'Da na kowa ne

188 17 2
                                    

"Hurry up Jannah it's time for Salah" Rahma ta kwalla mata kira. Daga kan prayer mat da take, ita ta ma manta Jannah bata sallah ba.

"Coming big sis". Jannah ta fito tana fixing hijabinta da ta kasa natsuwa ta daura. Zuwa tayi ta gefen Rahama ta rad'a maya a kunne "sis I'm not praying remember?"

"Assalamu alaikum wa rahmatullah, assalamu alaikum wa rahmatullah."

"Allahumma inni as'aluka imanan sadiqa, wa ilman nafia, wa rizqan wasi'a, wa lisanan zaakira, wa qalban khaashi'a, wa badnan saabira, wa tawbatan qablal maut, wa nasiban maghfiratan ba'dal maut, wa nasiban minal Jannah, wa najatin minan naar bi rahmatika ya arhamar raahimin"

"Amin"

"Allahumma Ja'alil Qur'anal adhima rabi'a qulubina, wa nura sudurina, wa jala'a ahzanina, wa zahaaba humumina,wa ghumumina, wa saa'iqna, wa dalilana, ilaika wa ila Jannatika jannatil na'eem, wa daarika daaris salami ma'al ladhina an amta alaihim minal nabiyyina, wa siddiqina, wasshuhadaa'i was saliheen."

"Amin".

Bayan sun idar suka wuce dining dan cin abinci. As usual Jannah ta zauna gefen Baba sai faman jera mishi tomatoes dake cikin plate dinta take acikin nashi dan bata son tomatoe a kan abinci.

Idan kuma taga Sumayya bata kallo sai ta kwashe naman cikin plate na Ahmad, wanda in banda murmushi babau abin da zai yi. Dan ta san Rahama ba kyaleta zata yi ba, in tace zata mata.

"Mommy i don't want lasagna i asked for toast." Jannah ta fada tana buga kafa tana hararan lasagna dake kan plate dinta, harara ta Sumayyah tayi hakan yasa ta tsuke bakinta tayi shiru.

"Jannah yanzu toast zai riqeki har gobe?" Rahma ta tambayeta cike da kulawa sanin cewa idan tana al'ada Sumyya bata cika bata light abinci ba dan musamman take sake dafa mata wasu abubuwan

"Come on big sis why are you all treating me like a five year old?  Haba mana big sis stop acting like a hundred year old grandma" tayi tsaki fuska a hade sam bata son yanda suke kula da cin abincinta tun da ta fara al'ada gani take kamar tana daga musu hankali. Ita da ba dan gudun magana ba ai scrambled egg dinta ma ai ya isheta.

"Toh ae condition dinki zaki duba Jannah. Didn't you heard what Doctor Rachael said? You need healthy diets" Rahma ta tunatar da ita abin da bata son ji. Sai wani sabta a gaba suke yi kamar wanda akanta aka fara al'ada.

"Pft will you let it slide? Ni am already tired of these never ending lectures. Dad please help" tayi narai narai da ido tana me kallonshi, tasan shi kadai zai ita biye mata in ko ba haka ba toh zata kare tana cin vegetables for dinner

"Jannah it's the bitter reality amma ku bata abin da take so" Baba ya maida hankalinshi kan abincin da yake ci wanda duk tomatoes na Jannah ne ya cika.

"If only za'a hada miki da something else" Sumayya ta fada babu alamar dariya a fuskarta lolacin da take maida wa Baba kebabs da Jannah ta zare daga plates dinshi.

"Mommy a hada min da tuna sandwich and a big tube of bubblegum ice cream" ta fada tana clapping hannunta. Cike da jin dadi dan ta san baza a hanata shan ice cream ba tunda taki cin abinci

"The typical foodie" Rahma ta fada tana dariya.

"That's what made me stood out" Jannah tayi flipping gashinta dake zube a bayanta, kamar yanda take gani ake yi a film.

"Just like a sore thumb ba?" Rahma tayi ruffling gashinta da ta dade tana gyarawa tsawon awa daya da rabi, dan Jannah akwai son ado.

Mommmyyy!!!..." Jannah ta hada fuska idonta ya cicciko tasan ko ba'a fada ba gashinta is now a complete mess.

"Jannah, don't count me in" Sumayyah ta daga hannayenta. Sannin cewa abin bana kare bane, kuma ita ba ta da kuzarin biye musu.

"Me too" Baba ma ya ja gefe. Hade da ture plate din daga gabanshi. Hararan da Sumayya ta mishi ya sa shi koma cin abincin shin dan yasan yanzu zata fara fushi tana cewa baya son girkinta tane.

"Me t..." Rahma bata karasa ba taji saukan ketchup akan sabon farin T-shirt dinta. Tayi expecting haka amma ba akan farin rigarta ba.

Sumayyah cw ta harari Jannah ganin Rahma ta bata fuska. Ajiye mayonnaise dake hannunta tayi ta tsaya ganin mess da tayi a jikin rigar Rahma sai kuma taji ba dadi dan da ace itace Rahma baza ta mata haka ba

Ahmad ne ya fara dariya kasa-kasa. Hakan yasa Rahma ta fara dariya kafin ta tashi a kunyace ta bar wajen.

"Big sis?" Jannah ta shiga dakin dauke da plate na Poutine da Saskatoon Berry Pie. Rahma ta shareta duk da cewa tana mutuwan son Poutine. "You are mad at me?" Rahma tayi saurin juyawa jin yanda muryar Jannah ke rawa. Ai ko tana juyawa taga Jannah na hawaye.

"Ya ilahi Jannah please don't cry baby sis i wasn't mad ban ji ki bane. Shush kinji?" Ta share mata hawaye hade da sumabatar goshinta "Eh gashi na san you must be dying to eat Poutine tunda kinfi sati baki ci ba"

Karba tayi tana murmushi "Sure baby girl. Can't wait to eat" "Kai big sis you're so dramatic." Jannah tayi dariya sannan ta zauna kan side drawer

"Why wouldn't i be? After all I'm your only sister" Rahma ta fada cikin wani flattery tone tana rolling eyes dinta "Sure that reminds me. Momma tana son ganinki kafin ki kwanta."

"OK"

"Assalamu alaikum Aunty." Rahma tayi sallama sannan ta karasa cikin mak'ek'en dakin Sumayyah. Wand aka kawata shi dai dai misali.

"Wa alaikum Salam Rahma shigo kinji?" Sumayya ta murmusa tana kokarin mayar da wani box cikin wardrobe dinta. Da mamaki Rahama ta bita da kallo tana tunanin dalilin da yasa bata so a taba wannan box din

"Rahma kiyi hakuri idan Jannah ta bata rai dazu nasan bara ki nuna ba" "Kai Aunty, it's nothing. Please don't make me feel like the bad girl, here." Rahma ta kada kai ta murmushi ai inda sabo sun saba da hakan

"So nake in gaya miki. Dan kanin mahaifinki ya janye magana auren" Sumayyah ta sanar da ita lokacin da ta zauna gefenta akan gadon, da sauri Rahama ta dubeta.

"Dagaske Aunty?" Rahma ta sake tambaya dan ta tabbatar ba wasa kunnuwanta suke mata ba.

"In sha Allah" Sumayyah tayi murmushi.

"I don't know what I'd do without you. You are a mother figure to me and I love you. Thank you for adopting me Aunty nagode sosai" Rahma ta rungumeta tana kuka. Wani hai take ji da taji an janye maganar aurenta da Muktar.

"Haba Rahma ai 'da na kowane" Sumayya tayi huggin dinta back tana me sa mata albarka.

Vote*comment

Bookaholicnutella

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now