Chapter 7

929 190 68
                                    

“They plan, and Allah (God) plans. Surely, Allah (God) is the best of planners.”
~~~Quran 8:30~~~

♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

Cikin dan qanqanin lokaci Habib Aliyu Nasidi ya canza ma Layla rayuwa.

Tuni ya bata sabuwar waya.. qirar Samsung Galaxy S10. Habib ya kula cewar Layla is from a poor family.. ya sani cewar idan har yana so tayi matching social class dinshi dole ne sai yayi polishing dinta..

Sossai ya dinga sakar mata kudi.. kudaden da yake bata kuwa tun tana lissafa yawan su har ta daina.

Da zarar ya bata kudi sai ta kawo ma Mamanta.. A nan dakin Mama suka samu wadrobe suna ta zubawa cikin Ghana-must-go.. sai dai kawai idan hidima ta taso su bude su cire.

Tuni ta siyo manyan atamfofi Super wax, manyan lesussuka, manyan shaddoji getzner da materials masu tsada kala-kala ta bayar dinki.

Jakkuna da takalma ta siyo su dayawa su ma.. Ga jewelries masu kyau da tsada

A yanzu haka Layla ta zama first class babe.. sossai ta dace da clique dinta- Maryam, Haleema da Yusrah.

Tunda ta hadu da Habib ta daina bin Ameera makaranta a Napep.. kullum shi yake zuwa ya dauke ta ya kai ta sannan ya dawo da ita. Akwai lokacin da baya nan ma driver ya aiko ya dauke ta ya kai ta.

Duk wannan hidimar da ake yi Abban su baya da labari saboda a bayan idanuwan shi ake yi. Bai ma san Habib ba sannan bai san yana zuwa ba... dayake lokutta da dama a makaranta suke haduwa.

Umman Ameera batayi mamakin abinda yake faruwa ba tunda dai dama Ameera ta bata labarin komai. A kullum dai tana cikin yi ma 'yarta nasiha akan lallai ta tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ta.. kar ta sake ta bari halayen Layla su rude ta. Banda kwadayi da son abin duniya... Duk mai kwadayi babu inda mota take sauke shi sai tashar wulaqanci.

Gaba daya Layla ta daina sauraron Zayd.. tun ranar da ta hadu da Habib ta fita batun shi gaba daya.. Sai ya zo sau biyar amma da qyar take fitowa sau daya.. shima din idan ta fito ba wata maganar arziki ke fita daga bakin ta ba.. banda cin mutunci da wulaqanci babu abinda take yi mishi.

Lokutta da dama haka zai dauki jiki ya je har gidan su ya aika a kirata amma sai ta qi fitowa. Hakan kuma bai hana shi dawowa gobe.

ikon Allah!!

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

One month later..

A yau ne ake bikin kamun qawar Layla mai suna Bilkisu.

Layla dai a dalilin tana so ta nuna ma qawayenta ta zama babbar yarinya sai bata dinka Chiganvy wax din da Zayd ya kawo mata ba.. instead sai ta siyo irin atamfar sak amma Super wax tayi mata wani shegen dinki mai kyau da tsada.

Chiganvy din ma wata qawar su ta ba kyauta don tana ta complain akan bata samu kudin siyan anko din ba.

Layla ta so ta gayyaci qawayen ta su Haleema amma ta sani sarai bazasu so irin bikin ba tunda dai tana ganin hotunan irin bukukuwa na manyan mutane da suke zuwa.

A Arewa house za'ayi bikin kamun.. dayake tayi planning tare da Habib zata je sai ta sanar da qawayen ta (Su Ramlatu..) kar su jira ta kawai zasu hadu a event hall din.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

AREWA HOUSE
RABAH ROAD

Mutane ne tsaye a waje yayinda ake jiran isowar amarya don a tsara yadda za'a shiga hall din..

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now