🌵🌵🌵Babi na Tara🌵🌵🌵

91 11 0
                                    

   Shi so sa'a ne Kuma sannan alkairi ne na Sami gwanata Mai sharen kukana : Hamisu Breaker😍

"Democracy is government of the people by the people and for the people "Abraham Lincoln.
HAPPY DEMOCRACY DAY

Kyakkyawar budurwa tana tafiya kamar Bata son taka kasa cike da nutsuwa take tafi daga ganin ta kasan bazatai hayaniya ba ga wata Kamala ta musamman tattare da ita hayaniyar sauran dalibai ke tashi kasancewar yau ranar farin ciki ce gare su Rana ce da Yan aji shida (SS3) suka rubuta jarrabawar hausa wacce ta kasance ta karshe a jadawalin Jarrabawar su ta National Examination council (NECO) sun shafe  wata hudu zuwa biyar rabon su da gida kasancewar sun zauna extension domin zana Jarrabawar WAEC a wancan lokacin gwamnati na Samar da komai na amfanin dalibai wannan yasanya ko kwasar kayan practical basu suje ba ga Wanda suke daukar darasin Food and Nutrition da Kuma home management,fadada fara'ar ta tai domin hango mahaifin ta abun alfaharinta sauri ta Dan Kara Wanda duk da haka Sai da ya Zama kamar yanga kafin ta Ida karasawa ta hango shi ya tsuguna yana gaida baffa gaban ta ya bada ras, rage sauri tai Wai ko kafin ta karasa zai tafi Sai gani tai ya dada Jan zance a zuciyar ta take raya kome  yake agun baffa oho bata gama tunanin abun yi ba taji an kwalla Mata Kira Aisha Umar ta waiga wata class mate dinta ce Kauna Moses yar jihar adamawa ta dora da fadin kije inji sir lawal gyada Kai tayi domin tari ga tasan tatsuniyar gizo Bata wuce ta koki bai wuce ya sake jaddada Mata kaunar da yake mata ita Kuma sam ba wannan a tsarin ta ba wata soyayya aganin ta maza macuta ba abun yarda duk halin su daya in ta tuno abunda kawun ta lado yai Mata sannan ta tuno da yadda Salma ta cikin littafin KADDARAR SU (next novel dina )yadda mijinta ya ha'ince ta Bayan ta bashi yarda dari bisa dari Sai ta Kara tsinkewa da lamarin maza ranta ya kara Kuna Shiyasa bata da wani buri da ya wuce ta Zama lawyer domin yaki da fyade da cin zarafin Mata da kananan yara maganar baffa ita ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fada gaishe shi tai cike da ladabi ya amsa yana Mai Taya ta murna sannan yace ta dauko kayan ta don su wuce su karbi pass don fita daga makarantar.
Dawowar ta gida tarar da abubuwa da yawa sun faru ciki har da auren kawu lado , tunda ta dawo take zuba Ido taga ko baffa zai Mata maganar Dan anace Amma taji shiru bai ce Mata komai Sai Kuma samari da sukayo Mata ca suna sonta Wanda ita kuma Inna take ganin ta Sami jari ba ruwanta da nagartar mutum Sai tace Sai ta fita baffa ya Ankara da barna da Inna ke kokarin yi Masa a gida ya tsawatar ya tauna tsakuwa don aya taji tsoro ta Kuma ji din domin Inna ta Shiga Hankalin ta.Da wani yamma ci baffa yai wasu baki manyan mutane wanda har fura aka dama masu, Aishatu tarasulu baffa ya Kira ta jitai gabanta ya fadi don tasan komeye Mai mahimmanci ne ,Aisha na karbi kudin auren ki yau din nan ban Kuma karba ba Sai danai bincike akansa da danginsa Alhamdulillah  mutum ne nagartance shiru tai tana tunanin ko waye ita fa karatu take son cigabawa kamar baffa yasan me take tunani ya Dora da cewa munyi maganar karatun ki dashi Kuma ya amince don  nasan kina matukar son cigaba da karatu to aure baya Hana karatu Aisha me Kika ce kanta ta Kara nutsarwa cikin cinyar ta sannan ta tashi da sauri murmushi yai danganin me tai, Sai Bayan ya Gama ganawa da Aisha ya sanar da Inna wacce ta washe baki jin cewa Kano za'a Kai Yar ta sannan ga kudin aure suna da yawa lallai Yar tayi goshi zata huta maganar da ake yada Mata kancewa Yar su nacan na boko babu aure babu tsayayye.
Zaune yake akan tabarmar da baffa ya shimfida Masa yana jiran fitowar Aisha domin su daidaita tana fitowa ta ganshi gaban ta ya bada ras sarki naci ta fada cike da madaukakin mamaki ba tare da tasan a bayane take maganar ba murmushi ya haske ta dashi kafin yace Kara so to dama sunan da Kika sakan kenan Kara sowa tai kamar mara laka inda ta hau tuna yadda akai yasanta wato career week sukai a makaranta Inda su gabatar da bayanai game da career dinsu shi sunan sa Sulaiman Muhammad Dogon nama ya karanci Geography a ABU zariya akwai job opportunities ga Wanda ya karanci Geography inda ya sanar dasu shi yanzu Yana aiki da National Hydrological Service Agency (NAHSA) parastatal ce dake karkashi Ministry water reasource aikin su shine nemo kasar da ta dace da ahaka domin samun ruwa akarshe ya rufe bayanin sa da he is a hydrologist & he is proud to be one ,tafi aka dauka rafraf rafraf cike da admiral students ke kallo duk Wanda suka gabatar da bayanai game da career su suna fata Allah ya su ma watarana su cinma buri kan su daga Nan aka gabatar da quiz Wanda Aisha tana ciki to tun anan ta fara daukar hankalinsa Bayan an gama Sai akai debate sannan aka gabatar da weather forecast (hasashen yanayi) domin nishadantarwa anan ma aka gabatar da Shirin inda kamar yadda suka tsara aka Kira bakuwa ta musamman aka tattauna game da yanayin damuna dake gaba towa akai fashin baki Wanda Aisha Umar kafin madaki  itace bakuwar ,Abu ne da bai taba samun sa wato ya ji ya fada tarkon kauna Wanda cikin Yan mintuna ya tafi hasashen har sunyi aure sun hayayyafa (hahhh fairy tales kenan injini)  kasancewar  ta mataimakiyar kungiyar geosa ya saka HOD geography na makarantar su ya saka ta kan hidimar kawowa baki abinci ta saka junior suka dauka ta wuce gaba domin kaimu su e-library inda akai masu masauki ya bita da Ido kamar idon sa zai fado kusan duk Wanda ke gun ya ga wannan kallon nasa gareta kafar tai ta hardewa Kamar zata Fadi azuciyar take cewa wannan ya cika kallo😂😂.Karaso Mana Aisha ya fada wannan maganar ta dawo da ita daga tunani kujera Yar tsugona data fito da ita ahannunta ta zauna akai nesa dashi cike da kunya murmushi yai bai Bata lokaci wajan Yi Mata bayanin Kansa Wanda ya riga yaiwa baffa sannan ya fada Mata in Sha Allah Bayan sun aure zai nema ta gurin karatu domin cikar burin ta na barrister dagowa tai tana kallonsa  yai murmushi kinyi mamaki ko ai inda so da kauna ya kamata na sani murmushi ta saki ba tare da ta shirya that's is my girl ya fadi Wanda ya hadda sa Mata boye fuskar ta cikin  tafukan hannun ta dari bisa dari taji yai mata ta amince zatai rayuwar aure dashi Wanda take fata *Har Abada* su  kasance tare ya zamo maji bancin lamuranta sannan uba a wajan yaranta Allah Amin ta fada a ranta.

