Babi na Biyu

177 27 2
                                    

Daki ta shiga ta kishin gide da niyyar bacci, har ya fara daukarta sai wayarta tayi ringing duk da rashin kuzari da take ji a jikinta ta daga. Sai ta fuskanci ashe Mai Kiran barrister Ummi ce kawar ta da suka yi karatun neman degree na biyu a jami'ar Bayero dake Kano,Kuma yanzu suke cikin kungiyar lauyoyi Mata dake yaki da fyade da cin zarafin Mata da kananan yara.
Sai ta amsa wayar tare da sallama-Assalamalaikum wa'alaiki salam barrister kina gida ina son shigowa bayan sallar la'asar please akwai wani case but bana fyade bane shi,Ina son nazo mu Dan tattauna eh Ina gida barrister Sai kinzo ta kashe Kiran.
Misalin karfe 4:00 daidai barrister Ummi tai parking motar ta kirar KIA picanto red color ta fito fara ce doguwa Mai manyan idanu tana da aure da yaro daya ba zata wuce shekara 26 ba haka Yar asalin jihar Kano ce tayi degree ta na farko a Umaru Musa yar'aduwa University dake jihar Katsina ,taso yin karatu a Nan BUK Sai dai Allah bai kaddara ba Ashe rabon haduwa da mijin tane ya kaita Wanda ya kasance shima Dan Kano ne Amma da yake kaddarar haduwar acan take bayan ta kammala degree ta ta wuce law school dake birnin tarayya Abuja Inda tai ma law school bugu daya ta fito da grade Mai kyau shine fa sukai aure bayan ta kammala,sannan tai NYSC a national women commission dake jihar Kano kasancewar tayi marriage certificate Sai batai zaman camp ba bata wani Jima da POP (gama NYSC) ba mijinta ya samo mata aiki a NGO wannan ya bata damar daurewa ta koma BUK Tai degree na biyu .Inda anan ne suka hadu da barrister Aisha kamun kan Ummi da nutsuwa ya saka kawance ya shiga tsakanin su duk da barrister Aisha ta girme ta sannan ra'ayin su na yaki da fyade da cin Zarafin Mata da kananan yara da yazo daya Sai ya karawa friendship nasu armashi dama hausawa sun ce Sai Hali yazo daya ake abota .Jakar hannun ta kamfanin Suzan taa dauka sanye take da doguwar riga ta zuro kafar ta waje Masha Allah kunshine ja yai maroon gwanin ban sha'awa ta fito ta rufe tare da Danna lock ,fara kwan kwasa kofar ta keda wuya sai Ni'ima tace waye tai murmushi sannan tace Ummin ce, Ni'ima ta sauri ta bude hade da cewa aunty Ummi sannu da zuwa,tare da leka bayan ta,tace yau ba a zo da Jawad ba Sai ta saka murmushi ta tace daga gun aiki nake direct shiyasa. bayan sun zauna a parlor Ni'ima ta shigo da food flask ta ajiye ta koma ta kawo plate da su spoon,Sai lemon Exotic da cup hade da ruwan Myer shima ta ajiye. barrister Ummi tace sannu diyata,Ni'ima Tai murmusjhi sannan ta durkusa ta gaishe ta da wucewa dakin su bayan sun gaisa. Barrister ke cewa Umman Ni'ima Mai nasamu ne ta nuna food flask ,ai kina cewa Zaki zo nai Miki faten dankali Dan nasan kina son sa Kai nakwa gode matuka ko kinsan yau ko launch ban ba naje haka na bawa gate man na gun aikin wato wani case ko Umman Ni'ima yarinya ce sunan ta sahura talla take a kofar wambai to Sai ga ciki shine iyayen suka rutsata Sai ta kaisu gun wani yaro he is just 17 while ita Kuma only 15 shine suka ce ya aure da cikin fa barrister suke nufi yaki Sai suka Kai Kara police station sukuma suka Mika su court