Babi na Goma sha uku

49 7 1
                                    

Oh Allah, We have  tried our best during this blessed Month of Ramadan, accept all our prayers, our fast,and all other efforts,reward us and let them be the light to our soul that carries us through the gates of paradise. Ameen ya Hayyu ya qayyum.Taqaballahu minna wa minkum Eid Mubarak!                                  

Komai na duniya Sai Allah ya nufa na , I have put to bed which I on go C.S Alhamdulillah I was blessed with cute baby girl ,wannan Rashin lafiyar ya janyo tsayuwar labarin Nan Amma in Sha Allah na dawo kenan zamu karasa da izni Mai duka fatan alkairi ga duk Mai bibiyar littafin *Har Abada* One love

Kwanci tashi babu wuya har gashi yau aka adaura auren ni'ima anyi komai cikin nutsuwa da sanin ya kamata  ba almubanzaranci akai ba amma komai anyi shi cikin tsari , a yau barrister Aisha na cike da garin ciki domin abun farin cikin ne ya samu ka haifi "ya ta girma har ka aurar ai dole Kai murna Allah ya saka zaka aurar da ita lafiya ...su hajiya iya kakar amarya an cashe sosai an kwaso shoki iya son rai...can na gano walida na tikar rawa ba kakkautawa ,Yan uwa na kafin madaki duk sunzo sunwa barrister Aisha kara matuka ,bayan la'asar Yan daukar amarya Suka iso tare da gabatar da al'adar daukar amarya da aka Saba wato kwalin cingum da kuma kudi yadda ya sauwaka Dubu biyar Suka dora saman kwalin cingam guda shida .Ni'ima ta kankame barrister ta rusa kuka da kyar aka babbare ta aka tafi kaita gidan ta dake rijiyar Zaki kafin su tafi kasar da akai posting dinsa , da walida na ta dariya yanzu daki ya zama nata Sai data ga da gaske fa Yaya Ni'ima sun barta agidan kenan su day ita Sai dai ziyara sannan hankalin ta ya tashi ta Shiga zare Ido Sai ga hawaye wani na bun wani aunty Jamila kanwar abbansu ce ta kada keyar ta Suka fito daga gidan.Amarya Ni'ima Allah ya Sanya alkairi Amin .
-----------------------------------------------------------
*Bauchi*kafin madaki

Lado gaba daya abun duniya ya dame shi ya rasa inda zai saka kansa tunda Suka tashi da safe Yar sa ke sheka a Mai ya rasa abun yi lallabawa yai ya kaita karamin asibitin dake kafin madaki domin a duba ta awan farko a tarar da ciki wata uku cif idan lissafin sa daidai wato dai bayan tafiyar matar sa cikin ya samu tirka shi .........wani lamarin in yai kamari kasa kuka ma ake ko ai fada ya rasa Mai zance kawai Sai yace ta taso su tafi ko tsayawa suji bayannin likita basuyi ba Kan maganar awo Dan shi Dr ya dauka matar sace.

Suna fitowa Suka tsaya ko zasu Sami a chaba Basu samu ba Sai Suka taho da kafa kasancewar ba lafiya gare ta Sai suke tafiya sannu sannu ...............suna Shiga gari lado ya fuskanci duk inda Suka wuce Sai kallon su ake Ana kuskus wato dama ance Dana ka da Wawa suke fada maka magana Sai ga wani makwancinsa Wanda yake Kamar dolo haka yace lado Ashe haka lamari ya faru lado yace eh wallahi ya daukan zance Kama matar da Aminin sa yake nufi baisan wata maganar da bance ta zagaye gari ba , yace to Allah ya rufa asiri Amma dai lado wannan Abu Bai kyau ba baka kyauta Ashe shiyasa ka Hana yawale aurarta Ashe Kai zagawa  kake gun diyar taka to Allah ya kare Mana yaran mu daga Sharrin ka don Kai yanzu abun tsoron ne tunda ka iya haikewa Yar ka to wace mace zaka kyale ai babu ....lado yai shiru Kamar Wanda lantarki ya ja ya rasa Mai zaice wato shiyasa ake ta kallon sa Ana kuskus to ya akai ma maganar cikin ta fito tunda kansu dawo gari yai shiru abun duniya ya dame shi.....(abunda ka shuka shi zaka girba kawu lado) abunda lado Bai sani shine iliya Mai acaba yakai wani Dan bautar kasa asibiti Sai yace ya jira shi to shi yaji zance Kuma ya dauko Dan bautar kasar ya sauke shi a Tasha daga Nan ya goyo ladidi ababur Suka yo cikin gari a hanya ne suke zancen yadda zamani ya ta barbare shine har ya Bata labarin abunda yaji ya Kuma gani asibiti ita Kuma tana sauka ta Shiga gidan balaraba Mai adashe karbar zubin dashe domin daukar tane to anan fa ta bada labari , dama ta tarar da Mata biyu agida daya acikin su dama kitso zata gidan jummai ita ta dauki zance ta fada gidan kitso ,dayar Kuma ta biya gun dauda Mai icce Nan ma ta bashi labari Nan take ya bawa mutanen dake zama agurin sana'ar sa labarin (look how fast gossip can be separated )Allah ya kyauta Amin.

