Rahma

239 20 0
                                    

"Mommy jinin yaki tsayawa kuma diaper da kika bani yana hanani zama mai kyau. Ni dai nasan am sick please take me to the doctor kar jinina ya kare"

Jannah tasa mahaifiyarta a gaba tana kuka ita wai a dole a tsayar da jinin. Dafe kai Sumayya tayi dan ta ma rasa me zata ce. Tun dazu fa take mata bayani amma duk yabi iska.

"Relax baby it's gonna stop in few days. Har yanxu cramps din na damunki? Ko kuma drugs da ta baki yayi subsiding pain din?' Ta shafa kanta tana me kokarin kwantar mata da hankali duk da cewa nata a tashe yake. Ita dama zata iya dauke mata bleeding din da ta jima dayi.

"Ni dai mommy ban sani ba I just wanna stop bleeding" ta kara feshewa da kuka. Tana me buga kafafu a kasa yayin da dogon gashinta ke faman rufe mata ido.

"Subhanallah Jannah lafiya? What's wrong?" Ahmad da yanzu ya shigo ya tambaya hankali tashe dan har wani seizing numfashinta ke yi, ganin Sumayya tayi takumi ya sake daga mishi hankali.

"Daddy I'm bleeding" ta karasa da Sabon kuka yayin da ya karaso inda take.

"Bleeding fa kikace?" Al'amin ya sake tambaya ganin babu alamar jini tattare da ita. Mikar da ita yayi yana kare mata kallo sosai. A iya sanin shi Jannah yarinya ce da bata da saurin kuka hakan ya sake tabbatar mishi akwai abun dake damunta.

"Eh tun dazu jini take fita from my nether region kuma mommy taki kaini asbiti tunda doctor Rachael ta tafi" Jannah ta fada tana kallon Sumayya da kanta ya fara ciwo. Shiru Sumayya tayi dan ta ma rasa na cewa. Abin har mamaki ya soma bata a ce budurwa kamar Jannah bata san me al'ada ba.

"Sumayya dagaske ne?" Ya maida kallonshi zuwa ga matarshi da ta zabga uban takumi tana jiran wani miracle dan ta ma rasa yanda zata fahimtar da ita. Tabass akwai aiki ja a gabanta indai haka Jannah take. Amma sai dai batayi nadaman hakan ba dan hamdala take yi da Allah ya tsare mata 'ya daga rashin ji.

"Daddy you don't trust me ko? Fine I should have known" tayi snatching hannunta daga nashi tafice da gudu zuwa balcony. Tana ji yana kiranta amma ko juyawa taki yi wai ita a dole tana fushi.

"What's up with her sudden mood swings?" Baba ya tambaya hankali tashe ko zama ya kasa ganin yarshi cikin wani yanayi. Numfashi Sumayya taja kafin tace

"She's on her period" ta ambata tana me kallon yatsunta. Kunyan fada mishi take amma sai taga kamar dole ya sani tunda mahaifinta ne kuma sunfi kusanci da shi.

"I see...wait...what?" Ahmad ya zare ido cike da mamaki yaushe ne aka haifi Jannah. Ji yake kamar jiya aka yayeta amma gashi ita harta girma.

"You heard me right your baby girl has finally grown up". Sumayyah ta murmusa. Tana me kallon shi cike da mamaki. Gani tayi ya ja jiki ya zauna kusa da ita hade da riko hannunta kamar wani yaro karami

"Ikon Allah me zance? Ma sha Allah Alhamdulillah. Was that why she was crying?" Ya sake tambaya cike da tausaya mata.

"Eh" mama ta fada tana murmushi.

"My naive little girl is so sensitive ".

2 hours later

"Haahh! Mama yanzu kina nufin nima za'a fara rubuta min zunubi? I though sai na kai eighteen fa" Jannah ta fada a tsorace hannu ta daura kan bakinta tana sake mamakin abin da taji. Kasa yarda tayi da Sumayya tace ta kai a fara rubuta duk wani zunubi da ta aikata.

"Wa yace miki eighteen?" Sumayya ta zaro ido tana kare mata kallo, anya lafiyarta kuwa? Toh ina takai ilimin addininta?

"Momma mana. Ko a ina ai sai mutum ya kai eighteen ake punishing dinsa. Ai ko a nan Canada ma hakane, kuma kin ga mu muna Toronto." Jannah ta nanata abin da malamarsu na school ta fada musu.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now