Takaici

13 7 0
                                    

Dedicated to eeman365

"He's not back big sis!" A shagwabe Jannah ta juyo tana kallon Rahma da ke kokarin futowa daga toilet. Numfashi Rahma ta sauke had'e da girgiza kai, fuskarta dauke da murmushi.

Bata amsa ta ba har sai data saukar da curtains din da yake a dage. Sai da ta tabbata window ya kullu sannan ta zame towel dake kanta. "Stop being a ninny baby! He must be busy at work".

Kallon Rahma dake faman taje kanta tayi, dayan hannunta dauke da hand dryer. A sanyaye ta mike ta sa hannu ta karbi dryer daga hannunta. " As you wish big sis, I'll let him be. Let me help you out, else you'll catch a cold".

Murmushi me kyau Rahma tayi ganin yanda Jannah ta maida hankali kan drying gashinta. Godewa Allah ta sake yi da Ya azurta ta da kanwa irin Jannah.

"It's done, your highness" Jannah ta fada cike da tsokana, fuskarta dauke da murmushi me kyau wanda ya sake bayyana dimples dinta. "Thank you peasant!". Cike da dariya Rahma ta amsa.

Komawa kan gadon Jannah tayi dan picking wayarya dake ringing. "Assalamu alaikum, Ummul Khieyr" dariya sosai Ummul Khair tayi jin yadda Jannah ke ambatar sunanta.

" Wa alaikum salam, Jennatul Khieyr" Ita ma murmushi sosai tayi idonta taf da hawaye dan ya da ta kira suananta sai da ya tuna mata da iyayenta.

" I miss you a lot, Ummi. When will you come over?" Yanda tayi maganan ne ya kashewa Ummul Khair jiki. Numfashi taja dan mayar da hawaye sannan ta maida kallonta kan Abbul Khair da ba lafiya. Kwance yake da cannula a hannunsa. Gaba daya ya rame. Currently suna asibiti, ciwon kidney ke damunsa.

" Soon, Jannah. Kunji baby?" G'yada kai Jannah tayi had'e da cewa toh. Daga nan ta tambayi su  Zarah da Mufidah. Sannan ta ba Rahama wayar. Nasiha sosai Ummul Khair ta musu, sann6a ta tambayesu matsalolinsu wanda suka amsata da babu.

Uncle Abdul ba dawo gida ba sai kusan sha biyun dare, shi ma da kyar ya iya shiga gidan. Shi kanshi mamakin irin wannan al'amari yake. Ba tare da yayi tunanin komai ba yayi wanka ya bi lafiyar gado.

Kwanciyar shi kenan ya tashi firgit sakamakon mafarkin da yayi. Ganin Sumayya yayi cikin mafarkin shi tana kuka tana cewa "na baka amanar 'ya'yana Andul, kaji tsoron Allah ka kula min da marayu".

A hankali ya mike kafanshi a sanyaye ya nufi bayi. Alwala ya dauro, sannan ya sallaci nafilfili, daga nan kuma ya hau karatu Alqur'ani me girma. Ko daya kammala karatun shi, hannu ya daga yana rokan Ubangiji da ya bashi ikon sauke hakkin marayun dake kanshi.

Sai a lokacin ya tuna sakaci da azkar na safe da yamma da yake yi. Nan ya karanto su, sannan ya mike a hankali ya nufi hanyar dakin su Jannah da nufi duba lafiyar su sai dai yana tsoron shiga kansu alhalin suna bacci.

Cikin rahamar Allah ya sami Aisha a kitchen tana waya tana jera plates. “haka dai kace barrister, amma ni dai bazan yi musu da kai ba dan ba'a musu da lawyers––” jin gyaran muryar Uncle Abdul ne yasa yayi saurin katse wayar. Da ganin kasan da saurayi take wayar.

Cikin ladabi ta runsuna ta gaishe shi, nan ya bukace ta da ta shiga dakin su Jannah ta duba ko suna lafiya. Yana tsaye daga bakin lofar dakin ta shiga, nan ta sanar dashi Jannah na bacci rahama kuwa tana assignment.

Wuce wa Aisha tayi ganin bai sake cewa komai ba, nan Uncle Abdul yayi knocking kofar jin muryar Rahama tana cewa a shigo yasa yace "Rahmatullah". Da jin muryar shi cikin sauri Rahma ta zuri hijab ta sa kan kayan baccinta.

ILLAR MARAICIWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu