Chapter 25

1.1K 171 67
                                    

"And whoever puts all his trust in Allah (God), then He will suffice him.”
~~~Quran 65:3~~~

♤♤♤♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH
MALALI

Jiki a sanyaye Layla ta iso gida.. Da qyar take tafiya yayinda take bin bango.. Jiri ne yake ta diban ta.. Ko da ta shiga gidan babu kowa a falon don haka straight dakin Mama ta wuce.

Mama tana Zaune akan gadon dakinta tana waya da Hajiya Suwaiba wadda suke hiran wata sarqar gwal da ita Mama take so ta siya.

Ganin Layla ta fado mata a gigice ne tayi saurin yin sallama da Hajiya Suwaiba tare da fadi mata zata kira ta anjima.

"Ke lafiya kike kuwa???"

Da sauri ta miqe ta nufi wurinta ta kamo ta.. Hankalinta ne yayi mugun tashi a dalilin jin jikin Layla da tayi ya dauki zafi sossai har tana kyarma.. Ga hawaye da ke ta bulbulowa daga idanuwanta..

Janyo ta tayi ta zaunar da ita kan gado sannan ta zauna a gefenta itama a rude tace "kenan dai dagaske shine??"

Layla dai rushewa tayi da kuka yayinda tace "na shiga uku Mama, Wallahi shine.. Zayd ne.." Daga nan ta bata labarin wulaqancin da yayi mata harda ma wanda Bilal ya dora a kai..

Mama dai salati ta shiga yi tare da dafe kai.

"aikuwa dai wannan yaro bai kyauta mana ba da ya boye mana asalin shi.. lallai wadancan munafukan sun sani sarai shiyasa suka maqale mishi.."

"Wallahi Mama bazan bari ta aure shi ba.. idan dai har ba ni zai aura ba toh wallahi itama bazai aure ta ba"

"sha kurumin ki Layla.. ai dole ne in tashi tsaye akan wannan lamarin.. tunda abin ya zama haka dole ne in hada da neman taimako. Bari yanzu zan kira Hajiya Suwaiba dama kwanaki ta bani labarin malaminta wanda yake taimaka mata a al'amuranta na yau da kullum.. sai mu ji ko zai iya taimakon mu akan wannan. Dama dai harka ce ta kudi kuma muna da shi.."

"Yauwa Mama, kawai ina so a karkato hankalin shi zuwa gare ni ya aure ni.. Ni dai buri na shine a raba su.. idan ma haukatar da ita za'ayi ko sheqa ta lahira zai yi wallahi I dont care.. I only want Zayd for myself" ta fada yayinda take share hawayen fuskarta.

"Kar ki damu Layla ta.. idan har na nemi taimako a wurin malamin Hajiya Suwaiba na tabbatar zamuyi nasara.. Yanzu dai kwanta ki natsu ki huta sannan ki cire damuwa a ran ki..  Zayd dai baya da Matar da ta wuce ke"

Layla ta qarasa hayewa kan gadon ta kwanta yayinda Mama ta tashi tana fadin "banda sakarci irin nashi ma ai bai kamata ya gwada mace ta haka ba.. waye zai je wurin budurwa a talauce? ta ya zata saurare shi?? da ya fito a asalin shi ma ai da yanzu an sha bikin naku.. ki more arziki ya more kyakyawar Mata. ita kanta baqar banzan can na tabbatar ta san ko shi waye ne shiyasa ta maqale mishi din, na rasa yadda aka yi shi kuma ya amince da ita duk munin ta.. Qila ma asiri suka yi mishi shegu dangin mayu, Zan karya shi kuwa"

Layla dai ta dan ji sanyi a ranta a dalilin wannan shawarar ta Mama.. A yanzu ta fara jin qamshin zata zama matar Zayd.

Gani nayi Mama ta dauki wayarta ta kira Hajiya Suwaiba.

toh fa...

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ZAYD AHMAD FADOUL'S MANSION
UNGUWAN RIMI GRA

Wuraren qarfe biyar saura yana tsaye a makeken kicin din gidan wanda ya hadu iya haduwa yana qoqarin kammala Chicken and cheese salad din shi.

Zayd dai rabon shi da abinci a yau tun breakfast din safe.. Yinin yau din suna cikin meeting tare da clients dinshi da suka zo daga Kano.. he was so busy that he didn't even had the chance to eat lunch don haka da yunwa ya dawo gida.

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now