Chapter 3

1.1K 231 42
                                    

“Never underestimate the power of Dua (supplication).”
~~~Anonymous~~~

♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

Bayan wata daya da auren su ne Sameera tayi shawara da Farouq akan tana so ta fara sana'a da kudin gadon ta.. ta tsayar da shawarar fara kunun aya saboda ta kula mutane suna siya sossai..

Yayi farin ciki da jin hakan. Ya tabbatar Sameera ba lazy mutum bace kamar Hindatu.

Nan da nan ta bayar da kudi aka siyo mata 'yar madaidaiciyar deep freezer, buhun aya da na sugar, bottles, flavour da duk wasu abubuwan da zata buqata.

Tuni ta fara yin kunun ayan ta.. tayi ma makwabta talla... Kunun ayan Sameera yana da masifar dadi.. hakan ya sanya nan da nan kasuwa ta bude mata. Idan tayi kunun aya kafin kace kwabo ya qare.

Duk qarshen wata idan ta hada ribarta sai ta ba Farouq ya zuba mata a account dinta.

Hindatu dai tana nan zaune babu aikin fari bare na baqi.. sai tijara da baqin hali.

Sossai Sameera take son Layla amma Hindatu ko daukar ta bata bari tayi.. Haka Sameera zata shiga kasuwa ta ga abubuwa ta siyo ma Layla ta kawo kuma babu kunya sai ta karba babu ko godiya.. tun halin Hindatu yana ba Sameera mamaki har ta daina.. Yau da gobe ma sai ta saba!

Lokutta da dama idan Farouq baya da kudi a hannun shi, Sameera ce take bashi.. Tabbas to him Sameera is a blessing in disguise.

A lokacin da suka yi wata hudu da yin aure ne Sameera ta samu ciki... kamar yadda yayi murna lokacin cikin Layla haka yayi wannan karon.. duk abinda Sameera take buqata kuwa yana kawo mata dukda ma lokutta da dama ba tambaya take yi ba.

A wannan lokacin ne Farouq ya dakatar da ita akan sayar da kunun aya saboda baya so tana wahala..

☆☆☆☆☆☆☆

A lokacin da cikin Sameera ya kai wata tara daidai ta haihu.. ta haifi 'yarta mace wadda ta ci suna Ameera.

Hindatu dai ganin yarinya baqa kamar uwarta ta dinga dariya tana fadin 'yarta dai ta fi kyau sannan duk inda aka hada su 'yarta za'a zaba.

Wannan kalaman na Hindatu suna matuqar ba Sameera mamaki.. wani lokaci kamar takan manta cewar Allah ya halicci kowa da komai yadda yake so.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

A haka dai shekaru sukayi ta tafiya. Tuni Hindatu ta qara haihuwa yara maza guda uku.. Ibrahim, Munnir da Suleiman.

Ita kuwa Sameera namiji daya kawai ta qaro wanda ya ci suna Aliyu Haidar. Aliyu ya kasance tsaran Munnir don haka kan su daya.

Tunda yara maza na gidan suka taso kawunan su a hade suke.. Ibrahim, Munnir, Suleiman da Aliyu tare suke yin komai. Abban su ya gina musu daki mai dan girma a waje suka yi zaman su a ciki yayinda ya qara dakuna biyu attached to the main house.. Ya dauki daki daya sannan ya bar ma yara mata dayan dakin.

A bangaren 'yan matan kuwa tunda suka taso Mama (Hindatu) ta sanya ma Layla qiyayyar Ameera da Ummanta (Sameera) a cikin zuciya. Layla ta girma bata qaunar Ameera da mahaifiyarta.

Har a wannan lokacin kuwa Umman Ameera bata daina yi ma Layla da Mamanta abin alkhairi ba.. Duk wani abinda ta siyo ma 'yarta sai ta siyo ma Layla kuma su karbe babu ko godiya. Hakan kuma bazai hana anjima suyi ta jefo musu baqaqen maganganu ba.

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now