🌵🌵Babi na goma Sha biyu🌵🌵

71 10 0
                                    


Not edited please

Life's A Surprise They say, life can amaze you, For it can bring abrupt changes and turns. But life is just a joyful ride, For the one, who with experience learns. A dream, an ambition, it is all attainable, All you need to do, is believe. A hope, some faith, will find its way, All you need is an eye, to perceive.

Call off latter ta fito inda duk da marriage certificate Sai da aka tura ikare akoko NYSC camp dake jihar Ondo ,Abba su ni'ima ne ya dauki ragamar raka domin tai registration ta Kuma karbi exist ta fito a ranar ba tare da ta kwana sannan ta Sami automatic redeployment (relocation).Tashar unguwa uku sukaje suka yanki tickets a notary kamfanin Big Joe washegari karfe 6 na safe suka dauki hanya cikin hukuncin ubangiji kan dare sun Isa Kuma directly suka wuce camp ta fara registration Wanda dama tuni wani abokin aikin Abba ni'ima ya hadashi da wani NYSC official ga duk Wanda yasan NYSC camp ya San ba'a bacci kwana ake Ana registration karfe 9:30 na dare Tai signing out daga camp suka Sami hotel na Mai suna Nova suka kwana washegari suka sake nuko gari zuwa kanon dabo.Bayan kwana ashirin da Daya (21) da ake a camp ya karbo mata relocation Allah ya taimake aka barta a Gwale local government sannan Kuma a Kano state polytechnic school unit Kuma school of management. A haka dakika ta Zama mintuna ,mintuna suka koma awanni , awanni suka koma kwana,kwanaki suka koma sati ,sati ya Zama wata ,wata ya Bata shekara har ta kamkala yiwa kasa hidima Wanda Allah ya amince ta Sami aiki da a inda tai NYSC watan uku da fara aiki Abba ni'ima ya cike Mata Post graduate diploma in education (PGDE) anan F.C.E Kano haka ta gungura tayi cikin watanni tara sukai teaching practice na wata uku suka karbi saka mako Nan ma bai barta Sai da sa ta nemi license na zama yardanjiyar malamar makaranta,daga Kuma BUK ya nema Mata MSC inda anan ta gamu da barrister Ummi har suka kullum kawance ,Mai zatace da wannan mutum Mai dinbin alkairi gare tsakanin ta shi Sai addu'a .
-----------------------------------------------------------
Abu Kamar Wasa maganar auren ni'ima ta kankama duk bangarorin biyu suna ta Shirin biki tuni har an kawo lefe.Komai cikin mutumci da Kamala ake gudanar dashi abun geanin ban sha'awa ,sau da dama barrister in ta zauna Sai take tunanin Wai yau itace zata aurar da yarinya lallai yau da gobe bata bar komai ba.

A Daya bangaren kuwa kawu lado nacan caji ofis a tsare sakamakon ta'asar da ya tafka Bayan ya Kama Aminin sa da rakiya suna cin amanar sa abunda lado bai sani shine rakiya da Aminin sa sun jima suna mu'amala tun Bayan da suka fitar da kofar su daban daga cikin gidan su lado kuma bashi kadai take kulawa a'a suna da yawa Kuma dama ita tajima da cire mahaifarta saboda haka tasan ba maganar haihuwa ,wato lamarin ya faru ne Kamar haka lado yai sallama da rakiya kancewa zai tafi Tasha ai Masa lodin Kano Kamar yadda ya Saba sukai sallama ya tafi yanayin garin na damuna saboda haka bayan rakiya ta kimtsa gida Sai ta nade agado abunta jitai Ana mata tafiyar tsutsa ta bude idon ta ya sauka Akan Aminin mijinta Kuma kwartonta Nan take ta saki murmushi Dan tasan zata Sami kudi cewa Tai ya zauna bari ta kuskure baki har kullum abunda take burgeshi da rakiya kenan akwai tsafta  ta kwa dawo suka Kama kazamar mu'amalar su ba ko shakka danshi da idon da yaga tashin motar lado sannan ya taho gidan sa gun kulu ,shikwa lado anma Lodi sun dauki hanya suka tarar gada ta karye babu damar wucewa yayi takai ci matuka da suka ga ba mafita haka suka taho gida suna cizon ya tsaya bacin Rai ya saka ko zama baiba a atasha yaiwo gida abunsa ya shigo ba tare da sallama ba dama ba al'adar sa bace yin sallama in zai Shiga guri Yana zuwa ya ga wani filankin Kato ya rasa daga Ina oho Sai ya dauka a hannu ya nufi daki da nufin tambayar kulu wannan fa abunda ya gani adakin ya saka Tai mutuwar tsaye ai kuwa su Basu ankare dashi bama ya daga murya ya kurma ihu kwarto abunka da kauye duk akayo gida haihuwar uwar su aka tarar dasu lado ya daddage kwaftawa Aminin sa katakon hannu San aka sannan ya laftawa kulu abaya ta gantsare tana ihu daga ita har shi sun manta babu Kaya jikin su sukai hanyar fita daga daki Sai ta tuna ta ja beedsheet ta rufe jiki daga Nan akai gun Mai gari dasu daga canma ganin yanda lado ya kunburawa Aminin sa Kai aka Kira Yan sanda suka kada kansu sukai police station dasu da ganan asibitin tafawa balewa dake bauchi aka wuce da Aminin lado kasancewar ya ta zubar da jini ta hanci ga ya kasa bacci tunda abun ya faru ,shi Kuma lado da kulu aka cigaba da tsare su karshe aka ce za'a bada bailing su wani abokin shashancinta ta Kira yai bailing shima Kuma lado baffan su Aisha ne yai bailing atake agun lado yace ya saki kulu saki Daya maimakon aga nadama da danasani Sai gani sukai ta ya tsina baki tace tafi nono fari take yace Kar ta fi Masa da Yar sa anan ne ma hankalin ya Dan tashi don tanasan yarta matuka gashi ita kadai Allah ya Basu tsawon rayuwar aure Amma ko me ta tuna Sai cewa Tai ta amince.kayan ta kawai ta diba ta bar na Salma (takwara Taiwa mahaifiyar ta) Wanda yai bailing ta ya dauke ta suka bar gari.Wannan kenan.

____________'__________________________
Bangaren Innar su Aisha kuwa kawai Shirin bikin ni'ima take badan malam ya taka Mata burki da har gun karbar lefen zata,Amma malam ya Hana ta aikwa ta kuka don haka bayan an kawo kwa ta wanke kafa ta tafi gani taje ta bararraje wajan sati guda Sai ga baffa yazo da Kansa ba sako yace su tafi zaman ya Isa haka tace ai ita da sai an Gama Biki zata taho🤣😂 Biki saura wajan wata uku yace a'a Kya dawo ya kwa iza keyarta badan taso ba Sai kafin madaki tana ta Jin haushi kan meya sa ya matsa Mata ita da gidan yarta bazataje ta ci arziki ba tunda taje take abunda take so ko girki ba'a dorawa Sai Wanda take so ,Naman kaza kwa kullum Sai taci shi haka ta kafawa Yar ta doka sannan balangu Kuma da yamma shima.

#Team H A
#say no to rape
#stay safe

Mrs Sadi😙

Har AbadaWhere stories live. Discover now