Dangin Miji

156 12 3
                                    

"Al'ameen kana ganin babu matsala? I don't like the idea of them coming kuma su tarar da su Jannah basa gida" Sumayya ta fada tana kaiwa da kawowa.

"Relax Sumy ki dena daga hankalinki ae ba yawo taje ba makaranta fa taje that too with Rahma" Ahmad ya fada yana kokarin kwantar mata da hankali.

"Ni ba shine damuwa na ba remember the other time da suka zo nan da zamuje Saudi? Kaima kaga ransu baiso ganin yaran nan cikin kanan kaya ba duk da cewa decent abu suka saka". Sumayya ta zauna akan kujera hankali tashe.

Yaya zata fara fuskantar 'yan uwan mijinta da suke nuna mata tsana karara? Ita ba ma shine damuwanta ba idan suka iso kafin su Jannah su dawo daga school to tabbas za'a samu matsala kasancewar riga da dawando suka saka sai jacket da yake dai dai guiwa hade da gele da sukayi rolling.

"Wallahi sai yanzu nake da na sanin rashin dinka musu natives" Sumayya ta fashe da kuka.

Zama Ahmad yayi a gefenta yana dafa kai. Ba abin da yafi daga mishi hankali kamar kukan matarshi ko 'yayanshi barin ma yau da 'yan uwanshi zasu zo all the way from Nigeria. Bai ga laifin Sumayya da take kuka ba saboda su a kullum basa rasa laifinta tunda dama ba sonta suke yi ba.

"Sumayya so kike ki daga min hankali? Dan Allah ki dena kuka I know it's not easy amma Allah baya daura wa bawansa abin da yafi karfinsa" Baba ya share mata hawaye yayin da yake rike da hanunta

"Hakane Al'amin amma bani da yanda na iya". A hankali Sumayya ta fada tana kallon kasa.

"Says who?" Baba ya tambaya yana murmushi, ido ya zuba mata yana kallonta hankali a kwance.

"Huh?" Sumayya ta sake baki tana kallonsa, ganin tana kallonshi ne yasa ya daga mata gira.

"Ki dena Sumy mesa kike kallona haka? Nayi miki kama da wani ne?" Ahmad ya karasa maganan yana fixing collars enshi kamar yanda samari suke yi.

"Really Al'ameen?" Sumayyah ta fashe da dariya, har da rike cikinta.

"Ko kefa Sumy? At least grace me with your smile. Yanzu tashi musan abin yi." Baba ya mika mata hannu.

"Toh ae Al'amin basu da dresses ko gowns. Na kyautar da duka last month dan kwatakwata sun nuna basa so"

"Ba matsala we can shop online" a cewar Baba da ya dauko macbook dinshi.

"A'a baba ni nafiso muje Arabian mall dake kusa da gida kaga wancan fifteen minutes drive ne kawai"

"As you say wife"

Misalin 2:45pm suka dawo daga mall. Zama Sumayya tayi a dakin Rahma sai data jera mata duka a closet kafin ta shiga dakin Jannah bayan ta gama arranging stuffs din tayi wanka ta canza zuwa wani grey vintage gown.

Saukowa tayi ta kara duba komai gudun a samu matsala.

Turaren wuta,

Abinci,

Towels,

Toothbrushes,

Toothpaste,

Toiletries,

"Phew Allah please help". Rufe bakinta ke da wuya wayan Al'ameen ta fara ringing.

"Assalamu alaikum" Al'amin yayi picking call din had'e da sallama

"Eh na turashi tun dazu but I'll be on my way"

"I'm sorry gani nan zuwa" da haka ya yankar da kiran, juyawa yayi yana kallonta.

"Allah yasa lafiya" fadan Sumayya kenan. Ganin yayi shiru bai ce komai ba.

"Lafiya Ya Majid ne ya kirani wai sun yi landing. Sumayya come let's go". Ahmad ya karasa yana kokarin jan hannunta.

ILLAR MARAICIOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz