Wa nake so? 130

325 29 2
                                    

*WA NAKE SO?* 💝💝💝
130

WRITTING BY MARYAM S INDABAWA
MANS

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
(HAJOW)
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
Email @Maryamsuleiman220@gmail.com

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

Dedicated to my lovelly sis *Nusaiba Suleiman Indabawa*

11:15am
Ta dawo office din nata bandaki ta shiga ta dauro alwala tazo inda take sallah ta shinfidda sallaya ta tada sallar walha raka'a hudu tayi ta sallame ta zauna tana adddu'a. Karfe sha biyu ta mike ta ninke sallayar sannan ta koma ta zauna akan kujerar ta.

Wayar ta dake office din ta dauka ta fara kira. Ana dauka tace
"Bring the files!"

Ta kashe wayar ba ai minti biyar ba ta shigo dakin da files a hannun ta.
"Dr Gasu!"

Ta ajiye akan table din dake gaban ta.
"Mutum nawa zan gani ne?"

"Mutane goma sha daya ne!"
"Sha daya kuma tayaya akai suka haura goma bayan nace kada suna haura goma."

"Dr wani ne yazo ya dinga magiya wai a taimaka a bashi yau ya ganki shiyasa."
"Shikenan."

Ta dauki files din farko tace
"Ki tabbata masu zuwa su shigo a yadda files din yake please!"
"Insha Allahu!"

Nan ta fara ganin patient din da sukai booking ganin ta dan ranar monday sabbin patient take dauka ranar talata kuma masu appointment wanda ta duba zasu dawo laraba ma haka alhamis ma sabbi jumma'a bata duba marasa lafiya sai dai in ita ta ga dama ta baka lokaci.

Kan karfe daya da rabi har ta duba mutum hudu dan haka ta dakatar dan zatai sallah. Sallah tayi ta zauna tai addu'a. Sai biyu ta dawo ta daura daga duba patient din nata.

Karfe uku da rabi ta kara dakatar da masu ganin ta shima dan zatai sallah. Sai da tayi sallah tayi azkhar sannan ta daura akan files din da suka rage guda uku. Na farko ya shigo baiyi thirty minute ba ya fita sai na biyun karshe da ya shigo shine suka dau thirty minute yana mata bayani ta bashi test tace ya dawo ranar laraba.

File na karshe ne a gaban ta lokacin biyar har tayi ta gama yin likis dan gajiya taji wayar ta ta dauki kara dauka tayi  tana duba wake kira. Nusaiba ce dan haka ta saki murmushi tayi sallama. Bayan ta amsa tace
"Nusy nah!"

"Na'am Anty na ina yini ya gida da Momy da aiki?"
"Alhamdulilah aiki gashi har yanzu ban koma gida ba."

"Haba ai na zata kin koma shiyasa na kira!"
"No sauran patient daya daga shi zan tafi gida."

"Ok bari na barki in kin koma gida mayi waya."
"To nagode Nusy agaida Mami!"

"Zataji!"
Ta kashe waya. Waya ta dauka tace
"Next!"

Nan akai sallama. Kan ta na kan file din bata dago ba ta amsa sallamar. Kan ta dago ta kara jin wata sallamar amman ita muryar namiji ne. Dagowa tayi jin muryar very familiar.

Tana dagowa suka hada ido dashi da sauri ta dauke kanta. Sanye yake da Brown kalar suit tai masa kyau sosai kafar sa sanye da sau ciki baki sai necktie maroon kala awuyan sa. Idon sa sanye da farin glass yai masa kyau kan kace me kamshin sa ya cika office din.

Duk da taji muryar mace kuma tana gaban sa amman da ta dago bata lura da ita ba kawai Aslam ta gani. Aslam ne ya kalli Jiddah yace
"Bismillah muje!"

WA NAKE SO?Where stories live. Discover now