0⃣0⃣1⃣

662 28 13
                                    

DA SUNAN ALLAH, MAI RAHAMA, MAI JINƘAI

Note: Wannan labarin ƙirƙiraren labari ne. Suna, wurin aiki, kamanni, da gidaje da komai abubuwa ne waɗanda marubuci ya ƙirƙira. Idan wani abu yayi kamanceceniya acikin labarin da rayuwar wani, ina roƙon koma waye da yayi haƙuri. Domin tozarci ba shi bane nufi ko niyyar Marubuci...

Wannan shafin sadaukarwa ce zuwa ga Aunty @Mai_Dambu

ZARIA

Dukansa yake yi yana jibgarsa da dukkan ƙarfinsa kamar Allah ne ya aikoshi. Fuskarsa babu alamun imani, tausayi ko sassauci a tare dashi. Sai faman gyara rawanin kansa yakeyi wanda ya ɗaura bisa kan hularsa da ke dawowa gaba sabida yanda yake dukan da dukkan ƙarfinsa, tare da babbar rigar koɗaɗɗiyar shaddar dake jikinsa dake ta faman warwarowa.

"Wayyo Allah! Malam dan..Allah kayi haƙuri wallahi zan koya na iya...Malam kayi haƙuri....wayyo Allah bayana..."
Yayita faɗa yana bashi haƙuri da ƴar ƙaramar Muryarsa da ta soma disashewa.

Sai da yayi masa lilis sannan ya ƙyaleshi ya kalleshi da idanunsa da suka yi Ja kuma suke nuna tsantsar rashin imanin da ke tattare dashi
"Wallahi na baka daga nan zuwa ƙarfe ɗaya zan waiwayeka, karka sake na kiraka baka iya ba dan wallahi dukan da zan maka sai yafi haka. Wawan yaro shashasha kawai!". Ya faɗa yana me fita daga cikin ɗakin...

Yaro ne wanda daga kallonsa kasan cewa ba zai wuce shekaru Takwas zuwa tara ba. Fari ne tas dashi wanda kallo ɗaya zaka masa kasan cewa ya haɗa jini da Fulani. Manyan idanuwa ne gareshi tare da dogon hancin da ya ƙara ƙawata fukarsa. Duk da sanyin da akeyi a gari wanda ya sa fatar jikinsa bushewa amma hakan bai hana bayyanar busassun pink lips ɗinsa wa'inda sukayi dai dai da fuskarsa ba. Sanye yake da riga T-shirt light blue duk yayi datti wanda yayi masa oversize tare da wando three quarter wanda girman wandon yasa yake sanya hannunsa a ƙugun wandon bayan nannaɗeshi da yayi ta sama.

Da sauri ya ɗauki Allon dake jingine a bangon ɗan ɗakin da koh arziƙin siminti bai samu ba. Cikin shessheƙan kuka da Ajiyar zuciyar da yake ta saukewa akai akai ya soma bitar
"Ba'asun....Mi ara..alu...."
yana ta karantowa a tsakanin shessheƙan kuka.
Sai da ya shafe tsawon awanni sama da uku yana abu guda wanda da ƙyar ya iya samu yayi craming saboda tsabar yunwar dake ƙwaƙwularsa. Shiru yayi yana tunanin yadda zai je ya cewa Malamin nasu ya gama ko don ya bashi izinin zuwa yayi barar abincin da ya saba amma firgici da tsoron da yake ji ya hanashi zuwa.

Kwantawa yayi a tantagaryar ɗakin riƙe da cikinsa da ke ta ƙugi da ƙara yana neman agaji. Kamar daga sama ya ji ana kiran sunansa
"IMRANA!....IMRANA!...IMRA...."
Katseshi yayi da saurin amsawa da "Na'am!".
Da sauri ya tashi ya na me buɗe labulen buhun ɗakin tare da ficewa zuwaga ɗakin Malamin nasu.
"Dan Ubanka kana jina ina kiranka kana min banza koh?. idan haka ta sake faruwa wallahi sai jikinka ya gaya maka! Kuma yanzu yanzu ka ɗauko robanka kazo ka fita yin bara, ban yarda ka ci wani abu ba har sai ka nemomin nawa naci. Idan kuma ka tsaya yawo bakayi sauri ba zaka dawo kazo ka fuskance ni!"

"Toh Malam". Ya faɗa haɗe da juyawa ya bar ɗakin. Ɗauko roban bararsa yayi ya fita bara a layin da ke bayan layin Makarantar tasu.

Da ɗan kuzarin da ya rage masa ya fara shiga gida gida yana bara. A gida na uku daya shiga ne aka kirasa akan ya kawo robarsa. Yana ƙoƙarin shiga ciki ne yaga wata yarinya tana miƙo mishi hannu da nufin amsar robannasa. Babu musu ya bata ta shiga ciki da shi. Jim kaɗan ta futo dashi shaƙe da abinci aciki. Amsa yayi yana ma ta murmushi tare da yi musu godiya da Addu'a. Sanin abinda Malaminsu ya faɗa mishi ne ya sa yayo hanyar Makarantar tasu. Ya na zuwa yayi sallama a bakin ƙofa Malamin ya amsa tare da bashi iznin shigowa...

