Chapter 40

1.1K 205 104
                                    

"Mistakes give you knowledge, hard times give you strength"

♤♤♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

Kamar dai yadda Zayd ya tsara tuni su Abba suka gama shirin su tsab suka hau jirgi sai Saudia.

Wani ikon Allah hankalin Mama yayi masifar tashi.. ta so ace da ita a cikin tafiyar amma ina babu halin tambaya ma balle ta sa ran za'a je da ita.. haka ta dinga fama da baqin ciki. Umma ta riga ta shiga jirgi.

Zayd dai musamman ya damqa ma Abba kudade dayawa don ya ba ma Mama da Layla.. kudin that they can use for their daily needs sannan ya qara sa an loda musu kayan abinci a gidan don dai a fita haqqin su.. Idan ka shiga store din gidan Abba zaka rantse kayan sayarwa ne saboda yawa..

Su Ibrahim kuwa dama dai interview din da suka je yi duk formality ne domin kuwa matsayin Abbu da Zayd a Nigeria ya isa ayi musu alfarma ko wacce iri ce a duk inda suka neme ta. Tuni an basu admission a Islamic Leadership Academy.

Dayake dai dama an riga anyi resuming suma babu bata lokaci Zayd ya kammala musu komai suka tafi.. Aikuwa Mama tana kallo yaran nata suka yi mata sallama suka wuce makaranta abin su.. Zayd da Ameera ne suka raka su har Abujan.

Su Ammi kuwa sun ji dadin ganin Ameera, Musamman 'yan biyu. Its the first time she visited tun auren.. Ameera dai ta ga soyayya wurin dangin miji.. sai nan nan ake yi da ita, abin har mamaki yake bata.. ko da wasa bata taba mafarki irin wannan rayuwar ba.

Sai da suka yi kwana uku a Abuja sannan suka dawo a dalilin makarantar Ameera.

Kwana biyu kacal da dawowar su daga Abuja kuwa aka tafi indefinite strike a makarantar su Ameera.. Hakan kuwa ba qaramin dadi yayi ma Zayd ba domin kuwa it's the perfect time for them to travel out of the country for their honeymoon especially because ya samu sauqin aikin shi a 'yan kwanakin nan.

Ba tare da bata lokaci ba kuwa ya shirya musu tafiyar su shi da Ameera zuwa qasashe biyar England, Switzerland, Greece, Dubai da Saudi Arabia..

A cewar shi duk lokacin da aka yi calling off strike din sai su sa pause su dawo idan yaso they will return and continue during mid-semester...

Sai da suka koma Abuja suka yi ma su Ammi sallama sannan suka bar qasar..

Fatan mu Allah ya dawo da su lafiya... Ameen!

♤♤♤♤♤♤♤♤

One week later!!

FAROUQ ABDALLAH RESIDENCE
MALALI GRA

A yau sati daya kenan da su Ameera suka bar qasar.

Tsaye take a gaban wadrobe dinta yayinda take jera kayan ta.

Layla dai tuni ta kwashe kayanta ta kai ma tela yayi mata 'yan dabaru a kai... Allah ya taimake ta dama yawanci kayan suna da allowance a ta ciki don haka duk wadanda suka matse ta an bude su.. haka masu manyan wuya duk an rage.. wadanda kuma ba'a iya yi musu dabara ta sallamar da su.

Kudaden da Abba ya bata na kashewa a school kuwa masu yawa ne.. (Kudaden da ta sani sarai daga wurin Zayd suka fito) a ciki ta cire ta siya sabon atamfofi ta bayar za'a yi mata decent dinkuna masu rufe jiki sannan ta siya manyan veils different colors.. su ma irin wanda ke rufe jiki dinnan.

Tana nan tsaye ne ta ji qarar qofa.. ko bata kalla ba ta san Mama ce tunda dai daga ita sai ita a gidan..

Ba tun yau ba Mama take shigowa dakin Layla tayi ta magana har ta gama amma Layla bata ko kallonta balle ta amsa ta.. Gaba daya Layla haushin Mama take ji don kuwa ita ta sanya ta a halin da take ciki.

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now