Rashin Gata

40 11 4
                                    


Dedicated to bilkisuali and Aysherhayat  thanks for your votes and comments, Jannah loves you.

"Jennah! Jennah!"

"Open your eyes Jennah!"  Ji tai ana jijjigata kuma ana Kiran sunanta. Firgit ta tashi tana haki, fuskarta a jike da hawaye yayin da jikinta ya jike da zufa. Salati ta fara tana kokarin tashi.

Muryar Talib ne ya dawo da ita hayyacinta. A hankali ta dago jajayen idanunta ta kalleshi. Tuni jikinshi yayi sanyi ganin irin damuwa da tashin hankalin da take ciki. Cikin karamar murya yace

"Are you okay Jennah? You had a dream" girgiza Kai tayi tana share hawayenta kafin ta amsashi. "Talib, I want to see my sister". Ko rufe baki bata yi ba wata nurse ta shige dakin. Mikewa Jannah tayi da nufin shiga dakin amma Talib yayi saurin dakatar da ita.

"Jennah ki jira ta fita tunkunna" saurin girgiza kai tayi  ba tare da ta kalleshi ba tace " I need to see her". Shiru Talib yayi kamar ba zai amsa ba sai kuma taga ya matso inda take hannunshi dauke da sallaya. "You should first pray".

G'yada kai ta karbi sallayar hade da godiya. Ba ta kai minti goma da tafiya ba ta dauwo. Yanda ta barshi a bakin dakin, haka ta sake tarar da shi. Tana karasowa taga nurse na dazu da wani dogon doctor sun sake shiga dakin. Ba'a jima ba taga an shigo da stretcher cikin ICU an sa Rahma akai.

Girgiza kai Jannah ta hau yi tana zub da hawaye. A rikice ta kalli Talib tana jijjiga hannunshi "where are they taking her Talib? Tell them to stop... " Tun lokacin da taga an sa Mahaifiyarta akan stretcher taji ta tsani abin gaba daya. Tuni  numafashin ta ya fara yankewa.

Cikin sauri Talib ya zaunar da ita a daya daga cikin kujerun wajen. "Relax Jennah za ayi shifting dinta zuwa private room ne" Kallonshi tayi da rinannun idanunta tana son tabbatar da gaskiyar maganarshi.

"I promise". Nodding tayi ta sake mikewa tana me gode wa Allah. At least hankalinta ya kwanta daji za'a kai ta private room ne. A room 17 aka aje ta.

Fitansu doctors din kenan Jannah ta shiga dakin. A hankali ta zauna tana kare wa Rahma kallo. Addu'o'i sosai ta mata, tana me zub da hawaye. Har yanzu ta tabon da Ashir ya bar mata a fuska. Har yayi wani purple purple. Bakinta a bushe shima ya zama wani blue haka, ga shi tayi haske.

Bakin gashinta a zube akan pillownta. Tana bacci cikin kwanciyar hankali. Sumbatar ta tayi a goshinta sannan ta juya ta fice dan five minutes kadai aka bata. Fitowarta kenan ta ta ga Talib tsaye a bakin kofar.

"How's she doing?" Karamin murmushi Jennah tayi wanda yasa Talib rike numfashinsa na tsawon lokaci. A zuciyarshi kuwa cewa yake "Subhanallah! Fa tabarakallahu ahsanul khaliqiin"

Duk da cewa iya idonta kadai yake gani, sai kuma kadan daga cikin girarta da karar hancinta, yasan cewa ba karamin kyau Allah ya azurta ta da shi ba.
"Alhamdulillah, I think she's doing better".

Shi ma murmushi me kayau yayi sannan ya kawar da idanunsa duk da yanda yake so ya cigaba da kallonta yasan haramun ne tunda ita ba muharramarsa bace.

"Ma Sha Allah, that's good to hear. Why don't you eat something, kafin doctors din su dawo" sai a lokacin ta kula da disposable cup na coffee da chips dake hannunshi. Har zata ce a'a sai kuma cikinta yayi fara kuka.

Murmushi Talib yayi sannan ya mika mata abin dake hannunshi. "Sorry, this is all I could get". Murmushi Jannah tayi tana kada kai. "A'a Talib, this is more than enough. Thank you".

Bayan ta wanke hannu ta zauna zata fara ci, sai ta tuna dole sai ta daga niqab dinta. Ga kuma Talib yana nan. Kallonta Talib yayi, sai yayi saurin dauka wayarshi. "Excuse me Jannah". Yasan babu yanda zata ci abu a gabanshi. Jiya ma sai da yabar wajen kafin tasha coffee.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now