shine to kanin baban yarin shine masinjan office din mu wlh yazo ya roki Alfarmar na tsaya masu to alkali ya ce close door listening zai ma'ana babu Yan kallo since underage duk dinsu to Barrister Sai na zauna da yaron nake tambayar sa tsakanin sa da Allah shiyai Mata could you imagine Sai cewa yai shidai yasan tana Masa away nace meye away ya saka dariya ma'ana tana zuwa gunsa har dakin sa zance(kalubale Mata away din Nan Sam ba abun kirki bane kin Kai Masa kanki har dakinsa Mai kike tunani zai Sam ba wayewa bace zuwa dakin saurayi ko fita outing dashi saboda komai na iya faruwa sannan daga baya ya gudu ya barki babu aure Kuma yai Miki tabo har abada da bazai warke adai kula sosai akuma dage da addu'a Allah ya Kare Mana al'ummar musulmi ..... Amin ya rabbi). Barrister abunda ya fi bakantan Rai harda cewa shi fa ba'a budurwa ma ya fara mu'amala da ita ba kuma ai tana biye biye ranar Nan ma ya ganta da wani sun shiga shago uhm bayan nagama dashi Sai na rutsa sahura nace ta fadan gaskiya basai ga magana tiryan tiryan ba tana biye biye Amma duk akasuwa suke haduwa ba Wanda tasan gidan su sai shida da wani Mai shago shi Kuma Mai shagon data koma ta tarar Ashe haya yake ashagon gidan da yace na iyayen sa ne karya yake yama tafi legas Neman kudi,shi yaro ya rantse bana sa bane ita Kuma Sai kuka Taki ma fadin komai Banda wannan bayan danaji daga gare ta to wannan shine Abu na farko daya kawo ni na biyun Kuma akan Ni'ima ne kanin Abban Jawad Wanda yai International studies a ABU eh Nura ko shifa to ya Sami aiki da embassy Kuma anyi posting Russia Masha Allah Allah ya temake shi yadda aiki ke kamshin dan goma akasar Nan eh wlh fa shine Abban Jawad yace in tambayo ki anwa Ni'ima miji dariya barrister Aisha ta saka da an Mata ai Zaki sani barrister Alhamdulillah to dama Nura muke so yazo gunta tare da fatan ai aure In yaso ko daga baya yazo ya dauke ta su wuce can kasar ,to yanzu dai Abba Ni'ima baya gari but this week zai zo weekend in Sha Allah Zan sanar dashi duk yadda mukai kyaji jimu, Amma barrister Anya yaron Nan minor ne Wanda ake zargi da yin ciki kudai bincika please don in ba'a hukunci ahaka suke cin bulus dole dan rashin hukunci ke sakawa hakan yake ta faruwa ta fada ranta na suya amma Umman Ni'ima bakya ganin harda laifin yarinyar ai ita takai kanta gunsa in bera na da sata ai daddawa nada warin ta ya za'ai mace baliga dake ki dauki kafa kije dakin saurayi zance haba wannan rashin sanin darajar Kai har ina suma iyaye da nasu barrister ki tura Yar ki talla kasuwa ta fita tun safe har magarib wata ma har Isha amma ko ajikinki wlh barrister ko islamiyya su Ni'ima suka tafi bani da kwanciyar hankali har Sai sun shigo gidanan Allah ya shirya mana zuri'a baki daya barrister Aisha ta fada hade da sauke ajiyar zuciya haka barrister ummi ta Kare shan fate Sannan sukai sallama akan cewa duk yadda sukai da Abban Ni'ima Zatai notifying din ta.

*Adinga Wasa Ana dariya Dan tauraron Nan na gefe yauwa kina karantawa Dan danna please*😀😃
Yana Kara karfin gwiwa fa pls comment.
Thank you maman abeela 😍

#Team H A#
#vote & share pls#
#Mrs Sadi#

Har AbadaWhere stories live. Discover now