Kusan rabi da kwatan abincin ya juye acikin plate ɗin da ke ɗakin sannan ya bashi sauran akan yaje ya ci ya huta zuwa anjima zai kirashi ya bashi karatun da ya ce mishi ya haddace...

Kamar yadda ya saba a kullum wani uncompleted building dake bakin titin da yayi nisa da Makaratar yaje. Kamar daga sama yaji ance "Kai!".
Sosai ya furgita musamman yadda muryar ya bada wani sautin amo acikin kunnensa. Da sauri ya juya jikinshi na rawa. Wani saurayi ne tsaye agurin yayi wata tsayuwa irinta ƴan daba idanunsa sun kaɗa sunyi jajur ga dukkan alamu wani abu ne yasha ya bugar dashi.
"Meye acikin robar nan?" Ya tambayeshi cikin wata irin buɗaɗɗiyar kausasshiyar muryan da ya ƙara firgitashi. Cikin in ina ya soma faɗin "Aaabinci...na ne a..cikiii". Ya faɗa ya na kauda kansa daga kallonshi.
"Bani robar nan!" Ya faɗa cikin ɗan tsawa.
"Dan Allah ka tausaya min ka bari inci wannan zan je in nemo ma...."
Saukan lafiyayyen marin da yaji akan fuskarsa ne ya katseshi yayi taga taga zai faɗi yayi saurin sa ɗayan hannunshi ya dafa jikin bango yayin da ɗayan hannunshi still yake riƙe da roban.
"Zaka bani ne ko kuwa sai na ɓaɓɓallaka?!".
"Kayi haƙuri wallahi yunwa nakeji"
Ya faɗa yayinda hawaye ke gangarowa kan kuncinsa.
Zare belt ɗin wandonsa matashin yayi ya fara jibgarsa ya na dukan sa ya amshi roban daga hannunsa. Bai daina dukansa ba sai da yaga yayi masa lilis. Zama yayi agaban shi ya cinye abincin tas sannan ya tashi yana mai faɗin "Daga yau ka sake min gardama kaga yan da zan ci ubanka inga mai tsaya maka a garinnan"

Wani irin kuka ya saki mai ban tausayi da taɓa zuciyar duk wani mai imanin da ke kusa dashi. Kuka yayi sosai har bacci ɓarawo ya sace shi batare da ya sani ba.

______________********____________
********

KATSINA

"Assalamu Alaikum!". Ya kwaɗa sallama a ƙofar bukkan Bokan zuciyarsa na dukan uku uku.
Wata uwar dariyar da tayi sanadiyar girgizar dajin ne gaba ɗaya ya zagaye dajin, har sai da ya kai hannunshi domin toshe kunnensa saboda yadda yaji muryar na amo acikin kunnuwansa. Ƙoƙarin toshe hancinsa yakeyi yadda yaji wani irin wari na dososhi. Wani Mutum ne ya bayyana agabansa sanye da tufa wanda aka yishi da fatar damusa fuskarsa gaba ɗaya ba kyan gani a matuƙar murtuke. Cikin wata irin murya mara daɗin ji da firgita mai sauraronta yace
"Wannan wani irin shashanci ne?!. Waye ya faɗa maka ana sallama anan?!. Ko so kake ka ƙona mun abokan aiki na?!. Kasani! Kayi laifi kuma Aljani muru yace kafita ka shigo da baya kuma da ƙafar haggu!"

Da sauri ya fice tare da shigowa da baya kuma da ƙafar haggu. Zubewa yayi a gaban Bokan yayi shiru ya rasa abinda zai ce saboda wannan itace rana ta farko da ya fara zuwa gurinsa. Motsa bakinsa ya farayi alamun ya na so yayi magana amma gaba ɗaya ya kasa furta komai. Cikin kausasshiyar muryarsa Bokan ya fara faɗin
"Na fahimci abinda ke tafe da kai, kuma tabbas buƙatunka zasu biya. Amma sai kayi wani abu guda ɗaya idan zaka..."

"Mene shi wannan abun Boka?. Ka faɗeshi koma mene ne zan yi shi matuƙar zan samu biyan buƙata ta"
Mutumin ya faɗa yana kallonsa

"Sai kayi luwaɗi da ɗanka!"

Da sauri ya ɗago idanu ya kalleshi cikin firgicin da yake ƙoƙarin dannewa ya ce "Bani da ɗa. Mun daɗe da Matata amma har yanzu bamu samu haihuwa ba!"

Wata razananniyar gurnani ya yi tare da sakin dariya lokaci guda yace "Akwai wata hanya guda ɗaya. Yau yau ake so. Kar a sake ayi shi sama da awa huɗu masu zuwa! Yaron yana nan acikin wani ginin da ba a ƙarasa ba dake kusa da Sabon birni. Da zaran ka ga ginin jikinka zai baka. Akwai hatsari a kan hanyar. Sai dai kai zaka ƙetareta komai rinsti. Idan ka jinkirta kuwa, kai da samun wannan kujerar har Abada!".













#VOTE
#FOLLOW
#COMMENT

Alƙalamin Real Ahmerd

IMRANWhere stories live. Discover now