Aishan.

*
*
*
Tana kwance a dakin ta,  ta kira wayar sa tafi sau nawa bai dauka ba. Mikewa tayi ta cire kayan ta,  ta daura towel sanna ta saka hijab babba ta fita ta shiga bandaki dan Ummah ta hada nata ruwan wanka.. Tana shiga Yaa Muhammad ya fito daga dakin sa sanye da manyan kaga a jikin sa milk shadda kansa ba hula. Dan ranar friday ce. Dakin ta ya nufa yai sallama yaji shiru kawai ya shiga.

Bata dakin dan haka ya tsaya yana bin dakin da kallo zama yayi a gefen katifar ta wayar ta dake kan katifar ya gani ya dauka yana juyawa ya bude ta yana danne danne call log ya shiga sai yaga *Yaa AK* ne last call din da aka kira but ta saka not connected. Ta kira yafi sau ashirin ajiye wayar yayi zuciyar sa na bugawa da karfi da karfi. Can kuma sai ya dauki wayar ya shiga inbox.

Sunan Yaa AK ne a duk list of message din da aka turo shiga yayi yana bi yana karantawa yadda yaje karantawa daga jikin sa gar zuciyar sa rawa suke dan tsabar kidimewa. Kuma ya kasa ajiyewa. Sakonni ne tun wandan ya fara turo mata da wanda yake nuna kulawar sa da soyayyar sa da wanda akai na kwanaki akan tana da wanda take so.

Wayar ya ajiye ba tare da ya fita daga inbox din ba sai kuma ya dauja ya shiga sent message auma duk Yaa AK aka kmturawa. Karanatawa yahi yankoma yana compairig nasu da wanda ya turi ya je kan wani na Yaa AK kawai ya ajiye wayar ba tare da yakarasa karantawa.

Da sallama ta shigo dakin kan ya amsa ta shiga a tsorace ta dafe zuciya dan ba tai zaton ganin kowa a dakin ba. Duk da yana cikin wani hali sai da ya saki murmsuhi ya mikeya na fadin
"Matsoraciyya."

Baki ta turo ta karaso cikin dakin ta zauna tace
"Kai Yaya na ba dole ba ka bani tsoro ban fa san ka shigo ba."

"To sorry na shigo naga bakya nan shine na zauna jiran ki."
"Wanka nayi?"

"Ya jikin?"
Baki ta turo tace
"Sai yanzu kazo dubani bana so. Kana can kana baccin ka baka san ya nake ba ko?"

"Haba Kanwata kema kinsan kina raina jiya banyi bacci bane sai dazu shiyasa."
"Me ya hanaka yin bacci?"

"Tunanin kanwata."
"Haba dai menene na tunani na bayan ni takace ai da kazo kai ta kallo na har baccin yazo kaga ba wani tunani gani gaka ko?"

"Hmmm Aisha kenan."
Ya fada yana murmushi. Baki ta kara turowa tace
"Me nayi?"

"Shirme mana!"
Fuska ta kwabe kamar zatai kuka tace
"Shirme Yayana na fadamaka abinda zaka ji dadi fa."

"Haka ne naji dadin to."
Murmushi ta saki tace
"Naji dadi Yaya na yayi farin ciki."

Sai ta dan bata fuska ta dago ta kalle shi idon ta na kawo kwala. Ya kalle ta yace
"Menene jikin ne?"

Kai ta gyada tace
"Kai nane kuma.kasan me?"
Kai ya girgiza gace
"Yayana gabana sai faduwa yake kuma sai naji ina jin rsoro."

WA NAKE SO?Where stories live. Discover now