Rabon Gado

97 12 3
                                    

Dedicated to JamilaSalihu

Hannu Uncle Abdul yasa ya rike kanshi. Umma ce daga gefe ta rike carbi tana kuka tare da Ummul Khair dake zaune a gefenta. Ga ba daya sun rasa me ke musu dadi. Ace Ahmad ya rasu matar shi ma ta rasu kuma duka a lokaci daya.

Babu abin da ya sake kashe musu jiki kamar wayar da suka yini sunayi safiyar jiya. Lafiyanshi kalau yana dariya kamar Yana gabansu. Numfashi Uncle Abdul yaja yana me tausaya wa kansa da su Jannah.

Sai a anan ne ma ya tuna alkawarin da ya daukar wa Sumayya.

"Promise me Abdul ko da wani abu ya sameni zaka kula da su Rahma kuma zaka nema min Akhi. Promise me Abdul. Arjuk, (please) don't say no" Sumayya ta fada tana kuka.

"I promise I'll try my best." Uncle Abdul ya fada jiki a sanyaye.

Numfashi yaja yana share hawaye. Da ma tasan zata mutu ne ta tambayeshi hakan? Basu Kai sati da yin maganar nan ba amma gashi bata nan.Allah yayi mata rasuwa.

Yau ya kama sati da rasuwan Sumayyah da Ahmad. Rayuwa ya cigaba sai dai komai ya chanza. Umma ta fita a hayyacinta gaba daya. Da zaran taga Abdul ko Abbul Khair sai ta fara kiran sunan Ahmad. Bata aikin komai sai kuka.

Haka ma Rahma kulle kanta take a daki tana kuka kamar ba gobe. Baci ba sha sai an tilasta mata. Hakan ma idan taci sai ta amar. Tayi wani mugun fari ta bushe har ta fita a kamanninta. Idan ba farin sani ka mata ba bara ka taba ganeta ba.

Kwana biyu kenan aka sallami Jannah a asibiti. Bata kuka bata magana sai dai tayi shiru tana kallon bango. Kullum tana cikin drip saboda rashin cin abinci. Uncle Abdul yana kaisu wurin therapist amma duk a banza.

Sannu sannu abu baya dadi sai Kara tabarbarewa yake. Hafsa kuwa tun bayan sadakan uku ta koma kula da Rahma duk da cewa ba wani kusanci ne tsakaninsu.

Ummul Khair dake kitchen tana kokarin hada wa su Rahma custard, tayi tunanin yiwa Abbul Khair magana  akan su Jannah dan tun da aka sanar dasu akan rasuwar mahaifinsu jikinsu ya sake tsananta.

Kuma a iya saninta Hafsa ba son yaran take ba why not su dauke su su hadasu dasu Mufida da Zarah tunda sunfi kusa. A ganinta zasu do sakewa a can  fiye da nan. Kodan rashin su Ashir da Abbas

A dakin Rahma ta sami Uncle  Abdul yana rike da hannun Rahma dake kuka. Jannah kuwa tana wanka dan tarewa tayi a dakin Rahma.

"Subhanallah! Abdul what is it? Lafiya Rahma?" A rikice Ummul Khair ta zauna a gefensu tana tambaya. Kuka Rahma ta sa tana cewa "Don't leave Uncle. Please!!" Sake rikicewa Unmul tayi ta maida idanunta kan Abdul.

"Ina zakaje kuma Abdul? Wai me ke faruwa ne".

Kallonta yayi yace

"Ummu Toronto zanje kinsan gidan Ya Ahmad yana hannun Mai gadinsa. Kuma tun last week Secretary dinsa me kirana yace akwai matsala a accounting department na 'J stones' da 'Rahma Textiles' kudade dayawa suna missing. Ga kuma batun sabon project da ya fara na  'Sumayyah Foundation'.

Ummul akwai wanda yake saida projects dinsu. Shi yasa tun farko nace a dakatar da aiki a companies din amma Ya Umar yaki ji. Ummu har kokarin sa wasu daga cikin filayensa ake a kasuwa fa. I have to do something. Dole a ba yaran Nan hakkinsu"

Shiru Ummul Khair tayi sakamakon idonta da ya cika da hawaye. A ce sati uku kacal da rasuwan mutum amma har ana kokarin salwantar da dukiyarsa? Wannan rayuwa da me tayi kama.

"You're right Abdul please do the right thing kar ka damu da Ya Umar I'll talk to Abul Khair nasan he'll make him understand".

"No Ummul"  kukan da Rahma tasa yasa Jannah tsayuwa abakin kofar bathroom din.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now