Babi na shida

105 12 0
                                    

In the Midst In the  monstrosities and discouragers, Have emerged the best of winners. You can be a winner too, cause you already have the blood of winning in you. You simply got to believe in yourself, and your destiny will be kept in good health. ☺️😊

Lallai brain din Esther tana ja hakan take ayyanawa a zuciyar ta bayan taji duk plans din Esther wani mutumin kano ne waishi gagarau anai Masa kirari gagarau ka gagari kowa shi Kuma ya bada amsar Banda mata garin shige shigen Esther suka hadu a wani club a jihar Anambra taje neman saurayi Wanda ya kasance Igbo Kuma bai taba tarayya da mace domin kaiwa ojuju akan wata sa'a da take nema agun ojuju shine ta hadu dashi Nan da Nan suka saba da yake shima takadarin kansa, shi yai Mata hanyar da ta sami yaron ma ta mika shi ga ojuju akai Mata aikin dashi to anan suka saba sosai har in dai akace ta kawo jini to gunsa take nufa don ya iya shirya harkalla gwanine shi amma ba fa gwanin na iya na cikin littafin Gwanin na iya na Maimuna  Beli ba lol.Murmushi yayi bayan  Esther Tai Masa bayanin abunda ke gaban su dakuma  kancewa sunan son Caroline ta iya hausa sannan ta samu Zama garin a matsayin mai sai da abinci duk wannan abun naku bazai samu damar aiwatarwa sai sun kunjiyo sunan garin da mutumin ya ke domin jihar Kano akwai girma da fadi ga al'umma da yawa sannan Sai kin koma musulma a idon duniya sannan zasu dinga zuwa siyan abinci maganar koyan hausa Kuma aiki nane nawa zaki biya Ina da hanya cike da dauki Caroline tace name your price dariya yai yace 1 million wani murmushi tai tace ta amince take yace sati ya war haka ki Zama cikin shiri Zan dawo.
Kamar yadda ya alkawarta masu ya zo musu da bayanin mai gamsarwa kan ceewa shi da Caroline zasu tafi cikin hausawa su zauna a matsayin Mata da miji a matsayin mai sana'ar kira Kuma bafatake wadda sana'a takai shi kudu har ya hadu da Caroline ta nuna sha'awar musulumta danginta suka ki da ta musulumta a boye Sai suka kore ta shi Kuma shine ya ji tausayin ta ya aure ta, tafa Masa suke suna jinjinawa kwanya irin ta sa Caroline da tai amanna da maganar sa ta Kara da cewa this northerner is very clever wooo, Amma Esther NYSC Dina fa inna tafi dariya Esther karki damu zanyi kula da wannan karki manta muna da connection.
Malumfashi dake jihar katsina anan suka sauka wannan labarin kanzon kuragen shi suka fada kasancewar katsinawa akwai Kar rama bako tuni aka amshe su hannu bibiyu tuni Esther ta Shiga ta fita aka sakewa Caroline relocation zuwa Government Boys Unity college Malumfashi inda zata cigaba da yiwa kasa hidima kasancewar makarantar kwana ce Sai aka Bata gida Mai dauke da daki daya da falo Sai toilet da wani corridor inda anan take girki , Chemistry shine abun ta karanta a jami'a Kuma shi aka Bata zataiwa dalibai anan ma wannan dama da suka samu shi ya Kuma sakawa gagarau bai Kama masu gida ba kamar yadda suka tsara. A hankali ta fara sabawa da mutane ta fara fahimtar yaren hausa Yan kana Nan kalmomi daidai, maman humaira Wanda ta kasance matar wani malami anan staff quarters itace makociyar Caroline ta temaka matuka wajan iya yaren hausa da Caroline tayi .A bangaren Esther Kuwa Sai dai suyi exchanging latter tunda lokacin babu G.S.M Sai landline ita Kuma  Babu a staff quarters bare ta Kira tunda akwai agidan Esther wacce ke staff room kuma ba zai yiwu ba tunda suna tafiya ne akan sirri sai dai duk wata suna haduwa gun meeting dinsu na agun Ojuju.
