Chapter 6

971 201 51
                                    

"The Life of this world is merely enjoyment of delusion"
~~~Qur'an 3:185~~~

♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

KADUNA STATE UNIVERSITY

A yau ne wani saurayin Haleema mai suna Yusuf Suleiman Mayana zai zo ganin ta. Asali yakamata ya je gidan su ne amma kuma tafiya ta taso mishi zuwa Russia wanda mahaifin shi ne ya aike shi don haka ne zai zo school don suyi sallama.

Yusuf dai yana cikin samarin Haleema da take ji da shi domin kuwa gayen yayi ne ta ko'ina. He is handsome, rich and sophisticated.

Tana zaune a garden tare da qawayen ta ne ya kira ta a waya tayi mishi kwatancen inda take.

"Yau dai Layla zata ga Yusuf dina.. " cewar Haleema.

Layla tace "tabbas yau zan gan shi.. na kula kina ji da shi ai.."

Yusrah ta tabe fuska tace "hmm.. ni kam duk gani nake yi bata lokaci ne tsayawa sauraren samari idan ba wai na shirya auren bane"

Maryam tana dariya tace "Yussy kenan.. Allah dai ya kai mu ranar da wani zai sace zuciyar ki, I swear we wont hear word"

Suna nan zaune suka hango shi a parking lot inda ya faka motar shi. Wata dalleliyar Lexus jeep mai kyan gaske, sai walqiya take yi.

Gani nayi Haleema ta miqe tace "babes let's go"

Zaune suke cikin motar tare da abokin shi mai suna Habib Aliyu Nasidi. Habib Aliyu Nasidi yaro ne a gidan Alhaji Aliyu Nasidi, tsohon senator. Habib ba fari bane sannan ba baqi bane, yana da kyau sossai sannan da ka gan shi ka ga hutu.. Ya masifar iya gayu shiyasa mata suke bala'in son shi.

Habib da Yusuf suna daya daga cikin manyan yara a cikin garin Kaduna.. A yanzu haka tunda suka kammala karatun su babu abinda suke yi sai kashe kudin iyayen su... babu aikin fari bare na baki. Iyakan su suyi ta kashe ma 'yan mata kudi sannan su ziyarci night clubs suyi sharholiyar su da 'yan mata.

"Abokina nayi gamo.." yayinda ya qura ma Layla idanuwa wadda suke dosowa wurin su tare da su Haleema.

"a ina??" Yusuf ya tambaye shi in a confused tone.

Yayi pointing at Layla yace "waccan farar, wallahi ina son ta kuma I dont care ko wacece, I dont care whether she is married.. I just like her and she has to be mine"

Yusuf ya fashe da dariya yace "Shege Romeo.. you've got all it takes to woo her ai.. I trust you. let's find out who she is"

A lokacin da suka qaraso ne Yusuf ya bude qofar shi ya fito..

Abinda ya faru next shine ya masifar ba su Layla mamaki..

Gani sukayi ya bude hannuwan shi yayinda Haleema ta qaraso da sauri ta shige tare da hugging dinshi..

"Babe how are you doing?"

cikin shagwaba tace "I am fine.. yanzu daga dawowa jiya kuma sai yau kace mun zaka tafi Russia?? Gaskiya Daddy baya kyauta mun"

Kafin yayi magana ne ya ji muryoyin su Maryam suna gaishe shi..

Yusuf ya riqe Haleema ta gefen shi yayinda ya jingina da motar sannan ya amsa gaisuwar su.

"Ya school??"

Maryam ce tace "lafiya lau"

Haleema tace "sweetheart these are my friends.. wannan itace Maryam, ga kuma Yusrah sai Layla.."

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now