Chapter 35

1.8K 224 126
                                    

If you don’t intend to marry her, Keep your hands off another mans Future wife.
If you do Intend to marry her, Keep your hands off until she is your wife

♤♤♤♤♤♤♤

✍ZABI NA✍

washegari!!

ZAYD AHMAD FADOUL'S RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA

Zaune yake a kan Ottoman na gadon dakin shi wuraren qarfe takwas da rabi na safe yayinda yake riqe da wayar shi yana video call da Zaheera.

Zayd dai ya farka bai ga Ameera ba.. da alama ta riga shi tashi ta bar dakin. Ciwon kan shi kuwa Alhamdulillah domin dai tun jiya da Ameera tayi mishi adduo'i ya samu sassauci sossai, a yanzu kuwa da ya samu one of the best sleep of his life sai ya warke garau.

A yanzu haka yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya na three quarter da T-shirt ne kiran Zaheera ya shigo wayar shi.

"Sweetheart ina ta kiran ka a waya jiya ka share ni ko? wallahi I was worried ne, na ji jikina babu dadi and I sensed you might not be feeling well.. na kira wayar matarka ita ma she wasn't picking"

"Sweetheart don Allah kiyi haquri, jiya kai na ya dinga ciwo.. na sha wahala sossai, ban ma san inda wayoyin suke ba.. Habibty kuma I am sure ta bar nata a dakinta ne.."

Yayi murmushi ya cigaba da fadin "...Nagode ma Allah da ya bani matar arziki.. addu'a kawai tayi mun and I felt some relief"

"and what happened next??" ta tambaye shi tana kallon shi in a mischievous way

in a confused tone yace "ban gane what happened ba.."

Zaheera ta fashe da dariya tace "what is that doing on your bed??" ta nuna bra din Ameera da ta hango a kan gadon.

Da sauri ya juya ya dago bra din tare da fashewa da dariya yace "Ya salaam, Sweetheart yaushe kika lalace haka?? see nothing hap..."

"hmmm.. na gane, Allah ya kawo 'yan uku"

"Ameen sweetheart.." ya fada yana dariya.

"ni kam dama na kira ne in ji lafiyarka.. let me go attend to Baby eeesh, gata can ina jin ta tana nema na"

"thanks sweetheart.. my regards to the kids"

A daidai nan ne Ameera ta shigo dakin.. Zayd wanda hankalin shi yake kan wayar bai kula da ita a tsaye ba

"insha Allah Sweetheart.. I love you so much"

"I love you too.. very much"

"Ba wani nan, So na ya ragu a zuciyarka tunda kayi mun kishiya.."

fashewa yayi da dariya yace "soyayyar ki daban ce Sweetheart.. You are.."

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un.." ya jiyo muryar Ameera wadda take a tsaye hawaye na bin fuskarta.

A rude ya tashi tsaye yace "Habibty.."

Tuni Ameera ta juya ta ruga a guje zata bar dakin yayinda ya bi bayan ta a guje ya riqo hannunta ya hada ta da bango..

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now