    Kwanci tashi asarar mai Rai yaune su Caroline keyin POP kowa ka gani cikin shigar kakin NYSC fuskar sa dauke da madaukakin farinciki kasancewar burin kowane graduate shine ya samu kammala bautar kasa lafiya ya karbi NYSC certificate dinsa,can na hangi caroline na tsaye ana ta fara'a da certificate din ta a hannu.Bayan kamala bautar kasar ta gagarau ya kama masu gida suka cigaba da amasa sunan mata da miji a idon duniya yayin da ta Zama kamar daduron sa a fakaice sai da suka Kara shekara guda a Malumfashi sannan suka ce ya Sami aiki a wani kamfani a jihar Lagos suka tattara suka koma jihar Lagos inda dama zaman baruwan kowa da kowa ne suka buga rayuwar su a agege Lagos na shekara guda sannan suka tattara suka wa jihar Delta tsinke zuwa gidan Esther.Ta Jima tana zagaye uhm caro ta ambata ta jinjina shu'umanci Gagarau domin kuwa caro ta goge iya gogewa hausa ta Shiga bakinta haka ma yaroba da take ji saka makon zaman agege ya saka idon ta dada budewa tar salute tai wa gagarau Wanda ke busa sigari what is Next ? Cewar Esther tana zubawa gagarau ido KANO ya ambata da ma daukakin sauti,kafin na tafi Kano  Zan kaiwa Ma ziyara tunda na shiga camp rabo na dasu da yake dama Bata damu ba ko takaina bata bi ba cewar Caro ,kallo suka maida kanta Wanda nima na maida na wa idon kanta gogaggiyar mace nagani fara tas da ita Mai manya ido da gashin kari bisa kanta ta Sha Dinka buba abunta da akai Mata da wata atampa wacce ake Kira da Mai tabarma  tayi daurin ture kaga tsiya bakinta bajau da Jan janbaki hannun ta dauke da farce irin na kari hancin ta an bula ansaka barima aciki Wanda tayi shi azaman ta a Malumfashi zamanin bautar kasa kunnen ta ma huda uku ce jere Wanda biyun ta Kara ne a Lagos agun kawarta Rhufkatu takalmi flat ne akafar ta sukan su yatsun kafar an saka masu farce an bishi da Jan janfarce ya tsina fuska ta Kuma yi it's almost 3 years fa dole na leka gida ta fada tana jijjiga jiki cike da kasaita da jin kai a matsayin ta cikakkiyar mace Mai Jan zaren zamanin ta.
         Kano ta dabo tumbin giwa ko dame kazo anfi ka  Mai Mata Mai mota Mai dala da goron  dutse garin cinikanya da kyautatawa bako gari ba Kano ba dajin Allah, Tashar Kano line dake Nan kofar nasarawa suka Shiga domin tafiyar dake gabansu mota Mai zuwa garin kachako (Aisha Bello & Rabi'a Sani Ina fata kun tuno kck) suka hau ita da wata Mata habi wacce gagarau ya hada su Kuma itace taje har garin duburde ta bude Mata gun Sai da abinci da zai Zama mallakinta wanda kawai nuna Mata Zatai ta dawo don basa son aga wata fuska da za'a shaida dan gudun bacin rana Caroline wacce ta koma sikiratu ta dago kanta sanda taji habi na cewa kwandasta akwai na Durbunde fa bambam ya buga motar suka sanko aka sauko masu da trolling su suka wuce Kai tsaye inda gidan abinci yake ta nuna mata ta Bata mukulli kamar yadda aka umarci habi ta juya ta koma bakin titi don hawa motar wudil Bata jin zata iya komawa Kano ayau don jikinta sai yai ciwo Kuma tasan in ta tsaya ta kwana a Durbunde Sai gagarau ya ji labari Kuma tasan kwanan zance in hakan ya kasance.
Haka sikiratu ta Kama siyar da abinci baka Kama bakin yaro gashi tana ciniki sossai nan da Nan Yan daudu suka Sami gu ba wadda ya san daga Ina take Kuma an kasa tuhumar ta Sai dai ai maganar kawai don tuni Ojuju ya rufe masu baki a haka suka hadu da mamman Wanda da farko ya so kin kulata Amma da yake ta hada da tsafi da Kuma ungo bi ma'ana bashi kyautar abinci Sai ta samu kanshi Wanda  sukai aure bayan gwagwarmaya da dangin sa har ta haihu Ojuju ya sanar da ita Abu na gaba bayan yarinyar tayi shekara 15, azaman ta da mamman ita din zata iya bugar kirji tace tabbas musulmi da  hausawa mutanen kirki don ba ta inda ya rage ta duk da tana sana'a komai zai Mata daidai karfin sa , haka take zuwa meeting da suke na kungiyar su a duk wata ta hanyar isgar da Ojuju ya bata haka in tace tatafi Kano sayen kayan girki suke mahada da gagarau da Esther in tana da lokaci acikin sabon gari suke haduwa.

Hey nasan yanzu kun fara fahimtar in da muka dosa to gadai labarin sikiratu da yadda akai abubuwa suka waka na .In Sha Allah next chapter will be coming soon
*a daure adinga voting pls Kuma ayi sharing ga family and friends nagode *Ana tare irin sossai

#Team H A #
#Team Innocent#

#Mrs Sadi

Har AbadaWhere stories live. Discover now