Chapter 9

912 215 88
                                    

"And whoever turns away from My remembrance - indeed, he will have a depressed life."
~~~Quran 20:124~~~

♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

Days later!

HABIB ALIYU NASIDI RESIDENCE
MARAFA ESTATE

Zaune suke a tangamemen falon gidan shi suna ta hira. Yawancin hirar tasu duk ta 'yan mata ce da kuma rayuwarsu ta sharholiya da suka dulmiya a ciki.

"abokina wallahi ta matsa mun akan lallai Abbanta yace inyi introducing kaina kuma gaskiya I am scared.. ya kake gani ne???"

Yusuf wanda yake kwance kan doguwar kujera 3-seater ne yace "gaskiya kar ka kuskura ka je don kuwa duk ranar da ka samu Layla kamar yadda kake so sannan daga baya abubuwa suka dan birkice za'a yi tracing dinka. Ni na rasa meyasa ka kasa exploring dinta har yanzu.. yau fa sama da wata daya kenan da haduwar ku. Haba Habib.. ni da na san ka at most 3 days ka aiwatar da komai amma ace ka kasa yin komai har yanzu"

Habib ya dan sosa kan shi yace "ai baka gane ba, yarinyar tana da dan taurin kai ne.. dukda she is a bit loose ina gani kamar upbringing din da aka yi mata was kind of strict.. a hankali nake bin ta don bana so in nuna yunwa ta a fili.. initially idan na taba hannunta, jikinta har rawa yake yi but ka ga da nake bin ta ahankali yanzu har kiss ina yi mata a kumatu kuma bata damuwa.."

Ya saki ajiyar zuciya yace "oboy, akwai ranar da na shafa boobs dinta.."

Ya lumshe idanuwa ya bude tare da hadiye wani miyau na tsaban maita sannan ya cigaba da fadin "...wallahi laushin bala'i kamar pillow.. Na rantse maka da Allah duk ranar da na samu Layla sossai zan gurje ta.."

Yusuf yana murmushi yace "I think I will be on queue.. idan ka gama da ita nima a bani in dana"

Habib ya fashe da dariya yace "Wallahi idan Leema ta ji labari babu ruwana.."

"bazata ji ba abokina.. afterall itama ai ina kyautata zaton tana holewa da wasu mazan ba ni kadai ba.."

"toh koma dai meye Layla tawa ce ni kadai.. saboda ina tunanin nan gaba auren ta zanyi" cewar Habib.

"what??? wallahi inaaa.. ai babu yadda za'ayi in auri macen da na gama sanin ta a kan titi. Sabuwa gal zan auro.."

"kuma fa da gaskiyarka abokina.. toh amma kuma ina son Layla"

Yusuf ya ja tsaki tace "soyayyar banza?? ni dai ina qara jaddada maka kar ka kuskura ka je wurin mahaifinta don wallahi zaka daure kanka.. if things should go haywire babu ruwana"

Haka dai suka cigaba da hirar su.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH
MALALI

Wuraren qarfe takwas na dare Layla tana kwance a kan gadon dakin su tana chatting da qawayen ta yayinda call din Zayd ya dinga shigowa tana rejecting.

A lokacin Ameera tana zaune a kan nata gadon tana karatu na wani test din da zasu yi jibi.

"Allah ya sani ka cika naci Zayd.. ni wallahi na gaji da kai. wai ana soyayya dole ne??? dagaske blocking din layin shi zanyi kawai.." ta fadi tare da jan wani mugun tsaki.

Ameera wadda zuciyarta take ta tafasa ce ta kalle ta cike da takaici tace "Haba Ya Layla.. meye laifin Ya Zayd ne?? don kawai yana son ki??? shin hakan laifi ne?? don Allah kar kiyi blocking dinshi.. kiyi haquri"

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now