EPILOGUE II

1.6K 216 109
                                    

Every action has equal and opposite reaction. This is law of the universe and spares none. Wrong done and injustice inflicted is paid back in the same coin. No one has escaped justice of the universe. It is only a matter of time."

✍ZABI NA✍

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

FLASHBACK!!!

A lokacin da su Ameera suka ji labarin hatsarin Layla an sanar da su cewar tana raye amma unconscious don haka su je asibitin St Gerrard.

Ba tare da bata lokaci ba Zayd da Ameera suka nufi asibitin.. A asibitin ne ake sanar da su cewar wadanda suke tare a motar duk sun mutu.. Wato Haleema da Tukur!

Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un..

Haleema ta rasu ba tare da ta gyara hali ba, ta rasu tana kan hanyarta na aikata mummunan aiki.. Ya Allah kar ka sa mu zamo masu aikata munanan ayyuka a duniyan nan Ameen.

A yadda labari ya zo daga eye witness an ce tyre ce ta fashe shine motar tayi losing control ta fada daji..

Ko da suka samu ganin Layla ta farfado kuma bata wani ji ciwo ba domin kuwa kanta ne da ya dan bugu sai targade da tayi a hannu da kuma scratches here and there on her body... and she had already been treated accordingly.

Babu abinda take rusawa banda kuka jin cewar qawarta Haleema ta rasu.. Yanzu shikenan Haleema ta tafi a cikin wannan hali.. yanzu me zata ce ma ubangijin ta idan ta tsaya a gaban shi???

Ameera ce ta dinga lallashinta yayinda Zayd ya gama formalities na transfering dinta to Garkuwa hospital tunda dai wannan asibitin is far from cikin gari..

Ko da suka kamo hanya Layla ta roqe su akan su kai ta gida domin kuwa all she wanted a wannan lokacin was to seek forgiveness from everyone (musamman Abba) because bata so ta mutu ba tare da ta nemi yafiyar su ba.

Ko da suka isa gidan kuwa Abba bai saurare ta ba.. asali ma korar ta yayi daga sashen shi yayinda yace ta nemi wani uban ba shi ba... hankalin ta kuwa ya tashi matuqa da jin kalaman Abba.. tayi kuka babu sassauci. Ameera da Umma sune suka dinga lallashinta Yayinda Zayd ya dinga ba Abba baki amma sam ya qi sauraron shi.. Babu shakka Abba yayi fushi sossai!!

Ni kuwa nace 'who wouldn't?'

Sai a lokacin Mama take jin abinda yake faruwa.. Cike da borin kunya ta nufi sashen Umma wurin Layla amma a gaban kowa Layla ta fara fadin abubuwan da Mama ta sa ta dinga aikatawa wanda har shaidan ya ingizata ta fada mummunan aiki-ZINA. Daga nan ta kore ta akan bata so ta qara ganin ta.. sannan she made it clear to her cewar she should consider her dead!!

Su Umma basuyi mamakin jin abubuwan da Layla ta fada ba domin kuwa sun sani cewar Mama can do anything for money.

Anan dai Layla ta nemi yafiyar Umma da Ameera akan abubuwan da tayi musu.. a ciki kuwa harda ture Ameera da tayi wanda yayi sanadiyyar kwanciyarta a asibiti kafin aurenta da Zayd.

Daga Umma har Ameera sun yafe mata domin kuwa a halin da ake ciki a wannan lokacin she is in a much bigger problem than that.. Sun lallashe ta akan ta kwantar da hankalinta har Abba ya sauko.

Layla dai a nan sashen Umma tayi zaman ta.. Umma ta kula da ita sossai, bata nuna qyama a gareta ba ko kadan.. sabanin yadda mahaifiyarta ta nuna mata.

Ko da Ameera ta fadi ma Zayd abinda Layla tayi mata he wasn't surprised domin kuwa ya sani.. lokacin da suke asibiti suna magana da ya zo wucewa he heard them talking about it and that was when he decided to just marry her dukda she was unconscious don ya ga tsiyar su! Ameera tayi mamaki matuqa na yadda Zayd bai taba fadi mata ba.. he really is a peaceful guy!!

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now