Chapter 13

962 176 77
                                    

 “The best among you are those who have the best manners and best character.”
~~Sahih Bukhari 6029~~

♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

Days later!!

A yau Saturday, Yau ne birthday party din Habib.. Layla dai tayi ma Mama bayanin komai amma bata fadi Mata cewar 'all night long' bane.

Ta dai fadi mata cewar za'a kai qarfe Goma na dare don haka ne zata bi Haleema gidan su ta kwana a can saboda kar Abba yayi fada.

Aikuwa tuni suka tsara abinda zasu ce ma Abba.

Sun yi da Mama akan tayi ma Abba qaryar yayar qawarta zata yi aure don haka ne qawarta ta gayyace ta. Da farko Abba ya hana ta kwana tunda dai bikin na yayar qawa ce ba na qawa ba..

Sai da Mama ta sa baki suka dinga roqon shi sannan ya amince.. Ya ja mata kunne akan banda shashanci.

Umma da Ameera dai sun sani sarai cewar qarya suka yi.. Sun sani cewar birthday party din Habib zata je amma dayake ance baqin ciki suke yi sai suka ja bakunan su suka yi shiru..

Da yamma kuwa Layla ta shirya tsab tayi ma Mama sallama ta tafi..

Dama dai sunyi da Haleema zata je gidan su sai su wuce daga can..

Abin mamaki gaba daya qawayen nata basu taba zuwa gidan su ba amma ita tana zuwa gidajen su musamman gidan su Haleema tunda sun fi shiri.

Sun riga sunyi shopping na kayan da zasu sa daga wani classy boutique wanda suka bari a gidan su Haleema tunda a can zasu shirya.

Maryam da Yusrah dai sun ji labarin Birthday party din kuma an gayyace su amma suka ce bazasu je ba... dama dai su ba ma'abota zuwa party bane.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI IDRIS BUNGUDU'S MANSION
UNGUWAN SARKI

Zaune suke a tangamemen dakin Haleema wanda yake cike da kayan jin dadi na zamani yayinda Lubabatu CEO ta blush beauty take yi ma Layla make up.

Musamman suka gayyaci Lubabatu don ta tsantsara musu kwalliya.. Sossai suke so su fi kowace macen da zata halarci partyn kyau.

Dayake dama iyayen Haleema sunyi tafiya babu kowa a gidan sai masu aiki.. ko dama idan suna nan ba hana ta fita zasu yi ba tunda dai sun shagwaba ta.. duk abinda take so shi take yi.

Haleema wadda aka riga aka gama mata nata tana zaune a gefe ce tace "Layla yakamata idan mun tashi zuwa kar mu je da wuri saboda ina so kowa yayi acknowledging presence dinmu.. especially you- babe din Celebrant din. Ko ya kika ce??"

"Haka za'ayi Leema.."

Bayan an gama ma Layla ne ta juyo ta kalli Haleema tace "Leema ya kika gani???"

"wow.. Babe kin gan ki kuwa??? I swear ke kyakyawa ce ta bala'i.. dole Habib ya sukurkuce akan ki. You look absolutely beautiful"

Lubabatu wadda take qoqarin arranging kayan aikinta cikin kit tana murmushi tace "I agree with you ma'am.. she is super gorgeous.. I am so looking forward to having more sessions with you"

Layla tana murmushi tace "you got it Lubcy.. thanks"

Haleema ce tayi ma Lubabatu transfer na kudin aikinta zuwa bank account dinta.. tayi musu sallama ta tafi abinta.

Daga nan ne suka fiddo kayan da zasu sanya suka fara shiri.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

HABIB ALIYU NASIDI RESIDENCE
MARAFA ESTATE

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now