🌵🌵Babi na Goma Sha daya🌵🌵

51 6 0
                                    

Assalamu alaikum,

10th Dhul Hijjah 1441AH:

Their (animals to be slaughtered on Eid) meat will not reach Allah, nor will their blood, but what reaches Him is piety (Taqwa) from you. Thus have We subjected them to you that you may glorify Allah for that [to] which He has guided you; and give good tidings to the doers of good (Q22:37)

O ALLAH!
Increase us in Taqwa & bless our lives, accept our worship, supplications & sacrifices from us. "Aameen"

Eidukum Mubarak Wa Kullu Aameen Wa antum bi Khair.

IKKO LAGOS
Bayan Dogon nazari Caroline taga gwanda su tafi saudia neman kudi ita fa tunda Ojuju ya bukaci ta bashi rakiya taji cult ta fita akanta dama da kudi a hannun ta nan da nan suka hau Shirin tafiya kasa Mai tsarki neman kudi,cike da fatan dacewa ko ta ina sannan Caroline ta karbi musulumci Rufkhatu ta cigaba da Dora ta akan hanya don ita Kam tana da ilimin addini abunta.Caroline wacce yanzu ta koma Salma da diyar ta rakiya tare da Rufkhatu suka lula kasa Mai tsarki domin yin sana'ar Sai da abinci, gidajen tikari yawanci akan tudu suke kasancewar sunzo da jari suka fada sana'a ka'in da na'in inda Rufkhatu ta bawa Salma shawarar ya Kama ita da rakiya suke zuwa islamiya da ake agidan dasuke da daddare domin samun Karin haske a kan addinin musullumci,haka kuwa akai suna zauna cikin rufin asiri kafin kaddara ta fado masu,wato askar ne suka kawo was gidan da suke inda suka Kama mutane da dama ciki harda rakiya da Rufkhatu inda Kai tsaye aka auno su gida Nigeria wannan shine rabuwar rakiya da mahaifiyar ta inda ita  ba'a Kama ta ba.Bayan an Gama guje guje askarawa sun tafi Salma ta fito daga maboyen tana dunduba fuskar mutane domin neman rakiya da Rufkhatu Sai dai ga mamakin ta babu su har Sai da Hari wacce suke zaune tare tace ita Kam da idon taga sanda aka Kama rakiya ,Nan Salma ta saka kuka tana tunanin Ina zata ga Yar ta aka shaida Mata ai  Nigeria za'a Mai dasu hankalin ya Dan kwanta ta dauki anniyar komawa gida shafa kajar (lalitar ) ta tayi ta kudi taji wayam babu tabbas gari haura katanga ta zubar dasu wani tashin hankalin ya Kara kamata to tun daga Nan rayuwar Salma ta shiga watan gari-gariya ,daga Nan ma Hari ta Basu shawarar su koma Bisha da Zama Ana samun aiyukanyi anan gashi akwai saukin takurar askarawa Nan take ta amince domin mafita take nema anan din cikin matsi take tasan da ba sabil da suke karba a masallaci ba da abinci ma gagararta zaiyi,a Bisha suka Sami aikatau sunayi ita da Hari Dadi ba Dadi yayin Salma ta Mai da hankalin wajan Tara kudin jirgin komawa gida. Ana cikin Wannan halin aikatau da yake kudin ba wasu masu kauri bane Hari ta kwanta ciwo haka Salma ke Yi aikin ita kadai Sai abiya su Ashe ciwon Hari bana tashi bane ta amsa Kiran mahalincinta,daga Nan Salma ta cigaba da aikatau Kuma duk aikin ita takeyi amma tunda hari ta rasu a ka dawo biyan kudin mutum Daya a cewar hajja ai ita kadai ce don haka kudin daya zata biya Amma aiki dole ai duka in ta gaji Kuma ta anjiye ta Sami wata.

************************************
KAFIN MADAKI

Haka Biki ya tashi cikin farin ciki da annashuwa kowa na San barka, inda aka wuce da amarya Aisha Kano tabo tumbin giwa Mai Mata Mai mota gari ba Kano ba dajin Allah lol😂tana kuka abun tausayi,Rakiya taso zuwa amma lamarin da ya faru ya saka ta hakura da zuwa domin tana bukatar bincike Dan haka ta hakura da zuwa Kai amarya Dan har da ita aka tsara zuwa kasancewar ita da Inna suna koren ganye (suna Shirin) lol🤣.

************************************Cikin wayo ,dabara da gogewa abariki rakiya ta Sami bayanai agun innar Aisha game da mutanen Durbunde da suka zo inda ta gano dalilin da yasa taga Aisha namata Kama Gwagggon ta Binta Ashe yayar mahaifin ta Binta itace mahaifiyar innar Aisha kenan Inna cousin din tace wato Yar mace da Yar namiji suke turkashi wato the world is just small world,aranta ta kudurta zata cigaba da boye sirrin ta baza ta Bari a ganota ba uhm ta sauke ajiyar zuciyar tunanin mahaifiyar tane ya kamata ko tana da rai oho.
____________________________________
Rayuwar auren su rayuwa ce da suka Gina akan tafarki tsaftacence Mai cike da tarbiyya da ganin mutumci juna tare da bin sunnah cikin hukuncin Allah ta Sami shiga jami'ar Bayero University Kano(BUK) inda zata karanshi law kasancewar abunda take sone wannan ya saka ta zage dantse mutaka don Samun cikar burin ta ,Allah ya taimake ta classes dinsu zuwa 2 na Rana ne an tashi Sai Kuma gobe gashi a old site suke lecture abunsu baruwanta da zuwa lulukin Nan wato BUK new site ,ahaka take karatu cikin hukuncin Allah Bayan kammala zangon karatu na shekaran farko har sun Shiga aji biyu second semester ta fara laulayi wannan ya Dan taba ta kadan amma da yake ta Sami suruka Mai fahimta Nan da Nan aka sama Mata Mai Taya ta Zama wacce kema taimaka Mata da aiyukan gida Bayan kammala Jarrabawar su da kwana Daya ta sunkuto baby girl dinta yarinyar taci suna Ni'imatullah haka rayuwa ta kasance ga wannan ma'aura ta .

Sunayen su suke dubawa na tafi law school dama law school dake jihar Kano wato bagauda ita ta cike Kuma Nan aka kaita ,yaran ta da alokacin su uku hajiya kakarsu ta dauke su suke zaune agun ta ita Kuma taje kafin madaki ta sanar masu sanna ta tafi law school Wanda ya dauke suke shekara guda tim suna gwagwarmayar Zama cikankiyar lawyer inda Allah ya amince Mata ta Sami nasara cin Jarrabawar a zaman farko ,Yau ranar ce Mai mahimmanci agare ta kasancewar yaune ta Zama certified barrister yau akai calling dinsu in to Bar farinciki ne kwance a fuskar kowa ka gani agun, shekara biyar a university Daya a law school aikuwa an Sha gwagwarmaya,gwarzon mijin ta Daya tamkar da dubu shine yaje mata da Kuma mahaifin ta Wanda da kyar ya yarda yaje Sai walima da za'ai idan ta dawo gida Wanda su Inna ma an Samu zuwa anata washe baki yayarta ma tazo da kanin iro Ana ta hidima da harkar arziki Sai muce Allah ya sa an Gama a sa'a Sai Shirin tafiya NYSC wato yiwa kasa hidima.

This chapter is for dear Allah ya bada sa'ar Law school Barrister Maimuna Mustapha 😍.

Vote and comment please share with family and friends

#team A H
#say no to rape
#ana tare

Mrs Sadi 😗

Har AbadaWhere stories live. Discover now