Tashin Hankali

45 12 5
                                    

Dedicated to MaryamMuhammad074

Yau sati kenan da dawowan Uncle Abdul daga tafiya, Babu laifi sun shirya da Rahama. Sai dai shi kanshi wannan sabon halin Hafsat dinne ya tsaya mishi a rai. Ace mutum baya sonka da safe sai kuma yace yana son ka da yamma ai hakan ba me yuwuwa bane.

Hakan ne yasa ya sake sawa Hafsat ido sosai, ita kuwa Hafsat abin ba karamin bata mata rai yake ba. Barin ma yanda yake lalata su Jannah. Kusan kullum sai ya fita da su idan ya dawo daga office. Hakan ne yasa Aunty Hafsat kawo shawaran sa su a islamiyyah.

Basu ki ba duk da cewa sunyi saukan alqur'ani. Yau ma kamar kullum Aunty Hafsat na zaune a palor, ta sa Aisha yi mata tausa, hannunta daya kuma na rike da plate na apricot. Sallamar makociyarsu kuma babbar kawarta, Hajiya Saude ne yasa ta fadada murmushinta.

Guda ta rangada hade da cewa "Iyyeh! Su Hafsa ikon Allah, mulki kike hankali kwance" murmushi sosai Hafsat tayi kafin ta amsa ta "to me za'a fasa Hajiya Saude". Dariya Saude tayi ba tare da ta amsa gaisuwar Aisha ba ta zauna a gefen Hafsat.

"Sai na fada miki ki kawo mata ruwane?" Cike da fada Hafsat ta harari Aisha. Cikin hanzari Aisha ta mike ta nufi kitchen. "Ki hado da abinci" Saude ta sake fada. G'yada kai Aisha tayi sannan ta fice.

Hira sosai suke kamar ba gobe. Nan Rahma da Jannah suka yi mata sallama zasu wuce islamiyyah. Kallon hadarin kaji tayi musu sannan ta shumfuda murmushin tsiya a fuskarta. Ita kuwa Hajiya Saude sai tabe baki da tayi.

Suna fita Hajiya Saude ta juya ta fuskanci Aunty Hafsat. "Wai ni Hafsa har islamiyyah ma kika sa su?" Tabe baki Aunty Hafsat tayi "toh ya zan yi Saude, wannan Abdul dinne wallahi gaba daya yake taka min biriki. Ni wallahi inta ni ne ma ko boko baza suyi ba. Amma mayen kullum yana tare dasu".

G'yada kai Hajiya Saude tayi, fuskarta dauke da murmushin tsiya. "Toh ai wannan me sauki ne, yanzu sai ayi mishi aiki ai yaji ya tsani gida kamar mutuwar sa. Amma ke din ne sai usatazancin tsiya".

Shiru Aunty Hafsat tayi na dan lokaci, kafin ta cigaba da magana. "Kin gani ko, Saude, ni fa shirka nake tsoron yi."

"Ai wurin malami zamu ba boka ba kuma ba ma sai ki nemi gafarar Allah ba" cike da wauta da farin ciki Hafsat ta g'yada kai. "Allah ko Saude shi yasa nake son ki wallahi. Kin ga gobe da safe in Allah ya kaimu sai muje kawai"

(Subhanallah! Allah ya tsare mu da shirka! Dan Allah mu rike azkar na safe da yamma)

*

Ko da suka isa gida Talib be kula Zynat ba, illa gaishe da Ummi da yayi. Wanka yayi sannan yayi sallah, kafin ya kunna TVn dake dakinsa. Har kusan Maghrib be fito daga dakin ba alhalin daga bayan la'asar zuwa Maghrib tare da Ummi yake zama, ko wani ranan Allah.

Ita kuwa Zynat gaba daya ta rasa me yake mata dadi, kome ya jagule mata. Ji take kamar ta tsala ihu ko zata samu sukuni. Ganin Talib be ci abinci ba yasa Ummi tambaya cike da kulawa.

Ko da taje ta duba shi ce mata yayi baya jin yunwa. Sai da ko kulashi bata yi ba illa sanar dashi da tayi, Ummita zata kawo masa lunch. Cikin fifteen minutes Ummita tayi warming abincin ta hada a kan tray sai dai har yanzu a tsorace take.

Har wani zazzabi take ji. Cike da natsuwa da tashin hankali taje dakinsa, jikinta sai bari yake. Ta kai five minutes a bakin kofan ba tare da ta bude ba. Sallati tayi hade da Bismillah kafin tayi knocking kofan. Jin ya amsa da "wa alaikum Salam" ne ya sake tsinka mata zuciya.

Sanin ce wa ya hanata yin knocking ba tare da tayi sallama ba. Kofan ta tura a hankali sannan tayi sallama. Kasa kasa ya amsa sallaman ba tare da ya kalleta ba. Nan ma ta jima a tsaye kafin tayi kokarin ajiye tray din.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now