Zynat

33 8 8
                                    

Dedicated to Aysherhayat aratuibrahim zaynablawal09 and HauwaAbubakar716
Thanks for your love and support Jannah loves you!

*

Talib na zaune a dinning, ba abin da yake yi illa juya abinci. Ummi ta riga da taci abinci ta koma dakinta dan lokacin shan maganinta yayi. Gaba daya ya kosa gobe yayi. Sannin cewa Monday ne kuma Jannah zata fara zuwa school. In sha Allah.

Zynat dake zaune a dan nesa da shine ta kula da rashin cin abincinsa, duk da cewa satar kallonsa take yi. Sai gaba daya taji ba dadi, ganin ya kasa cin komai yasa appetite dinta tafiya. Ita ma sai taji bata son cin abinci.

Ko yayansa Bashar da matarsa Zuwaira da suka zo duba Ummi basu kula da rashin cin abincinsa ba dan suma fama suke da yayansu Amma da Nana.

Kasa jurewa Zynat tayi sai da ta tambaya "Ya Abbati, in dafa maka wani abunne in baka son wannan din?" Sake kallon white rice da shredded beef dake gabanshi yayi sai kuma ya girgiza kai.

Ido ta runtse tana kokarin maida hawayenta. Zuciyarta na mata wani irin ciwo; mussaman ta girka sabo dashi amma ya ki ci."na tabbata da Jannah ce ta tambayeshi ba zai ce a'a ba". Sai kuma tayi saurin kada kai tana maimaita astaghfirullah a ranta sannin cewa bai taba kushe abincinta ba. Hasali ma yana yawan yabon girkinta.

"Toh Ya Abba kaci mana? Ko in dafa maka noodles ne? Ko zaka sha kunu ne, kaga tun breakfast baka ci komai bafa". Yanda tayi maganar cike da tsananin kulawa da damuwa ne yasa Abbati har sai da ya juya ya kalleta.

Itama Anuty Zuwaira matar Ya Bashar maida spoon da take ba Amma abinci tayi tana kallon kanwartan. A ranta kuwa cewa take me yasa Ummita ta damu da shi haka. Ganin bata da amsar tambayarta ne yasa ta girgiza kanta sannanta cigaba da abin gabanta.

Zynat kuwa kasa ko motsi tayi hatta nufashinta sai da ta rike. Yayin da zuciyarta ke dukan uku uku. Ko dai ya gane sonshi take yi? Gaba daya ta gama tsorata da shi har idanunta sai da suka fara ciccikowa. Sai taga yayi murmushinsa me kyau ba tare da ya dauke idanunsa a kanta ba.

"I'm alright Ummita, kawai bana jin yunwa ne kinji Zee?" Kasa dauke idanunta tayi daga fuskarsa. Rabonshi da ya kira ta da Zee har ta manta. Kawar da kanta tayi tana kokarin boye smile dinta tace "Amma Ya Abba ko kadan kaci kaji? Ko kuma bari inje in dama maka kunun Madara in kawo maka nasan zaka sha" tana fadin haka ta mike ba tare da ta saurarehi ba ta tafi.

Ba tafi 20 minutes ba ta dawo dake da karamin flask da kuma mug. A hankali ta ajiye a gabansa. Yanda ta barshi haka ta sameahi a zaune a wajen sai dai ya dan ci kadan a cikin rice din.

Murmushi yayi sanan ya gode mata. Yana bala'in son kunun Madara ba karamin murna yayi ba. "Ke baza ki sha ba?" Talib ya tambayeta bayan ya fara sha. Sai yanzu ya kula ita ma befi spoon biyu taci ba. Kuma ko taba abincin bata sake yi ba illa wasa da yatsun ta da take yi.

Cup ya cika mata sannan ya bata sannin ba kulashi zata yi ba. "Gashi ki shanye yanzunan". Gyara zaman mayafi ta tayi sannan tayi saurin kada kai.  Be bari ta yi magana ba ya katseta.

"Not a word Ummita, bana son musu." A hankali ta g'yada kai had'e da cewa " thanks" sannan ta dauka ta fara sha.

*

Ko da Jannah suka sauko breakfast, Hafsat bata dena sabon halin nata ba. Sulaimi kuwa hara ta watsa musu tana wani yamutsa fuska. Ita ko Jannah ko a jikinta sai ma 0pp0p
Temper ma kadan ta iya ci. Jannah kuwa sai murna take yau favorite person dinta zai dawo tun da Rahma ta sanar da ita.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now