Ramadan

175 15 3
                                    

Sumayya da ta kasa bacci tsananin tashin hankali ta mike daga kan gado. Cikin sauri ta yi wanka had'e da shiryawa cikin doguwar riga. Taje kanta tayi kafin ta nufi kan gado domin tasin Ahmad. "Al'ameen wake up" ta fa'da yayin da take ta'ba shi. Murmushi ya sakar mata had'e da mikewa. "Good morning beautiful wife" "Morning husband ka tashi kar mu makara kaji?" Shiru yayi kafin ya mike. Ko k'ad'an baya son tafiyar nan.

Jiki a sanyaye Sumayya ta mike zuwa d'akin Rahma. "Daughter tashi ki ki shirya" Juyawa Rahma tayi had'e da buga kafada. "Umm umm" "C'mon Mercy tashi kinji?" "Aunty ba school fa please let me sleep" "Kin manta yau zamuje Nigeria?" Ai kua da sauri ta mike. "Hasbunallah Allah na manta". Cikin sauri ta nufi bathroom gudun sa su letti.

"Angel!" Sumayya ta kira Jannah. "Umm umm Mommy please" ta sake cusa kanta cikin pillow. "Ke umm umm Rahma umm umm ya zanyi da kune?" Shiru Jannah tayi kamar bata ji ta ba. "Wake up Baby kin ji?" "Mommy five minutes" da k'yar Sumayya ta samu ta lallaba Jannah ta tashi.

Ai kua tana ji Nigeria za su je ta saje komawa kan gado. "Jannah me haka? weren't you the one insisting?" "Not anymore Mother dearest I'm out because i can't stand Granny". "K'aryanki kuma ai'' da haka ta d' aga ta cak." Mommy put me down!!! "" You wish baby" har sai data sa ta a k'arkashin shower kafin ta fito tana cewa. "Fifteen minutes Jannah".

Kitchen ta wuce a nan ta sami Rahma dauke da bowl na Poutine da plate na Jacket Potato. Ita har yanxu mamaki suke bata. Ta rasa me suke so a cikin Poutine ko Jacket Potato gani tayi duka ai dankali ne.

"Sannu daughter" Murmushi Rahma tayi kafin ta tayata k'arasa BeaverTails da lobster rolls data fara. Cikin two hours suka gama girka komai hade da jerawa bisa dining. Kamar ance suje parlour ai kua samun Jannah suka yi tana faman fad'a da Umma.

"Wai Granny me hakane? Idan haka zamu cigaba da zama Allah I'm not coming ai I'm not obliged to" "Toh sannu Firdausi ko me ma uwar taki taje kiranki dole sai kinzo ko kina so ko ba kya so" "Toh amma ai I'm not obliged to cook any kuka thing. Wait mema kikace Miyir kuk..ku.." "Dalla matsa miyar Kuka ake cewa" "Subhanallah you mean kuka na crying ko? Please dont tell me da hawaye ake yi. Yuck! K'azanta sai 'yan Nigeria."

"Ke dan abu kaza kazanki har kin isa ki zagi Nigeria? Abincin mu befi jagwalgwalonku na iraq da na turawanku ba?" "Allah befi ba" Jannah ta b' ata rai. "In kinga dama ki fashe amma nidai yau bazanci kayan aman naku ba. Wa yasan ma ko alade kuke dafawa mutane". Dariya Jannah ta tayi har da rike ciki.

"Granny what is Aledede?" Harara Umma ta watsa mata "Wawiya Alade ake cewa not Aladede" "Whatever ni dai tell me. Please.." "Mtcheewww Alade shine pig kuma naman shi ba shine pork da kuke ci ba?" "Ohhh that dirty thing? Amma ai yafi 'yan Nigeria tidiness saboda baya cin hawaye" Jannah ta fad'a fuska dauke da murmushi. "' Ya dai fi Uwarki wawiya kawai" da gudu Jannah ta mike ganin Umma na kokarin Jefa mata pillow.

"Ni dai I'm not wayiya" "Jaka wawiya ake cewa not wayiya" "Whatever I'm not a bag I'm a human... Ouchh!!" sai kuma ta saki ihu sakamakon karo da sukayi da uncle Abdul. "Jannatul Firdaus..!" "Sorry Uncle" "it's okay"

Daidai lokacin Ummul Khair ta shigo tare da 'ya' yanta Zara me shekaru fourteen da Mufida me shekaru seventeen kasancewar manya biyun Hamza da Usman sunyi aure. Zarace ta fara k'arasawa wajen Jannah. "Hey Jannah you look good" ta fada tana k'arewa abayan da tasa kallo "You too sister" nan suka gaisa da mul Khair da Mufida.

"I heard some commotion downstairs d'azu da nake shiryawa" Ummul Khair ta fad'a tana kallon Jannah. Hararan Umma Jannah tayi ganin bata kallon ta. "Ni kike harara?" suka jiyo muryar Umma.

"Mtcheewww" Jannah tayi tsaki k'asak'asa. "I didn't hararara you old woman". "Kin ga irin rashin kunyar da uwarta ta d'orata a kai ba?" Umma take fad'a wa Ummul Khair bayan sun gaisa.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now