Maganar kawu lado har gun Mai gari karshe dai uwar gidan Mai gari ce ta titsiye yarinya akan wa yai Mata wannan aika aika karshe wani Dan ci Rani ne da ya sauka gidan lado da matar sa yai ta bawa lado abun duniya lado najindadi Ashe shi cutar sa ake Bai sani ba take lado ya yanke jiki ya fadi domin shima kuwa ya na lekawa gun matar mutumin shi a ya dauke shi ke cin riba dasu Ashe shi aka Sha dashi wannan shine daya daga cikin illar Zina domin bibiyar jini take Allah ya tsare Mana zuri'a baki daya Amin ya rabbi.

*AUCKLAND*

Kyakyawar matashiyar macece wacce dagani Allah ya rufa Mata asiri kallo daya zakai  kasan akwai nutsuwa tattare da ita Hadi da Kamala waya ce Kare a kunnen tana amsawa shekarar su ta hudu kenan a auckland  yayin da aure su ke da shekara biyar da dauruwa haihuwar biyu Amma yaran ta uku tayi na farko Ibrahim Sai twin amanee da Amara Wanda ta Haifa anan Auckland rabonta da kasar ta haihuwa wato Nigeria shekara hudu kenan yanzu ne take Shirin tafiya Wanda take cike da dauki , Haba walida kin cika Abu Mana na Gaya miki ki tsaida magana daya pls, ban San Mai wacce ta Bata amsa ba Sai ji nai to Amma Allah ya Kamata ki rage high test wlh ai ita rayuwa dama dole wani ya fika katse Kiran tai, ta daukar Mata takalman da dama don su tafito jirgin dare zasu bi dama ita da Mai gidan da yaran zuwa kasar su ta haihuwa wato Nigeria .

MALAM AMINU INTERNATIONAL AIRPORT KANO.
 
Cikin Abaya sakar kasar Oman red velvet hannun ta rike da waya kirar kamfanin apple wato iPhone 11 fuskar ta sanye da glass murmushi Tai sanda ta hango Yar uwa da family ta sun nu fota take dimple ya lotsa,daga gani kaga budurwa Yar kwalisa Wanda ganin farko zaka fuskanci akwai rawar Kai tattare da ita Dan sowa ta saki Tana fadin Yaya Ni'ima suna Kara sowa ta rungume Yar uwar itama tuni ta rungume yayin da hawaye ya Shiga sintiri bisa fuskarsu saboda murnar ganin juna , murmushi abban twins ya saki yasan Ni'ima tayi missing gida matuka Kuna Yana jinjinawa kokarinta ko a fuska Bata nuna Masa Rashin jindadin ta ba sanda ya Hana zuwa gida da zata haifi twins haka ta hakura ta zauna, madallah da mar'atussaliha (sunan da yake kiranta).bayan Yan gaishe gaishe suka dun guma sukai gidan da yake mallakin nasu Wanda ya turo da kudi aka Sai Masa anan gate 3 yake aforestation gida ne Mai matukar kyau da ya dace da zamani , suka Shiga suka iske abinci na jiran su Wanda aiki Maamah wato barrister Aisha da Kuma barrister Ummi matar yayansa Suka Fara watsa ruwa kafin su sanko Ibrahim tuni ya sake da walida Amma Yan biyu Kam Sai dari-dari suke da mutane duk da yadda suke video call da aunty waleeda da duk wata Hira Sai sun Fadi sunan ta Amma Ina Rashin sabo ya saka suke nokewa , ita Kam in ta kalle Sai taji nishadi ya Kamata ai dole taje dasu school aga yaran sister dake aure akasar waje da take bada labari ,gashi Kuma Yaya Ni'ima ta siyo  Mata iPhone 12 ga kayan kwalliya na burgewa dole ai bagu this semester a school  da tuno mima yarinyar dasuke ta kunsaka a class Sai ta bushe dariya ita kadai zata so ganin zuciyar mima in ta ganta da iPhone 12 ,zata zama mace ta farko a ajin data mallaki iPhone 12.

#Say no rape
#Team H.A
 

Mrs Sadi😘

Har AbadaWhere stories live. Discover now