Mugu Bai Da Kama

26 9 2
                                    

Bismillahir rahmanir rahiim.

Please idan ba kuyi sallah ba kuje kuyi, the story can wait. But Salah doesn't wait for you.

Dedicated to zaynablawal09 & amienerh Rahma loves you!

Kwana Sulaimi tayi tana me takaicin faruwan al'amarin nan. Allah kadai ya san irin tsanar da take yi wa Rahma. Ko kad'an bata son ta, ko inuwa daya bata son ya had'a su. Toh kuma sai ta zuba ido ta kyale yar rik'o ta aure mata 'dan uwa?

"Ai wallahi basu isa ba!". Tsaki ta ja ta mike zaune ta fara sake sake a cikin zuciyar ta. Haka ta kwana ido biyu, har ta samu ta tsara makircin da zata yi wa Rahma. Dan tasan matukar Ashir ya kafe akan abu toh babu mai chanza masa ra'ayi.

Hakan yasa bata yi mamakin kyautatawar da yake yi wa su Rahma bayan dukan da yayi mata kwanakin baya wanda yayi sanadin rike ta a asibiti. Sanin cewa tun asali mahaifiyar su ce ta gina musu tsanar marigayiya Sumayya da 'ya'yanta. Amma duk da haka ma, Ashir na taka wa Hafsa briki. Sosai yake hanata yin wasu abubuwan.

Garin Allah na wayewa ko sallah bata yi ba ta dauki waya ta kira Muhsin. Yana dauka ta fashe da matsanaicin kuka har da shesshek'a. Sosai hankalin Muhsin ya tashi jin yadda take kukan babu kakkautawa.

"Subhanallah! Habibtie! Sulaimi! Please ki daina kuka, tell me, me ke damun ki?". Cikin kukan ta ce " Muhsin Rahma ce! ". Shiru yayi na seconds kad'an sannan yace " Rahma? 'Yar Uncle Al'amin me rasuwa? ". Nan ma " eh" tace dashi.

Cike da rashin fahimta yace " toh me tayi miki? Ki fad'a min, ni kuma nayi miki alkawarin rama miki har sai in da karfin na ya kare". Murmushi sosai Sulaimi tayi had'e da goge fuskarta, dama ta san Muhsin na matukar kaunar ta kuma duk abin da take so zai yi mata cikin kiftawar ido.

Cikin rawar murya ta fara magana. "Habibi Rahma ta asirce min 'dan uwa. Ko kad'an baya hankalin shi wai ita yake son aura ita kuwa wasa da hankali take mishi, gashi kuma Mama tace sai Ya Ashir yayi aure kafin in yi aure..."

Ba tare da ta kammala zancen ta ba nan Ashir yayi saurin katse ta " dakata, Sulaimi habibtie. Kina nufin sai Ya Ashir yayi aure kafin a amince min in aure ki? Kuma a tak'aice dai yanzu ko zancen auren shi ba'a fara ba?".

Cikin jin dadin nasarar da take yi a kan Muhsin nan ta fara shirga mishi k'arya ta fara labarata mishi karya da gaskiya akan yanda abubuwa suka wakana tsakanin ta da mahaifiyar ta har ma da cewa " habibi, har zuga Mama tayi wai kar ta amince min da auran ka saboda kai Bahaushe ne.." sosai Muhsin ya tunzura da jin zancen nan.

Lallai 'dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido. Malam Bahaushe yayi gaskiya da yace 'mugu bai da kama'. Muhsin bai taba kawowa a ranshi Rahma zata yi haka ba, sosai yake mata ganin kamila wacce tasan me take yi, duk da cewa sau biyu kacal ya taba ganin ta. Ashe dai munafuka yake wa ganin mu'mina.

"Dani take yi, Sulaimi habibtie, ki gaya min how should I deal with her? Ina so in koya mata lesson da zai sa baza ta sake aikata munafurci a rayuwar ta na duniya ba!". Farin ciki sosai Sulaimi tayi da jin zancen shi. Ga dukkan alamu tayi nasara akan shi.

Cikin murya me rauni tace " Habibi have her raped. Kasa ayi raping d'inta". Hafsa baza ta taba yarje wa Ashir ya auri macen da bata da martaba ba. Kuma hakan zai sa dole Ashir ya hakura dan iyayensa baza su amince ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 11, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now