Babi na Sha hudu

59 8 1
                                    

Har bada nayi alkawari ba zana barka ba komai wuya da Dadi kazaman riken amanah.
                                   Mahmoud Nagudu

Eid Mubarak to you and your family! May this Eid brings nothing but joy and peace for all. Have a safe and happy sallah🙏🏾🙏🏾🙏🏾

Tafiya take cike da yanga da taku dai-dai acikin harabar North West university Kano (YUMSUK), yau a city campus take da lecture waya take dannawa don bashi amsar sakon good morning da yai mata, ga duk wani saurayi ko namiji da yasan kansa yasan mace na matukar kaunar good morning text from her boyfriend or spouse ,abune da Mata keso Wanda ke alamarta ka damu da ita kenan , to haka ce ta kasance ga waleeda domin kwa munnir boyfriend din ta tuni ya Aiko Mata sakon good morning wanda tunda Suka hadu Bai taba fashi ba kimanin shekara guda da haduwar su Amma ga mutan gidan su wata biyu kenan da suka  sanshi yawanci sun fi waya in tana school , dai dai sanda ta tura sakon gare shi ta sami isowa lifter 7th floor ta fadawa lifter operator din.
       Lecture da zatai ta Organic chemistry wacce zata dauke su tsahon hour biyu wato takwas zuwa goma Kuma tasan malamin bashi da Wasa Kai gaba daya ma courses din yau masu zafi ne domin kuwa yau ma suna da physical chemistry Wanda Dr  ke daukar su visiting lecturer ne dake zuwa daga Bayero University Kano , Sannan har ila yau akwai Entrepreneurship Study course wannan malami ne daka BUS wato second floor yake masu , Ana isowa 7th floor ta wuce da azamar ta ta Shiga aji .Bayan gama EEF 4-6 munnir ya Kira ta wai in ta Gama Bari yazo suje ShopRite cinema kallo take tace Masa a'a Bata jindadi ayya sorry baby tace sayi waya, ta katse call din. Wato waleeda akwai rawar kai da Kuma San nuna ta waye ba abunda ya dameta take bin munnir su je ShopRite kallo abunsu ba tare da agida an Sani ba yawanci interval tsakanin lectures ta samu Sai yazo ya dauke ta su fice ,abunda ya hana ta binsa yau tsoro take ji saboda wancan karon yai kokari ta Bata Wanda da kyar ta Sha har fada sukai karshe Suka sasanta duk rawar kanta Bata yarda da soyayyar mint ba Sam, domin tana kyamar hakan matuka.

Aforestation ta wuce gidan Ni'ima sister dinta Wanda yanzu suke sati uku da dawowa kasa Nigeria ranar da munnir yazo ya gaida Ni'ima ita Sam guy din Bai Mata don akwai rawar Kai Amma ta fuskanci ya Gama sace zuciyar kanwar ta gashi by age ma zai Kai daddyn twins Bai taba aure ba haka yace , ta murda kofar falon hade da sallama twins dake zaune a falon Suka taho da gudu Suka dane ta suna zuba Mata surutu suma shigowar su kenan don an sama musu malami sunanl daukar karatun addini kafin sabon posting din Daddyn su ya fito Kar suyi ta zama haka, tsarabar da tashigo masu da ita ta Basu kafin su ka kyale ta wuce Kaya ta hau canzawa sannan ta daura dankwali akan ta gama warta ke da wuya akai knocking tace shigo Yaya Ni'ima ce

Assalamualaikum ta Fadi tana shigowa Ashe kin dawo

Eh twins sunce kina dakin daddy

Wanki akai masa  na ke jera Masa

Cike da tsokana tace "love things" tana dariya ,
Murmushi kawai Ni'ima tai ta dora da fadin Maamah tayo waya cewa lallai lallai ki koma gida Abba ya Fara fada ,ta dan bata rai ita fa ta fison gidan Ni'ima don mutum ya fi sakewa abun sa, Amma tasan tunda Abba yai magana ya zamar Mata wajib ta koma gida in ba haka ranta zai baci Kai har Yaya Ni'ima ma.