🌵🌵BISHA   SAUDIYYA🌵🌵

Wata macece take ta tikar aiki kamar me daga gani tayi haske zamannin kuruciyya sannan daga ganinta idon ta abude suke Sai dai abunda ake cewa duniya jujuyin Wai kwado ya fada ruwan zafi to yanzu dai da alama duniya Bata yi da ita ta juya Mata baya ko muce Tai mata attishawar kura Salma aka Kira matar dake aikin ta dago na'am hajja baki karasa ba har yanzu wankin geron kwano goma ne ya gagareki lallai baki shirya tara kudin jirgin komawa gida ba na kusa gamawa hajja maza kiyi da jiki katuwar matar ta fada ,sauri ta cigaba da yi tsayawa nai Ina kallon ta nikai Sai da razana ganin ba wata bace illa Caroline ko Kuma sikiratu zance mahaifiyar rakiya mamman durbunde uhm nace Kam dana tuno gayun ta da ado da kudin da ta rike ko ya akai aka haihu a ragaya masu karatu Mai yakaita saudiyya? Naji ance Mata Salma kuma ikon Allah sai kallo.

WAIWAYE

Bayan barin su garin durbunde ita da yar ta rakiya Kai tsaye filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano International airport suka nufa anan suka tarar Gagarau (kun tuno shi just check chapter six)inda ya damka masu ticket dinsu kasancewar rakiya wannan ne Karo na farko da zata Shiga jirgin sama ya sata yin kauyanci jirgin kabo air suka hau inda suka tsaya Abuja daga Nan suka lulala Delta da saukar su Carolina ta Danna waya (public phone booth) kancewar sun iso ita dai rakiya Sai binta da ido take domin dai taji mahaifiyar na wani irin yare parking lot suka karasa anan suka tarar da driver yana  jiran su da sauri ya karbi jakar su ta hannu (hand bag) Wanda itakadai suka taho da ita ya bude masu gidan Bayan suka fada lumshe Ido rakiya tai tana tunanin Wai yau ita rakiya itace a motar gida ba bus ko akuri kura ba ikon Allah inda ranka kasha kallo.kai tsaye gidan Esther suka wuce suka samu tai masu tarba Mai kyau daga nan wanka suka wuce Wanda Sai da Caroline ta koya wa rakiya yadda ake amfani da abubuwan toilet Bayan sun yi wanka suka ci abinci daga Nan akace rakiya taje ta huta sun kwaso gajiya tamboyoyi ne dankare a ran rakiya Amma ta adana su tanajiran zuwa su kebe da mahaifiyar ta.

Please vote and comment share with family and friends

#Team H A
#Say no to rape
#No cultism
# Ana tare 🤝

Ya Allah kaimana maganin wannan annoba stay at home stay safe.

Mrs Sadi 😗

 

Har AbadaWhere stories live. Discover now