Me Ke Faruwa

31 9 2
                                    

Kuka sosai Jannah take, tana jijjiga Rahma dake kwance. Ganin bata motsi yasa ta fice a guje. Taxi ta nema, da taimakon Ibro me gadi tasa Rahma a mota.

Ko da suka isa asibiti, ihu take tana kiran doctors din. A stretcher aka sa Rahma aka wuce Emergency da ita. Bayan kusan twenty minutes wata nurse ta fito ta fad'a wa Jannah akwai internal bleeding dan haka wani daga cikin family dinsu yayi signing a wuce da ita Operation Theater.

Kuka Jannah ta saka da tayi realizing ba su da kowa. Kuma ko ta Kira su Ummul Khair ba za su iso on time ba. Ga shi kuma Uncle Abdul yana Japan. Zata yi signing kenan nurse din tace " ba ke zaki yi signing ba. Ina iyayenku ko mijinta?" Cikin kuka Jannah tace mata su marayu ne basu da kowa a kusa. Da haka tayi signing.

Ba karamin godiya tayi wa Allah ba ganin schoolbag dinta data zo dashi. Thank God Atm card dinta yana ciki, cikin sauri taje tayi payment din.

Tana ji tana gani aka wuce OT da Rahma. Kuka sosai take tana addu'a. Masallaci ta wuce ganin Maghrib yayi sosai tayi addu'a cikin sujjadarta kafin ta bar masallacin. Tsawon rayuwarta bata taba kewan iyayenta irin yanxu ba. Da yanzu suna nan, da sun dade da kwantar mata da hankali.  Kamar daga sama taji an dafa kafadarta.

"Jennah?!" A razane ta juya da jajayen grey eyes dinta. Duka da niqaab dake fuskarta bai hana Talib ganeta ba. Bakinta na rawa cikin muryar kuka tace "T-Talib".

Hankali tashe ya bude baki zai mata magana sai kuma ya tsaya yayin da idonshi suka firfito sakamakon jinin da ya gani a jikinta.

"What are you doing here at this hour of the day, Jennah? Why am I seeing blood on your clothes? Why are you still in your uniform? Wait where is your sister?" Girgiza kai tayi cikin kuka tana kallon farin riga da blue skirt dinta da jini ya bata. Hatta farin hijab da white niqab dinta da blood stains.

"Say something, Jennah. You're scaring me" kuka ta fashe dashi tace "she's in the Operation Theater, Talib". Baya Talib yayi Yana kallonta. Last three to four hours fa ya rabu da su amma wai har an kawo ta asibiti? Numfashi yaja had'e da zuwa inda Jannah take "Subhanallah! Jennah, you aren't supposed to be here. Muje mu duba ko ana bukatar wani abu!".

Basu fi seven minutes da zuwa ba wata nurse ta fito a guje. Suma guje suka sameta suna tambayarta. Cikin sauri tace musu jini ake so. A hanzarce aka je blood bank da ikon Allah aka samu daya. Kallonsu nurse din sake yi tace leda biyu ake bukata.

Sake cikowa idanun Jannah sukayi sannin cewa Blood group na Rahma ya banbanta dana kowa a gidan saboda, Jannah da Ahmad jininsu B+ ne. Sumayya kuma O+  Rahma kuma Ab- ce.

Ba yanda ba'a yi ba amma an rasa Ab- ganin haka yasa Talib yace a gwada nashi. Juyawa Jannah tayi tana girgiza kai "you don't have to, Talib. I've already troubled you a lot". Smiling yayi reassuringly yace "no Jennah, your sister's life is at stake. Besides what are friends for!"

"Thank you, Talib. Thank you" Jannah ta gode cikin kuka. Da ikon Allah jininsu yai matching. Anan Talib ya bada  leda daya. Awa biyu da tsayuwansu Doctor yafito, da sauri suka tareshi da tambaya. Murmushi doctor yayi yace "Alhamdulillah your sister is out of danger. Sai dai we'll keep her under observation for 24 hours".

Sujjada Jannah tayi, tana ma ubangijinta godiya. Ba karamin dadi Talib yaji ba ganin relief dake fuskar Jannah. Bai taba tunanin akwai ranar da zai ba wani jini ba amma gashi yau yayi. Kuma yasan ko ba komai mahaifiyarshi zata yi alfahari dashi.

Muryar Police na dazu ne ya dawo da Jannah cikin hayyacinta. Ita sai yanzu ma ta tuna da police da suka zo daukan report dinta tun da aka fara operation din. Ganin bata hayyacinta yasa suka kyaleta. Sai kuma yanzu suka dawo.

Ganin Jannah bata da niyyar magana yasa Talib ya basu hakuri, ya kara da cewa ' she's not emotionally stable, su dawo gobe dan tana bukatar hutu'.

Ko da akayi shifting Rahma ICU, ba a bar Jannah ta shiga ba. Zama tayi a wajen dakin kan daya daga cikin kujerun dake wajen.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now