Babi na uku

128 15 3
                                    

Thank for the love & support family & friends.This page is for you my sisters Engineer Aisha Badawi & Mrs Badawi S .S 😘
#Not edited please #

Yau ta Kama Friday yau ake saka ran
zuwan abbansu Ni'ima weekend gyara musamman barrister tayi tai tuwo shikafa miyar wake Wanda yaji Ugwu ganda da stock fish miyar tai shar saboda man ja da tai ammafani dashi, sai tai kunun gyada san nan Tai zobo saboda shi bai fiya son carbonated drinks ya fison natural don sun fi ammafani ga lafiyar dan Adam.Bayan sallar juma'a ya iso Don ahanya sallar ta riske shi wanka ya fara sannan ta gabatar Masa da abinci yaci yana buga Santi Wanda dama indai yaci abincin ta Sai yayi Santi tare da Sanya Mata albarka , bayan ya kammala ne yaran suka zo suna gaida shi tare da Masa bangajiyar hanya ya tambayi kowa game da makaranta sannan ya Kare da cewa uwata (walida) ya makaranta Yana kunshe dariya Don yasan ta da rashin son zuwa makaranta akwai Nan korafi ya tashi kowa sai da dara don dama haka halinta yake Bata son zuwa makaranta yace ahaka Zaki Zama barrister kamar Umman ki ai Sai andage uwata Kuma Ina da kyakyawar kyauta ga duk Wanda yai kokari islamiyya da boko , Ni'ima tace Abba nifa kenan bani a kyautar tunda nai candy a boko islamiyya Kuma munyi sauka kina da ita Ni'imatullah ayanzu ma akwai kyautarki barrister ya kalla danko jaka ta (Nima naje Malaysia Jakar goyo school bag)ta kawo hade da durkusawa ya zura hannu ya dauka packet din bounty ya mikawa waleeda takarba cike ta murna harda gwalo ga waleed sannan ya miko mata wani hijab sai fara'ar waleeda ta karu , J.C ta Nigeria wacce sukai amfani da ita a world cup ya mikawa Waleed da Nura suma tuni fuska ta washe aka shiga godiya har waleeda, Ni'ima ya kalla meye tukwicina tace Abba komai ma yace to Zan zaba kwalin waya ne samfurin kamfani Infinix ya mika(S5 gold) ,Sai su waleeda aka dauki sowa masha Allah ya Ni'ima kin more wlh barrister ma ba'a barta abaya ba wajen cewa abbansu ka gwangwaje Ni'ima Allah ya Kara budi Ni'ima ma godiya ta hauyi har Sai da yace ya Isa je ku shirya zamu dogon nama anjima duk suka Mike suna Kara godiya baki daya barrister ta turo baki dear ni bandani yace taki special yanzu dai ga wannan hijab ne biyu naki Daya na'ima naji ance Wai komai hannu pocket Kai Abba nagode dama Ina son siyan irinsu ragowar Kuma tsarabar zaki ganta zuwa anjima nagode Abba Allah ya raya zuri'a Allah Karo budi Amin my barrister.

Karfe tara na dare take masa bayanin kanin mijin barrister ummi dake neman iznin zuwa gun Ni'ima , barrister yazo ai tana iya cigaba da karatu Don aure baya Hana karatu haka ma karatu baya Hana aure but in zaizo ya zo da yamma banson zancen dare sannan su zauna a drive inn suka saka kujerun rabo sauran dai duk nasan Zaki tsara I trust you ya fada Yana murmushi.washegari kasancewar Yana da daurin aure karfe 10 a dogon nama ya saka suka tashi da wuri yai breakfast ya wuce sai da yaran suka tashi suka baya Nan don ma sun hadu gun sallar asuba, wayar ta sauka ta Kira innar ta baayan dogon gaishe gaishe ta hada da tambayar malam cewa tai bayan nan ya tafi caji ofis ,caji ofis Inna barrister ta fada kedai bari Hajiyanan wato matar kawun lado aka Kama da abokin lawandi wani bakin ciki hade da radadi ne ya ziyarci barrister jin sunan da aka ambata Bata kaunar ko sunan afada bare Kuma shi Mai sunan ita fa samma Bata son abunda zai hada ta shi Tai nisa a duniyar tuno mugun halin kawunta lado tuno abun yake aikatawa agareta tuno mummunan hoton abun da yake aikatawa akanta ba tare da ya tuna halaccin iyayenta gare shi ba ba tare da ya tuna alakar da ke tsakanin sa da mahaifiya ta ba ba tare ya duba girma Allah ba yake aika ta Mata abun Allah ne shaidarta abun ya na ci Mata Rai matuka kullum kwanan duniya Sai ta tuna shi ,Nisan da tai a tunani ya saka Bata ji me innar ke cewa ba Sai da innar taji ba ammasa ta ke fadin kina jina da karfi Wanda shi ya dawo da ita daga duniyar tunani sannan ta dawo ta dora da cewa Allah ya sauwake ki gaida da malam Sai anjima Inna girki zanyi ta katse layin ba tare da ta jira amsar innar ba.A bangaren Inna ta rasa Mai yasa tun zamanin kuruciya hajiyannan Bata son maganar lado sau da dama ko aikenta zai in yace ta zo ba ta zuwa Sai dai in innar na gun daga baya kuwa kirikiri take cewa ba zata ba yanzu kuwa komai hirar da kuka dauko inda zaka sako lado to hirar ta katse numfashi ta sauke hakika tana son sanin dalili Sai dai tambayar duniya hajiyannan Taki bada amsa(kalubale iyaye matukar Yar ki ko Dan ki yananu baya son zuwa gun wani to karki tursashi shi kadai yasan dalili a kiyaye tura yara dakin samari Kai musu Abu pls Allah ya Kare Mana zuri'a baki Daya).

In Sha Allah a next chapter zamu tashi labarin barrister Aisha muji Mai kawu lado yai Mata anan zamuji sakon labarin .

#TEAM AH#
#TEAM Barrister#
#TEAM Lado#

Yauwa adinga karfafa gwiwa pls Vote & share with family and friends pls .Adinga Danna tauraro pls😀 number of votes yana Kara karfin gwiwar typing one love 🤝

#Mrs Sadi

Har AbadaWhere stories live. Discover now