Sabon Al'amari

55 12 4
                                    


Jannah na zaune kan sallaya tana tasbihi bayan sallar asuba. Rahma kuwa tana goge mata uniform nata. Ko da ta gama zama tayi gefen Rahma da ta kammala gugar.

"Now that I'm done, You should go to bed baby. There's still an hour left. I'll wake you up at six" gyada kai Jannah tayi hade da rungume Rahma.

"Alright big sis, you should also have some sleep" murmushi Rahma tayi sannan ta lullubeta da bargo.

"I will, princess".

Tana fadin haka ta hau gyara dakin. Sai sa ta share tayi mopping har ma ta wanke toilet. Ciro wa Jannah jaka da sandals dinta tai sannan ta shiga wanka.

Fitowarta kenan taji ana knocking kofar. Hijabi  Rahma ta zura cike da mamakin wanda ke buga musu kofa karfe 5:48.

Ba karamin mamaki tai ba ganin Hafsa a tsaye a bakin kofar. Sanye take da kayan bacci.

"Morning Aunty" harara Hafsa ta watsa mata. "Ni rabani da kanan turancinki. Maza kuje ku dora breakfast". Baki Rahma ta wangale tana kallonta cike  da mamaki.

"Breakfast kuma? But mairo and  Aisha -" da sauri Hafsa ta katseta. " Dallah yimin shiru malama. Wani irin Mairo da Aisha zasuyi? Ke kike biyansu ne? Ko kuma me amfaninku a gidan? Kin San Allah idan baku yi girki ba babu me zua makaranta a cikin ku"

A fusace Hafsa ta juya ta fice. Jiki a sanyaye Rahma ta juya idonta cike da hawaye. Ita ba girkin bane damuwanta tunda ai sun saba yi. Amma mesa baza a musu uzuri ba tunda zasu school.

"Big sis?" Da sauri Rahma ta shanye hawayenta tana smiling ta amsa Jannah. "Why don't you sleep, princess. I'll be right back" girgiza kai Jannah tai tace. "Let's go I'll help you"

"Lil sis you don't have to-" kin kulata Jannah tayi sai ma kayanta da ta mika mata.

Misalin 6:37 dai dai su Rahma suka gama hada breakfast na fruit salad, omelette, toast, orange juice da tea.

Ko da Hafsa ta fara complain a dining table, Uncle Abdul ne yayi saurin katseta.

"Jannatul Firdaus go get your bag". Nodding tayi sannan ta wuce daki. Dama Hafsa da Ya Umar sun shiga ciki. Sulaimi na bacci Asiya, Ashir da Rahma ne suka rage a dining room din. Ganin Rahma ta hau tattare plates din yasa Uncle Abdul dakatar da ita.

"You don't have to do this Rahmatullah. I'll call Mairo"

"No Uncle Abdul, I'll manage" Rahma tayi forcing smile.

"I insist" ya sake fada. Hakan yasa Rahma tayi nodding sannan ta juya zata koma ciki ganin irin hararan da su Asiya ke mata.

"Thanks for the  breakfast, Rahmatullah" ta ji Uncle Abdul na fada. Sake murmushi tayi. Dai dai lokacin Jannah ta fito.

Rungume Rahma tayi "I'll get going, Allah Hafiz".

"Fi amanillah" Rahma ta amsa da sauri ganin 7: 16 kuma tana da lecture 9.

Ko da Uncle Abdul yayi dropping Jannah a school, ko sau daya bata yi magana ba. Dan ko yai magana amsarta bata wuce 'eh' ko 'a'a'.

Bundle na 200 Naira ya saka mata a jakanta. "Uncle you don't have to" da sauri ta ciro kudin daga jakanta. "I insist princess, hope zai isheki wannan week din?"

Nodding tai "thanks".

Murmushi Uncle Abdul yayi "take care, baby".

Nan ma gyada kai tai ta fice daga motar. Shiganta class ke da wuya taga Talib tsaye a bakin kofar. Tun kafin ta karasa ya zo inda take. Ko data fara zuwa school bai samu ya mata magana ba sai yau. Dan bata fi sati da fara zuwa ba akayi rabon gadon iyayenta, sai kuma yau ta sake zua.

ILLAR MARAICIWhere stories live. Discover now