Zan iya cewa gaskiyar bature da kance life begins at 40 kusan hakan ce ta kasance ga barrister Aisha cikin kudurar Allahu buwayi gagara misali sun Sami yalwar arziki ta kowace fuska sun sami cigaba arayuwar su Basu da abunce cewa sai dai hamdala ta zama abar alfahari ga iyayen ta Kai har ma da garin su baki daya , yanzu da take matakin deputy rector da kananun shekarun ta yawan ci Sai mutum ya haura shekara 50 yake kaiwa wannan matsayin , Amma cikin ikon Allah Ta samu kaiwa nan, littafin da take nazarta na 1999 Constitution ta anje ta Kai idonta Kan agogon falon, mikewa tai ganin gab da magrib Amma waleeda na harabar gidan tana zance bata shigo ba mikewa tai don Sam Bata Saba dokar mijin ta , ta dauki hijab din ta zura ta wuce harabar gidan don kawo karshe tadin da waleedar keyi da saurayin ta .

Tana fitowa kuwa idon ya gano Mata irin zaman da waleeda da munnir sukai gab da gab abunsu akan kujerun roba kallo daya Tai waleeda tasan ma'anar kallon munnir ya Dan zame Yana gaida barrister Aisha ta amsa masa fuska babu walwala ta juya gida.sallamar sa Waleeda tai a kidime ta shigo gida a falo ta tarar da maamah

karki sake na Kara ganin kin zauna kusa dashi baki da hankali ne kinsan irin illar da hakan zai haifar kuwa ta fada kasan cewar mikin zuciyar ta ya motsa ta fada a zafafe , al'amari ne da bazai tabaya gushewa a ranta ba maganar da Bata taba furta ta ga kowa ba, shi *ciki badan tuwo kadai akayi shi ba* wannan maganar *Har Abada* ba Wanda zata fadawa dashi zata je makwancinta , Allah ya sani ba zata iya yafe Masa duk yana halin da yake ciki na rai kwakwai mutu kwakwai an kasa gane cutar da ke damun sa har ya zamto baya magana komai nasa ya Kare Babu, ita kanta baffa ya roketa ta taimaka da kamar bazata ba da komai ba Sai ta ga yaci albarkacin musulumci da Kuma baffa har ma da Inna da Kuma Yar sa wacce Allah ya taimaka tai aure , Allah ya taimake ta tayi aure a wani kauye Wai shi Jalam , kowa ya shede ta mutuniyar kirki ce kaddara ce ta fada Mata da Kuma abunda haifanta Suka shuka ta girba ,Dan da ta haife kakarta gwaggo yalwa ce ta karba ta rike shekarar sa biyu yai amai da kudawa na kwana daya ya rasu , lado nanan yana girbar abun da ya shuka duk Wanda yace aikinsa Zina da biyebiye karshensa baya kyau, Zina ita bashi ce ko baka da yara Sai anyi da bangon gidanka ,Allah ya shirya mu da zuri'a baki daya Amin ya rabbi.

"Abba Yana son ganin ka anjima " walida ta fada

Gyada Kai tayi Sai kazo to .

Wannan ya biyo bayan samun abban Ni'ima da maama tai akan lallai ai wa waleeda aure hankalinta Sai ya fi kwanciya

Anyi wani abunne barrister"Abba ya fada

Ba'ai komai ba Abba kawai dai Naga ya Kamata ace mun Kau da ita cewar barrister

Ya kalle cike da nazari Amma Bai fahimci komai ba ya gyada hakane,

Ki shaida Mata yaron Nan munnir ya zo Ina son ganin sa anjima in Sha Allah Kanna Gama weekends Ina so in ga magabatansa

Gyada Kai Tai cike da gamsuwa ,batai jinkiri ba ta Sanar da waleeda maganar Abba .

______________________________________

Karo na uku kenan ta daga Kai ta kalli agogon dakinta ikon Allah munnir yace Mata zaizo amsa kirar Abba Amma har yanzu shiru farko da taga yamma ta wuce baizo Sai ta alakanta hakan dacewa saboda da ba gunta zaizo ba , tunda yasan anything after magarib Bata fita sam, Amma ganin har goma na dare ba munnir ba labarin sa , ta gwada wayar sa da farko tana shiga daga baya kuwa Bata shiga hankalin ta  ya tashi matuka ta rasa Mai ke faruwa Kuma .........

#Say no rape
#team H.A
#Team waleeda
                                          Mrs Sadi 😘

Har AbadaOnde histórias criam vida. Descubra agora