Chapter 34

1.4K 233 93
                                    

“The Worst of our faults is our interest in other people’s Faults"
~~~Ali Ibn Abi Talib~~~

♤♤♤♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

ZAYD AHMAD FADOUL RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA

Zaune suke a falonta suna hira da qawarta Zarah..

Duka awa biyu kenan da Zayd ya tafi Lagos wanda jet dinshi na sauka ko fitowa bai yi ba ya kira ta a waya.

Yau din ita ce rana ta farko da suka samu zama bayan bikin ta.

"don Allah qawata kiyi haquri.. ni kam ba komai ya wuce ba yanzu??" Zarah ta fada cikin muryar roqo.

"eh komai ya wuce amma ai raina mun wayau kuka yi.. tell me something, since when have you known?" Ameera ta tambaye ta yayinda ta sa mata idanuwa.

Zarah tana murmushi tace "wallahi tun ranar da yayi proposing miki.."

"what??? you mean tun ranar Zarah?? and you didnt tell me?"

"Haba qawa ta.. da bakin ki fa kika fadi mun cewar bakya son auren mai arziki.. mun ji tsoro ne kar ki qi amincewa da shi.."

"aikuwa kun yi playing dina.. Ni kam I am glad na zama matar Ya Zayd kuma ya bani assurance din da nake nema... Kin ga dazu fa da zai tafi ya so mu je tare amma na qi.."

"what??? kenan kin gwammace ki zauna a nan shi kuma yana can??"

Shiru Ameera tayi yayinda take tunani.. ita kanta fa sai da ya tafi ta ji dama ta bi shi, Sossai tayi missing dinshi musamman da ta gan shi ta video call.

"Ke qawata, saurare ni ki ji.. a duk lokacin da zai yi tafiya ya nemi ku je tare please follow him.. ke close marking sossai yakamata ki dinga bashi.. duk wata kunya fa a yanzu ajiye ta zakiyi a gefe.. wannan soyayyar da kike yi mishi ita ce zaki zage ki nuna mishi.. yanzu da kika zauna a nan me kike yi? ke ba makaranta kike zuwa ba.. kina nan zaune a gida" ta harare ta sannan ta cigaba da fadin "ko dayake ba laifin ki bane.. baki shiga sahun matan aure bane tukun shiyasa.. da kin dandana wannan rayuwar wallahi na tabbatar maqale mishi zakiyi kamar chewing gum"

Ameera wadda take kallon Zarah with a straight face ce tace "toh yanzu dai the damage has been done.. zan kiyaye gaba"

"yauwa qawa ta.. yanzu ma bata baci ba, Bari in kira miki wata mai gyaran jiki ta zo ta shirya ki kafin ya dawo jibin.. tunda dama ba'a kammala wancan ba kika samu accident din da har kika kwanta jinya.. ko baki so??"

"ina so qawa ta.." Ameera ta fada kai tsaye yayinda Zarah ta fashe da dariya tace "da kyau juliet.. na ga alama Yayana will be in trouble kenan"

Ameera tana dariya tace "ke toh son shi nake.."

"na fi kowa sanin haka"

Aikuwa anan Zarah ta kira Aina'u Marwan.. wata shaharariyar mai gyaran jiki ce wadda tayi fice a garin Kaduna.. dayake harka ce ta kudi nan da nan ta nemi address sannan tace tana nan zuwa in the next 3 hours.

Bayan ta kashe wayar ne tayi ma Ameera bayani.

"nagode qawa ta" Ameera ta fada

"Meye abun godiya Ameera?? we are like sisters remember??"

Kafin Ameera tayi magana ne Zarah tace "ni kuwa ban tambaye ki ba.. ya labarin Layla??"

Ameera ta turo baki tace "toh wa ya sani.. jiya da muka je gida na ganta.. ko magana batayi mana ba ta wuce daki and daga nan bata qara fitowa ba.. I swear qawata tun ranar da tayi threatening zata kashe ni saboda Ya Zayd har yanzu tsoron ta nake ji.. tunda tana da saurayinta mai kudi ta haqura mana.."

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now