Babi na Takwas

79 8 0
                                    

Ya Allah, we have done it to the best of our ability. Please accept it from us!
Do not make this to be our last Ramadan, grant us the opportunity to witness many more Ramadans in good health.
🤲🏽
Taqabbalallahumma minna wa minkum

Not edited please

Wannan shine yadda auren lado da Hauwa'u mamman gogaggiyar karuwa ya kullu bawanda yasan yai aure haka ya share gu ya zauna gidan rakiya ya shi gaba da buga bugar sa ya dawo ya iske abinci Mai rai da lafiya sannan ga gun kwana ga Mata kuma haba duniya tai Masa Dadi.Inda a bangaren kulu kuwa ta cigaba da sheke ayar ta San ranta amma da yake ta iya takunta lado bai sani shidai tunda Yana ci Yana Sha ai shikenan Babu ko kwabon sa.Bayan aure da shekara Daya kulu ta tillas tawa lado Sai sunje garinsu saboda da halin rayuwa acewar ta gwanda dangin sa su san da ita Kar ta haihu shi Kuma ya mutu Suki karbar ta,Yana Bata rai Yana komai sukayo Kano daga Kano suka Kwan Daya sannan suka wuce bauchi  suka zarta kafin madaki.Suka hau achaba ya Kara sa dasu gidan su lado.
Ga lado ga lado ga lado ihun yara kenan da gwagggo yalwa ta jiyo farko ta dauka tsokana don ganin yadda ta saka ran dawowar sa garin har tsokanar ta ake da hakan saboda haka ta cigaba da tuka tuwon ta abun ta kamar daga sama ta tsikayi murna ladon ya doka sallama mikewa tai da azama tana Kai duban ta kofar shigowa Sai kwa tai tozali dashi tare wata mata abayan sa Yar gayu ta Sha ado ,lado ta furta da mamaki shi kwa gogan naku Yan Kare hakora yai yana murmushi lale marhaba ta wuce daki ta dauko tabarma karauni ta shimfida musu sannan ta wuce Randa ta debo ruwa ta kawo sannan aka Shiga gaisawa da lado amma gaba daya Hankalin ta nakan kulu wacce take sunkuyar da Kai wai ita taga suruka.kasake tai tana kallon kulu ita dai wannan Mata basai an fada ta girmi lado sannan wayewar dake tattare da ita sai dai kurum ai shiru ,uhm ta fada lado ne ya muskuta yace Gwagggo nayi aure fa gatanan Hauwa  sunan ta shiru Gwagggo Tai tana jinjina lamari tace Bari baffa yazo tace Bata gama rufe baki ba baffa ya shigo kasacewar har labari ya baza gari lado ya dawo daga ikko yazo da kilakin sa abunka da mutane wasu suka ce har da goyo baffa na isowa lado ya hau gaishe shi haka ma kulu ya amsa musu kadaran kada han Nan lado ya hau sanar da baffa shifa yayi aure nannauyar ajiyar zuciya baffa ya sauke tare da fatan alkairi inda ya cewa yalwa zo maza a shirya abun tarbon amarya in Banda abun lado ya kamata ka sanar ai don ai Mata tarbo Mai kyau janye Gwagggo yalwa yai zuwa dakin sa kamar Mai jira ta hau cewa baffa kaga yaron Nan ko ni wlh ban yarda ba ,baffa yace haba yalwa kinsan Mai mutanen gari ke cewa Nan ya sanar da ita sannan ya Dora da cewa ai gwanda da aure sukai ba wannan zargin da mutane suke masa ba   yace nasan abunda yai bai kyauta Kuma Zan Masa magana ni dashi Amma Sai ba tare da matar sa ba Kinga in muka nuna muna adawa ada abun irin wannan Mata abun tsoro ne sannan wlh Allah ya sani dama nagaji da rashin auren lado ,gyada Kai take cike da gamsuwa sannan ta Dora yanzu baffa Ina zai anjiye ta yace Sai abashi aron dakin can da bashari ya gina tunda shi Yana kano Amma Sai yai sauri ya tada nasa ginin Don Kar bashari(kanin lado) ya zo gari ya rasa gun Zama nasan dai ko bashari na zuwa sainan da karshen shekara maza akama waccen kazar ki masu dahuwar daddawa sannan Bari ai samo shinkafa ko gwangwani biyu ce ki da fa masu abunka da mutunen kauye akwai Kar rama baki fitowa sukai tsakar gida baffa ya nufi kaza don yankawa yayin da gwagggo ke cewa ku Kara so nan gurin ta ja su zuwa sabon dakin dake kare Kara ta bude masu sannan ta wuce ta Danko tsintsiya da sauri kulu ta amshe (uhm nace bariki)  ta hau shara wannan ya sa ta burge Gwagggo cewa tai da lado zo ka dauko shimfida kan ku shirya dakin ta barma karauni ta dako masu da katifar rimi (abunka da uwa )har da buta ya dauko katifar suka kawo dakin aka shimfida tabarmar sannan Gwagggo ta juya don kin baffa ya Aiko da shinkafa don ta Dora sanwa ,abunda zai baku mamaki kulu fitowa tai ta zage ta Taya Gwagggo girki uhm harda jawo wa Gwagggo ruwa ta cika mata bokiti sannan itama ja nata tai wanka ta koma daka.
Wannan dakin na kani nane baffa yace aro kan na tada nawa lado ke sanar da kulu yayin da suka zo kwanciya ,ai gobe in Allah ya kaimu Sai ka Nemo magini ya fara Mana ginin yai saurin cewa ban da isassun kudi Wanda nazo dasu Naga baffa yai dawainiyya damu shine na bashi wani hakan Yana da kyau ai Amma karka damu zan yi komai in maginin yazo Zan Masa bayanin yadda nake  son ginin ya kasance Nima jira nake safiya tayi nakaima su Gwagggo tsaraba ya jinjina Kai wato tsaraba taiwa iyayen sa shikam ya more mata ga gini Zatai masu gashi dama tace zata Sai Masa hayis ya dinga jigila su Sami na cefane ita Kuma zata dunga abincin sayarwa (nace ba haye kikai ba gado ne lol).Cikin ikon Allah tuni anyi ginin ban garen su lado abunka da naira don kwa kulu tazo da ita Dan Kam ,tuni ya fara sanar tukin hayis saida abinci da kulu taso yi ne ya Dan tada Kura baffa ya so kin amincewa Amma da gwagggo yalwa ta goya baya tuni amince kasancewar kulu na yawan Mata alkairi yasa Bata son laifin kulu ko kankani,suna  cikin wadata abunsu don Basu nemi komai sun rasa ba,Wannan kenan .

#Team H A
#say no to rape
#Allah yai Mana maganin wannan annoba.
Barka da sallah thank you so much all
                                                 Mrs Sadi

Har AbadaWhere stories live. Discover now