Chapter 2

1.3K 221 37
                                    

The bravest heart is the one that stays close to Allah (God), even, when it’s in pain.” ~~~Anonymous~~~

♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

WAIWAYE....

Malam Farouq Abdallah ya kasance mutumin Kano ne. Mahaifin shi Malam Abdallah baya da qarfi sossai don kuwa sana'ar trader yayi a wata kasuwa ta kusa da su. Asali Iyayen Abdallah sun haifi yara guda hudu ne.. Farouq shine babba kuma shi kadai ne namiji. Sauran duk Mata ne: Aminatu, Khadeeja da Zainab.

Farouq shi kadai ya samu zuwa makaranta domin kuwa Mahaifin su baya da halin biyan kudin makaranta.

Shi kanshi Farouq din sai da ya hada da aikin qarfi wanda anan yake samun 'yan kudaden da yake hadawa ya biya kudin makarantar shi.

Yayi karatun primary da secondary dinshi a nan cikin garin Kano. Daga nan ya wuce BUK inda yayi karatun jami'ar shi.. Ya karanta Economics ne a bangaren Education.

A wannan lokacin kuwa tuni qannen shi sunyi aure.

Aminatu tana gidan mijinta a Sokoto sai Khadeeja da Zainab suna aure a nan cikin garin Kano.

Bayan Farouq ya kammala karatun jami'ar shi ne ya fara neman aiki.. Kamar dai yadda kuka sani samun aiki a qasar mu abu ne mai wahala musamman idan baka san kowa ba.. Ga mahaifin su ya tsufa.. sana'ar trader din ma Farouq ne yake dan taimaka mishi yana zama a shagon.

A haka ne har Allah ya taimake shi ya samu aikin teaching a wata makarantar private a nan cikin unguwan su.. Dukda dai albashin babu yawa...

Dayake Farouq yana da qoqarin neman na kan shi bai yi sanya ba wurin cigaba da neman aiki.. A hakan ma idan an tashi daga makarantar yana zuwa koyar da wasu yara lesson a gida da yamma.

Sai da yayi kusan shekara daya da rabi yana koyarwa a makarantar private din wata rana kwatsam sai aka aiko mishi da letter daga Garin Kaduna cewar an dauke shi aiki a State ministry of Education ta Kaduna.

Farouq yayi murna sossai da samun wannan aiki. Ai kuwa nan da nan ya tafi Kaduna yayi documentation dinshi gaba daya sannan ya dawo Kano yayi resigning a private school din da yake teaching.. Inda Allah ya taimake shi dama wata saura kwana biyu ya qare don haka suka yi mishi alqawarin zasu biya shi salary din dukda a qa'idance shi yakamata ya biya su albashin wata daya in lieu of notice kamar yadda yake a rubuce toh amma Farouq was a hardworking teacher and the least they could do was pay him as gratitude..

Bayan dan lokaci kuwa Farouq ya tattara tsab yayi sallama da iyayen shi ya koma garin Kaduna.

Dayake akwai sabbin gidaje da gwamnati ta gina tana raba ma ma'aikatan ta masu so sai kawai ya karbi daya wanda a cikin albashin shi za'a dinga cire wani percentage har tsawon shekarun da zai gama biya ya mallaki gidan.

A wannan lokacin kuwa Farouq ya so iyayen shi su dawo gidan nashi su zauna tare amma Sam suka qi. A cewar su tunda dai gidan da suke ciki nasu ne gwara suyi zaman su.. Shawara suka bashi akan lallai ya fitar da mata yayi aure... tunda dama muhalli shine babban matsala kuma ya samu.. Da wannan ne kuwa Farouq ya fitar da yarinyar da ya dade yana nema.

Hindatu yarinya kyakyawar gaske.. Asalin Mahaifinta dan Kano ne amma mahaifiyarta 'yar Qasar Niger ce...

Hindatu Fara sol mai dogon gashi.. tana da jiki mai kyau... Gaba daya ta dauko Kamarnin mahaifiyarya. Tunda Hindatu ta taso ta ga tana da kyau ne take masifar ji da kanta.. Girman kai gareta na bala'i.

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now